ZANGA-ZANGA A MAHANGAR MUSULUNCI:

Danna nan domin shiga group na karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo jalingo



Zanga-zangar talakawa saboda neman tabbataccen wani hakki nasu, ko saboda neman tunkude wata barna da ke gudana a cikin kasa tabbas wani al’amari ne da ake gani yana faruwa daga lokaci zuwa lokaci cikin al’ummai daban-daban.
1. Babu sabani a tsakanin Malumanmu cewa: zanga-zangar hayaniya da kone-kone, da kuma zanga-zangar da za yi domin tabbatar da wani zalunci lalle irin wannan nau’i na zanga-zanga ba ya halatta a mahangar Musulunci.
2. Zanga-zangar lumana wacce aka tsara saboda neman wani tabbataccen hakki, ko neman tunkude wani tabbataccen zalunci daga shugabanni, ko daga wasunsu, lalle malamanmu na Musulunci a wannan zamani sun kasu kashi biyu game da hukuncin irin wannan zanga-zangar.

Kashi na farko suka ce: Zanga-zangar talakawa ba ta halatta saboda abubuwa uku:-
1. Akwai kamanta kai da Kafirai cikin yin ta; saboda Kafirai ne aka san cewa suna daukar yin zanga-zanga a matsayin wata hanya ta neman kauda wani munkari; duk kuwa abin da Kafirai za su kebanta da shi, to ba halal ba ne Musulmai su rika yin shi.
2. Ita Zanga-zanga tana daga cikin fararrun al’amura a cikin Addini; duk kuwa abin da yake fararren lamari ne a cikin addini to lalle ba daidai ba ne a yi shi.
3. Dogara da Qa’idar “sadduz Zari’ah”; domin sau da dama yin zanga-zanga saboda neman kauda wani munkari ya kan sabbaba fadawa cikin munkarin da ya fi shi girma, wannan kuwa zai wajabta nisantar yin ta tun farkon fari.
Kashi na biyu kuwa suka ce: Zanga-zangar lumana halal ce “babu wani laifi a yi amfani da ita saboda neman kauda wani munkari, ko tabbatar da wata ayyanannar maslaha; saboda hujjoji kamar haka:-
1. Suka ce: zanga-zangar lumana wani abu ne da Salaf suka yi amfani da shi domin kauda munkari; saboda Imam Abubakar Bin Al-Khallal ya ce cikin littafinsa mai suna Al-Amru Bil Ma’arufi Wan Nahyu anil Munkari shafi na 50:-
((عن محمد بن أبي حرب قال: سالت أبا عبد الله عن الرجل يسمع المنكر في دار بعض جيرانه. قال: يأمره. قلت: فان لم يقبل؟ قال: تجمع عليه الجيران وتهول عليه)).
Ma’ana ((Daga Muhammad Dan Abi Harb, ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (watau Imam Ahmad Dan Hanbal) game da mutumin da yake jin munkari cikin gidan sashin makwabtansa. Sai ya ce: Zai umurce shi (da ya bari). Sai na ce: To in bai karba ba fa? Sai ya ce: sai a tara masa makwabta a tsoratar da shi)).
2. Har yanzu Imam Abubakar Bin Al-Khallal ya riwaito cikin cikin lattafin nasa a shafi na 50-51 ya ce:-
((عن جعفر بن محمد النسائي قال: سمعت أبا عبد الله سئل عن الرجل يمر بالقوم يغنون؟ قال: اذا ظهر له هم داخل. قلت: لكن يسمع الصوت يسمع في الطريق. قال: هذا ظهر عليه ان ينهاهم. ورأى ان ينكر الطبل يعني اذا سمع حسه. قيل: مررنا بقوم وقد اشرفوا من علية لهم وهم يغنون فجئنا الى صاحب الخبر فاخبرناه. فقال: لم تكلموا في الموضع الذي سمعتم؟ فقيل: لا. قال: كان يعجبني ان تكلموا لعل الناس كانوا يجتمعون وكانوا يشهرون)).
Ma’ana: ((Daga Ja’afar Dan Muhammad An-Nasaaii ya ce: Na ji Abu Abdillah an tambaye shi game da mutumin da ya wuce wasu mutane suna wake-wake? Sai ya ce: idan ya bayyana gare shi cewa suna cikin gida. Sai na ce: sai dai ana jin sauti ana ji a cikin hanya. Ya ce: wannan ya zama wajibi a kan shi ya hana su. Kuma ina ganin ya yi inkarin babbar ganga, watau idan suka ji motsin shi. Sai aka ce: mun wuce wasu mutane suna kan wani bene nasu suna ta wake-wake, sai muka je wa jami’in hukuma wanda ake kai masa labarai aka ba shi labari. Sai ya ce: ba su yi magana cikin maudhu’in da kuka ji ba? Sai aka ce: a’a. Sai ya ce: ya kasance yana kayatar da ni su yi magana, watakila mutane za su kasance suna taruwa suna yayata lamarinsu)).
