Wasu daga cikin Ladduban Layya

Danna nan domin shiga Online Islamiyya.

Ana koyar da Hada baki, da Qur’ani da sauran su

Layya Sunna ce mai ƙarfi akan Musulmi Wanda yake da iko.

  • Lokacin Layya yana fara wa ne bayan Sallar idi.
  • Anaso a gaggauta yanka da zarar lokaci ya shiga
  • Anaso mai layya ya yanka layyansa da kansa in yana da iko
  • Anaso yayi Bismillah Sannan yayi Kabbara yayin yankan
  • Wanda yayi Layya zai ci daga naman, yayi sadaƙa dashi, yayi kyauta, kuma ya ajiye saura in yaga dama
  • Baya Halatta a baiwa mai gyaran nama ladan aikinsa daga cikin naman layya, ko fata ko kai da ƙafa ba za’a bashi ba a matsayin Lada. Sai dai sadaƙa.

Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates