Warware Shubuha kan Cin yankan Kirismeti da Taya Murna

Danna nan domin shiga karatu Online

Maqala

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

Akwai wasu shubuhohi da wani dan uwa ya kawo a shafin sada zumunta na X. game da abinda ya shafi cin yankan da akayi domin kirismeti da kuma taya kiristoci murna. aka bashi amsa gwargwadon fahimta, shine naga ya dace in rubuta wannan amsar anan, domin Yan Uwa Musulmi su Amfana.

Shubuhohin sune kamar haka:

  1. Allah ya halatta wa Musulmi cin yankan kirista, saboda haka babu laifi aci yankan da sukayi domin kirismeti.
  2. Allah yayi umarni da ayi kira zuwa gare shi da Hikima da Kuma Wa’azai mai kyawu, saboda haka yana daga cikin Hikima da wa’azi mai kyau taya kafirai murna yayin bukukuwan su.
  3. Allah yana duba zukatan Mutane ne, ba Gangan jikin su ba, saboda haka lokacin da nake taya kiristoci Murnar Kirismeti ba ina nufin na yarda da Addinin su bane, Allah kuma yasan abinda yake cikin zuciya ta.

Amsoshi Game da Wannan Shubuhohi.

Assalamu Alaikum Dan’uwa. naga wannan rubutu da kayi, kuma ina girmama fahimtar ka kan wannan zance, amma inada wata fahimta ta daban, wanda nake ganin itace daidai. da farko kace baka yin bikin kirismeti wanda hakan daidai ne, sai dai kuma kace kana cin shinkafa da naman kaza da akayi domin wannan rana.

Hujjar ka shine Allah ya Halatta mana cin yankan Kiristoci, wanda Haka ne. Allah ya bada wannan dama acikin suratul Ma’ida Ayah ta 5. Sai dai akwai Banbanci tsaƙanin yankan da Kirista yayi a ranakun da ba ta bikin sa ba, da kuma wanda yayi domin bikin sa.

Wanda yayi ba domin wanin Allah ko dun wani biki haramtacce ba, ya Halatta muci idan har bai ambaci sunan wanin Allah akai ba, amma wanda ya yanka domin wanin Allah, ko domin wata biki wanda Allah ta haramta. Wannan baya halatta muci.

Domin yana daga cikin abinda shari’ar Musulunci ya hanamu ci na abinda aka yanka, duk wani abinda aka yanka domin wanin Allah. Wannan Rana ta kirismeti, rana ce da suke riya cewa an haifi ɗan Allah, wanda Sammai da ƙassai sun kusa su kekkece domin an danganta wa Allah ɗa. Kamar yadda Allah yayi bayani Acikin Suratu Maryam. Ayah ta 88-95.

Saboda haka ne ma Maluma magabata suka Haramta cin yanka da akayi Domin wasu ranaku ta bukukuwar Kafirai. Amma suka halatta cin ƴaƴan itace da abinda ba’a yanka ba. Ansamo Athar daga Aliyu Bin Abi ɗalib, da Aisha, da Ibnu Umar da sauransu.

Zaka iya Duba Littafin Iqtida’u Tsiraɗil Mustaqeem 1/250-251. Zaka samu ƙarin bayani kan wannan magana. Saboda haka bawai haramun ne cin yankan Ahlul kitabi ba. A’a abinda suka yanka domin ranar bukukuwan su shine ake zance.

Sannan na biyu kace: Zaka taya su murna saboda Allah yace: “Kayi ƙira zuwa ga tafarkin Ubangijin ka da Hikima da Wa’azi mai kyau. Shiyasa zaka taya su murna kan wannan biki nasu, domin kanaga hakan zai jawo ransu.

Da farko wannan Ayah an sauƙar da ita ne wa Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, amma har ya bar duniya ba’a rawaito ya taya wani wanda ba Musulmi ba murnan bikin sa. Haka nan Sahabban sa da wa’inda suka zo bayan su. Kuma abune sananne cewa babu wanda ya kai Annabi Usulubi mai kyau wurin Da’awah. Amma duk da haka bai taɓa taya su Murna ba. Kowa yana kan Addinin sa. Hakan yana nuna cewa idan mutum yana laifi bashi daga cikin Wa’azi mai kyau ka tabbatar dashi kan wannan Abinda yake yi, abinda yafi dacewa shine Ka faɗa masa kuskuren sa ya gyara. Misali ne mutum yana da wata biki da yakeyi ko wani shekara wanda yake tara mata yana Zina dasu, sai kazo kace ina taya ka murnan zagayo war wannan rana. Wanda abune sananne cewa Zina bata kai danganta wa Allah ɗa ba.

Saboda Hakane maluma sukace tayasu murna ma zai ƙara musu ƙarfin Guiwa ne kan wannan abinda suke aikata wa, suga kaman suna aikata daidai ne.

Sannan na Ƙarshe ka nuna cewa Allah yana duba zuciyar mutane ne ba gangan jikin su ba, saboda haka lokacin da ka ce musu “Merry christmas” ba kana tabbatar da abinda suke kai bane acikin zuciyar ka.

Abinda yake nufi kamar yadda Maluma sukayi bayani shine, Allah ba yana amfani da kyawun gangan jikin Mutane ko Surar Jikin su bane wurin basu lada, ko wurin sanya su a Aljannah, A’a yana duba zuƙata ne. Domin zai iya yiwuwa anan duniya kaga wani yana da kyawun Jiki Da yawan Arziƙi, amma cikin zuciyar sa babu Imani, sannan wani kuma zai iya kasance wa Bashi da kyawun gani, ko talaka ne, ko yana fama da wata cuta a jikin sa, amma kuma zuciyarsa akwai Imani. To da wannan Abinda ke ciki zuciyar Allah yake amfani bawai da kyawun sura ba.

Domin idan muka ɗauki hadisin a yadda ka fassara ta, mutum zai iya zuwa coci yaje ayi bauta dashi ko yaje wurin bautar gunki ayi bauta dashi idan aka tambaye shi ya za’ayi kana musulmi kuma zaka je coci? Sai yace Ai Allah yasan abinda yake cikin zuciya ta, Ni naje cocinnan ne ba wai nayi Imani da abinda ake faɗa ko ake bauta wa a wurin ba, naje ne kawai. Kuma Allah yana amfani ne da zuciya ba zahiri ba. Wanda wannan kuma ba Haka bane. Dole sai mutum ya haɗa Imanin Zuciya da Ayyukan gaɓɓai kafin ya zamto cikakken Musulmi.

Saboda Haka ɗan’uwa ka ƙara bincike kan wannan Batu, Allah kuma ya datar damu da daidai. Kuma ka sani Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “ Lallai halal a bayyane yake, haka nan Haram a bayyane yake, amma a tsaƙanin su akwai wasu abubuwa masu rikitarwa, duk wanda ya faɗa cikin su, to zai Faɗa cikin Haram, wanda kuma ya guje wa wa’innan Abubuwa Masu rikitar wa, to ya kuɓuta da Addinin sa, da Kuma Mutuncin sa” . Saboda haka irin wa’innan Abubuwa da ake ta cecekuce akan su mu kula mu kiyaye kan mu.

Allah yasa mudace, ya kuma tsare mu daga faɗawa Halaka. Wassalamu Alaikum.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates