By: Dr. Ibrahim Jalo
1. Yana daga cikin ayyukan lada da al’ummar Musulmi za su yi: azumtar sittu Shawwal, watau yin azumin kwana shida cikin watan Shawwal bayan an gama azumtar Watan Ramadan mai yawan alfarma. Wannan kuwa shi ne abin da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah ya zo da shi, kuma Jumhurin Al’ummar Musulmi suke yin aiki da shi, sai wanda ilmin wannan sunnah bai kai gare shi ba, wannan kuwa za a yi masa uzuri saboda wannan larurar.
2. Daga cikin wadanda za a yi musu wannan uzuri akwai babban Malami a duniyar Musulunci Imam Malik Bin Anas Allah Ya yi masa rahama, inda yake rubuce cikin littafinsa Muwattaa a karshen Kitabus Siyam, kamar haka:-
((قال يحيى: سمعت مالكا يقول: في صيام ستة ايام بعد الفطر من رمضان؛ انه لم ير احدا من اهل العلم والفقه يصومها، ولم يبلغني ذلك عن احد من السلف، وان اهل العلم يكرهون ذلك ويخافون بدعته، وان يلحق برمضان ما ليس منه اهل الجاهلية والجفاء لو راوا في ذلك رخصة عند اهل العلم، وراوهم يعملون ذلك))
Ma’ana: ((Yahya ya ce: Na ji Malik na cewa game da azumtar wasu kwana shida bayan shan ruwa daga Ramadan: cewa shi bai ga daya daga cikin ma’abuta Ilmi da Fikhu na azumtar su ba, kuma hakan bai zo mini daga wani mutum daga Salaf ba, kuma ma’abuta Ilmi suna karhanta hakan suna tsoron zamantowarsa bidi’ah, kuma kada ma’abuta jahiliyyah da nisantar shari’ar su hada Ramadan tare da abin da ba daga gare shi yake ba in sun ga izinin yin haka daga ma’abuta Ilmi: su gan su suna aikata hakan)). Wannan shi ne fahimtar Imam Malik game da azumtar Sittu Shawwal, Wannan kuwa ba wata mas’ala ba ce don an sami haka daga wani Malami babba kamar shi Imam Malik; saboda babu wani a duniyan nan da za a ce ya san dukkan wani hadithi da manzon Allah ya taba fada, a’a ko wani malami akwai abin da ya sani, akwai kuma abin da ya buya a gare shi koda kuwa abin da ya buyar ba shi da yawa.
3. A nan da wani zai ce: Ai abin da aka hana kawai a matafiyar Imam Malik shi ne: fara yin azumin a ranar biyu ga Watan Shawwal, amma kana iya farawa daga uku har zuwa sama! Sai a ba shi amsa da cewa: Wani nassin Annabi mai tsira da amincin Allah ne ya hana a fara azumin daga rana ta biyu? Tabbas babu wanda ya isa ya kawo wannan nassi daga Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah, kai a gaskiya ma babu wannan nassin hatta daga bakin shi kan shi Imam Malik Allah Ya yi masa rahama.
4. Sannan har yanzu daga wannan nassin da ya zo daga bakin Imam Malik ne za mu fahimci cewa: lalle ya hurta wasu abubuwa muhimmai dai dai har guda biyar kamar haka:-
Na daya: shi dai Imam Malik da idonsa bai ga ko da mutum daya ba cikin ma’abuta Ilmi da Fikhu da yake azumtar Sittu Shawwal.
Na biyu: Babu wani labari da ya zo masa daga ko da mutum guda ne daga cikin Salaf cewa yana azumtar Sittu Shawwal.
Na uku: Ma’abuta Ilmi suna karhanta azumtar Sittu Shawwal.
Na hudu: Ma’abuta Ilmi suna tsoron zamantowar azumtar Sittu Shawwal wata bidi’ah ce da wasu suka kirkira.
Na biyar: Ma’abuta Ilmi suna tsoron kada ma’abuta jahiliyyah da nisantar shari’ah su hada Ramadan da abin da yake ba Ramadan ba in har sun ga ma’abuta Ilmi sun ba da izinin azumtar Sittu Shawwal, ko in sun gan su suna azumtar sa da kansu.
5. Lalle uzurin Imam Malik a nan shi ne: shi dai bai sami kaiwa ga hadithin da Imam Muslim ya ruwaito cikin sahihinsa ba hadithi na 1164 na cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((من صام رمضان ثم اتبعه ستا من شوال كان كصيام الدهر))
Ma’ana: ((Wanda ya azumci Ramadan sannan ya biyar da shi shida daga Shawwal ya kasance kamar azumtar Zamanin ne)). Wannan kuwa ba wani abin mamaki ba ne saboda babu wani mutum guda a duniyan nan da za a ce ya yi ihaadar dukkan hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya yi wa Imam Malik rahama ya kuma sanya Aljannar Firdausi ita ce makomarsa, Ya kuma ba mu ikon dabbaka wannan Sunnah muhimmiya ta azumtar sittu Shawwal. Ameen.
Leave a Reply