Kamar yadda kuke gani karara a cikin wadannan atharai biyu Imam Ahmad ya yi fatawar mutane su taru saboda inkarin munkari saboda a tsoratar da mai munkarin da kuma yayata lamarinsa.
3. Abul Faraj Abdurrahman Ibnul Jauzii wanda ya rasu shekarar hijira 527 ya ba labarin wata zanga-zangar da Malaman Musulunci na Ahlus Sunnah suka shirya saboda neman Mahukunta su kauda wani munkari da yake gudana; ya ce a cikin littafin tarihinsa mai suna: Al-Mutazim Fi Tarikhil Muluuki Wal Umam 8/240:-
((واجتمع في يوم الخميس رابع عشر المحرم خلق كثير من الحربية والنصرية وشارع دار الرقيق وباب البصرة والقلائين ونهر طابق بعد ان أغلقوا دكاكينهم وقصدوا دار الخلافة وبين ايديهم الدعاة والقراء وهم يلعنون اهل الكرخ، وازدحموا على باب الغربة وتكلموا من غير تحفظ في القول، فراسلهم الخليفة ببعض الخدم: اننا قد انكرنا ما انكرتم، وتقدمنا بان لا يقع معاودة، ونحن نغفل في هذا ما لا يقع به المراد. فانصرفوا وقبض على ابن الفاخر العلوي في آخرين، ووكل بهم في الديوان. وهرب صاحب الشرطة؛ لانه كان أجاز لأهل الكرخ ما فعلوا)).
Ma’ana: ((Mutane da yawa suka hadu ranar alhamis sha hudu ga Muharram, daga Harbiyyah, da Nasriyyah, da Shari’u Darir Raqiq, da Babul Basrah, da Qalaawiin, da Nahru Tabiq bayan sun kukkulle kantuna sun nufi Fadar Khalifah, a gaba gare su akwai Masu wa’azi da Makaranta Alkur’ani suna ta tsine wa jama’ar Karkh, suka yi cinkoso a kofar gurbah, suka yi ta magana ba tare da wani rufa-rufa ba. Khalifah sai ya aiko wasu yaran Sarki zuwa gare su (da sakon): Lalle mu mun yi inkarin abin da kuka yi inkarin shi, kuma muna gabatar da (akawalin cewa) haka ba zai sake faruwa ba, kuma mu za mu tushe aukuwar dukkan abin da ba shi ne manufa ba. Sai suka watse, kuma aka kama Ibnul Faakhir Ba’alawe da ma wasu daban. Kuma aka jingina su cikin Diwani, sannan shugaban yan sanda ya gudu, saboda shi ne ya ba wa jama’ar Karkh izinin yin abin da suka yi)).
Wannan zanga-zangar ta faru ne a shekarar hijira 458 watau yau shekaru 975 ke nan da suka wuce. Idan kun dubi maganar Imam Ahmad sannan kuka dubi wannan kissa za ku fahimci cewa zanga-zanga saboda inkarin wani munkari lamari mai asali a cikin Musulunci, ba yi da alaka da abin da za a kira shi da cewa: Shi Kwaikwayon kafirai ne.
4. Da za a kaddara cewa: zanga-zanga wata sabuwar wasilar inkarin munkari ne ba wai tsohuwa ba ce a cikin Musulunci, to da ma hakan ba zai maida ita haramun ba, ko kuwa hakan ba zai sanya ta cikin jerin bidi’o’i a cikin Addini ba, saboda su Wasaa’il matukar dai ba su kasance haramun ba ne saboda zatinsu, ko kuwa matukar dai ba su kasance wani shi’ari ba ne kebabbe ga kafurai to babu wani laifi Musulmi su fa’idantu da su a cikin Maqaasidush Shari’ah, kamar yadda dai Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yake cewa cikin Majmu’ul Fatawa 30/206 watau kamar fa’idantuwa da kayayyakin gini, da saka, da sauran sana’o’i. Kuma a wannan zamani namu sai mu ce kamar su lasfikar da za a kira salla da ita saboda Kara sauti. Kai kamar rike tasbaha saboda kidayar lafuzan zikiri, kun san cewa babban Shaikhinmu Sheik Ibnu Uthaimiin yana ganin halaccin amfani da shi, kamar yadda ya zo cikin littafin: Jalasaatu Wa Fataawa Ibni Uthaimeen 8/32 saboda ita tasbaha tana daga cikin babi ne na Wasaa’il.
WANI TSOKACI:
1. Idan kuna cikin Kasar da ta haramta yin zanga-zanga to lalle wajibi ne ku bi dokar Kasar saboda tabbatar da maslahar zaman lafiya cikin Kasa.
2. Idan kuna cikin Kasar da take halatta yin zanga-zanga amma bayan samun izini na musamman to dole kafin yin zanga-zangar ku sami izini na musamman daga mahukunta tukun.
3. Idan kuna cikin Kasar da take halatta sakakkiyar zanga-zanga to halal ne ku shiriya zanga-zangar lumuna a duk lokacin da kuke ganin akwai maslaha cikin yin hakan. Allah Ya taimake mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories