Yawan Adadin Sahabban Annabi Sallallahu alaihi Wasallama

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: Nawa ne yawan Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam?

Amsa: Godiya Sun Tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, Alhah yayi daɗin tsira wa Shugaban mu Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.

Abune mai matuƙar wuya sanin adadin Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallama. Domin ba awuri ɗaya suke ba, suna rarrabe a birane, da ƙauyuka da garuruwa mabanban ta, kuma babu wani littafi da ake rubuta sunayen wa’inda suka Musulunta a zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Saboda haka sanin Adadin su abisa haƙiƙa abu ne mai wuya.

Kamar yadda Sahabi Ka’ab bin Malik Allah ya ƙara masa yarda ya faɗa a Ƙissar ƙin fitar sa yaƙin tabuka. Yace:

Musulmai suna da yawa tare da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, babu wani Littafi wanda ya tattare sunayen su baki ɗaya.

Bukhari: 4418. Muslim: 2769

Sai dai an rawaito daga Al-Hafiz Abu Zur’a Arrazi Malamin Imamu Muslim Allah yayi masa Rahama yace adadin Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam dubu ɗari da goma sha huɗu ne(114,000)

Al-jami’ Na Khaɗib: 2/293

Sannan akwai riwaya da take nuna cewa adadin su 124,000.

Wannan Adadin abune mai yiwuwa, sai dai kamar yadda mukayi bayani a baya sanin adadin alal haƙiƙa abune mai wuya saboda dalilai da muka bayar a baya, amma zai yiwu sufi wannan adadi, sannan kuma zai yiwu su gaza kaiwa da adadi kaɗan. Domin suna da yawa sosai.

Domin a yaƙin Tabuka Annabi ya fita da Adadin mayaƙa dubu talatin, da dawakai dubu ashirin. Wanda kuma tsaƙanin rasuwar Annabi da wannan yaƙi shekara biyu ce kacal. To idan muka ɗauki wannan Adadi muka haɗa da yawan Mata Musulmai, da yara, da wa’inda suke ƙauye, da wajen gari da wa’inda suke da uzururruka mabanbanta, da wa’inda suke nesa wa’inda basu samu daman fita ba zai yiwu adadin su yakai dubu ɗari. Sannan kuma bayan wannan yaƙi ansamu adadi da yawa da suka Musulunta.

Shiyasa Lokacin da Jabir ɗan Abdullahi yake bayanin yawan wa’inda sukayi Hajji ta ƙarshe tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace:

Lokacin da Annabi ya tsaya akan raƙumar sa, mutane suna kewaye dashi ta ko ina iya ganinka. Ta gaba, ta baya, ta dama da hagu duka haka.

Sahih Muslim: 1218

A taƙaice: an rawaito cewa Adadin Sahabban Annabi mutum dubu ɗari ne da goma sha huɗu. Amma tabbatar da cewa iya adadin su kenan abune mai wuya. Allah yasa mudace, ya kuma ƙara musu yarda.

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates