Yana daga cikin falalar Allah ga Musulmai ta yadda ya sanya musu hanyoyin samun lada da yawa, mutum zaiyi aiki kaɗan Allah ya bashi lada ninki mai yawa.
Haka nan kuma ya sanya wa bayinsa wani tsari na fansho ga duk wani wanda ya saba aikata wata ibadah sai wani lalura ya sanya ya kasa yin wannan aiki, kaman tafiya ko rashin lafiya.
Misali wanda ya kasance yana Sallar walaha kullum, sai Allah ya jarrabeshi da wata cuta da ta hanashi wannan sallah toh Allah zaici gaba da rubuta masa ladansa.
Haka nan wanda ya kasance yana lazimtar sallah a cikin jam’i sai wannan Annoba ta Covid19 ta hanashi zuwa toh Insha’Allah koda yayi Sallah a gidansa shi kaɗai Allah zai bashi ladan jam’i cikakke sabida kyakkyawar niyyarsa kamar yadda Maluma suka bada fatawa. Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:
إذَا مَرِضَ العَبْدُ، أوْ سَافَرَ، كُتِبَ له مِثْلُ ما كانَ يَعْمَلُ مُقِيمًا صَحِيحًا
Bukhari: 2996
Idan bawa yayi Rashin lafiya ko yayi tafiya, za’a rubuta masa kwatankwacin abinda yake aikata wa na ibada alokacin da yake a gida cikin Ƙoshin Lafiya.
Bukhari: 2996
Duk wani lalura da zai hana mutum aikata wani Ibada da ya kasance yanayi toh Allah zai bashi ladansa cikakke koda ko bai aikata ba.
Sabida haka ne Maluma suka bada fatawar cewa wanda yayi Sallah a gida a dalilin covid19 to yana da ladan Sallar sa cikakke, da sharaɗin dama ya kasance yana lazimtar Jam’i kafin zuwan annobar. Haka nan wanda ya saba zuwa wurin tafsiri kowani shekara sai wannan shekarar ya kasa zuwa sabida wannan Annoba toh yana da ladansa cikakke.
Allah yasa mudace, ya kuma yaye mana wannan musiba.
Leave a Reply