Duniya ba gidan zama bane.
Gida ne na jarabawa
Gida ne na aiki domin neman lahira.
Kada ka bari neman duniya ya sanya ka rasa lahirarka. Duk abinda zakayi a duniya kada ka bari yaci karo da ainahin abinda ya kawo ka cikin duniyar wato bautar Allah. Domin dalilin halittar ka kenan, Allah ya halicce ka ne domin bauta masa badon neman duniya ba. Ana neman duniya ne domin samun guzurin neman lahira.
Ka sani cewa duk abinda Allah ya ƙaddara maka zaka sameshi koda ko duk duniya sun taru domin su hana ka samun shi, haka nan abinda Allah ya ƙaddara cewa bazaka sameshi ba, ba zaka samu ba koda ko duniya sun taru domin su samar maka shi. Ka dogara ga Allah ka sani cewa Allah shine mai bayar wa, kuma shine mai hanawa. Ka mance da mutane kayi riƙo da ubangijin mutane.
Ka samu ka rinƙa tashi da dare kana faɗa wa Allah buƙatunka kana neman afuwansa, Sannan ka lazimci ambaton Allah da kuma Salati wa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama zaka samu Sa’ada duniya da lahira
Leave a Reply