Tarihin Ranar Valentine da kuma Hukuncin raya shi

Danna nan domin shiga karatu Online

Assalamualaikum Warahmatullahi wa barkatuh.
Kamar yadda kowa ya sani ne gobe 14/02/2019 itace rana da dayawa daga cikin mutane a duniya suke raya wannan rana ta Valentine. Meye tarihin wannan rana? Kuma shin ya dace musulmi ya raya wannan rana?
Takaitaccen Tarihin Ranar Valentine:
Wannan rana asalin sunanta a turanci shine: “Valentine’s Day, ko “Saint Valentine’s Day” ko kuma “Feast of Saint Valentine“. Ta samo asaline kuma daga addinin kiristanci tun a daular romawa ta wancan lokacin, Kuma shi wanda ake raya wannan rana domin shi shine: “Saint Valentine“. Ya kasance a wancan lokacin daular romawa(The Roman Empire) ta haramta wa sojoji yin aure, sabida sunaga hakan zai shagaltar da wa’innan sojoji wurin yaƙe yaƙe da sukeyi, toh amma shi wannan Saint Valentine yaci gaba da aiwatar da auren sirri tsakanin wa’innan sojoji da masoyansu. Bayan da asirinsa ya tonu sai sarki na wannan lokacin(Claudius) yayi umarni da a kashe shi. A lokacin da aka tsare wannan Saint Valentine a gidan kaso kafin a zartar masa hukuncin kisa ya faɗa soyayya da ɗiyar Alkali mai masa shari’ah, yadda aka rawaito cewa kafin a kashe shi ya tura mata saƙo ta soyayya, wanda yake mata bankwana aciki. Daga nan aka samu Kalmar “Your Valentine” wanda masu tura sakonnin soyayya a wannan rana suke amfani dashi a kyaututtuka da saƙonnin soyayya da suke tura wa juna.
Wannan itace riwaya da tafi shahara kan dalilin wannan rana ta Valentine. Akwai riwayoyi da suke nuna tana da asali ne tun a daular romawa kafin su shiga addinin kiristanci, wanda a wannan lokacin ana raya wannan rana ne a 15/02. Kafin daga baya lissafi ya canza ta koma 14. Ma’ana dama ranan ta na nan. Bayan kuma abinda ya faru da Saint Valentine, sai wannan rana ta ƙara samun armashi da wasu sauye suye.

Domin neman karin bayani kan wannan rana zaku iya duba Wikipedia, ko History.


Hukuncin Raya Ranar Valentine a addinin Musulunci:
Kamar yadda duk wani musulmi ya sani ne cewa addinin musulunci addini ne cikakke, wadda baya karɓan ƙari, Annabi (Sallallahu alaihi Wasallama) bai bar duniya ba sai da wannan addini ya kammala baki dayansa. Allah(Madaukakin Sarki) ya saukar da faɗinsa:
اليوم أكملت لكم دينكم وأتممت عليكم نعمتي ورضيت لكم الإسلام دينا.
“A yau ne na cika muku addinin ku, kuma na Cika muku Ni’ima ta, kuma na yardar muku da addinin musulunci ya zamto addini”
Daga wannan rana duk wani abinda Allah ko manzon sa basu shar’anta ba ba zai taɓa zama addini ba.
Kamar yadda ya zamto abu ne sananne cewa haramun ne Musulmi ya raya wata rana ta biki na wa’inda ba Musulmi ba. Domin hakan taimakawa ne wurin tsaɓa wa Allah, kuma Allah ya hana taimakekeniya kan tsaɓonsa. Allah yace:
وتعاونوا على البر والتقوى ولا تعاونوا على الإثم والعدوان.
“Kuyi Taimakekeniya kan ɗa’a da tsoron Allah, kada kuyi Taimakekeniya kan saɓo da ƙetare iyaka”
Abu Dawud(1134) Ya rawaito hadisi cewa: “Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallama) yazo madina, lokacin mutanen Madina suna da wasu ranaku biyu da suke wasa acikinsu, sai manzon Allah ya tambaye su meye labarin wannan ranaku? Sai sukace mun kasance muna wasa ne acikin su tun a jahiliyya, sai manzon Allah yace: Allah ya canza muku wa’innan ranaku da wa’inda suka fishi albarka, ranar Idin Babban Sallah, da karama.
Haka yake nuna karara yadda annabi yayi hani kan yin wata bukukuwa ta jahiliyya, kuma yayi umarni da a tsaya kan bukukuwa da Allah ya shar’anta. Wanda sune Idi Babba, da karama. Sannan kuma hakan yana nuna cewa Bukukuwa suna daga cikin abubuwa da suke banbance tsaƙanin Addinai. Ta yadda duk wanda kaganshi yana raya wata biki zaka iya fahimtar meye Addininsa.
An tambayi Sheikh ibn uthaimeen kan hukuncin raya wannan rana ta Valentine: sai ya amsa da cewa:
Yin bikin ranar Valentine bashi halasta sabida dalilai kaman haka:
Wannan Biki ta ranar Valentine Bid’ah ce bata da asali a Shari’ah.
Wannan Rana ta Valentine tana janyo Irin soyayya wacce Shari’ah bata amince da ita ba da kuma ɓarna wacce bata da iyaka.
•yana janyo zuciyar musulmi ta ta’allaƙu da irin wa’innan abubuwa wanda basu da amfani, wacce ta saɓawa wa Tafarkin Magabata.
Sabida haka bashi halasta musulmi ya yi wani abu dake nuni da cewa yana raya wannan rana.
Daga ƙarshe:
Bayan wannan bayani takaitacce zai bayyana cewa:

  • Wannan Rana ta Valentine bata da asali a addinin Musulunci, kuma haramun ne Musulmi ya raya wannan rana, sabida hakan Bid’ah ne, kuma koyi ne da wa’inda ba Musulmi ba, da kuma kamanceceniya dasu, wanda kuma kamanceceniya da wa’inda ba musulmai ba haramun ne.
  • A addinin musulunci Rana biyu ne Allah ya shar’anta ta zamto Idi ga musulmai, shine ranar Idi babba da karama.
  • Dole ne Musulmi ya ƙaurace wa wannan rana, ya kuma faɗakar da ƴan’uwansa haɗarin dake cikin ta. Domin bashi ɓoyuwa ga duk mai hankali yadda ake tsaɓon Allah acikin wannan rana da sunan nuna soyayya.
  • Ba wayewa bane musulmi ya rinka bin irin wannan bukukuwa domin dacewa da zamani, wayewa shine bin tafarkin Annabin Tsira (Sallallahu alaihi Wasallama) domin itace zata tserar da mutum duniya da lahira.

Allah madaukakin sarki yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates