​HADITHIN KHASEEB BIN JAHDAR

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai Rubutu: Dr. Ibrahim Jalo


Imamut Tabraaniy ya ruwaito cikin littafinsa Almuujamul Kabiir hadithi na 16,563, daga Sahabi Mu’azu Dan Jabal ya ce:-
((كان النبي صلى الله عليه وسلم اذا كان في صلاته رفع يديه قبالة أذنيه، فإذا كبر ارسلهما، ثم سكت، وربما يضع يمينه على يساره)).
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance idan yana cikin sallarsa sai ya daga hannu daura da kunnensa, idan ya yi kabbara sai ya sake su, sai kuma ya yi shiru, wani lokaci ma nakan gan shi yana dora damansa a kan hagunsa)). 
Da farko dai ya kamata a san cewa wannan hadithi maudhuu’i ne, watau hadithi ne wanda cikin isnadinsa akwai makaryaci kazzaabi wannan kuwa shi ne: Khaseeb Bin Jahdar, mun kira shi kazzabi saboda abin da ya zo cikin littafin Miizaanu Litidaal 1/653 kamar haka:-
((الخصيب بن جحدر: عن عمرو بن دينار، وأبي صالح السمان، كذبه شعبة والقطان وابن معين. وقال احمد: لا يكتب حديثه. وقال البخاري: كذاب استعدى عليه شعبة)).
Ma’ana: ((Khaseeb Bin Jahdar, daga Amr Bin Deenar da Abu Salihis Sammaan: Shu’ubah, da Qattaan, da Ibnu Ma’en sun karyata shi. Ahmad ya ce: Ba a rubuta hadithinsa. Bukharii ya ce: Makaryaci ne, Shu’ubah ya yi bayanin karyarsa)).
Na biyu: Yakamata a san cewa lalle da za a kaddara cewa wannan hadithin Hadithi ne da yake ingantacce a gurin malaman Hadithi, to da ba zai isa a dauke shi a matsayin hadithin da yake tabbatar da cewa Annabi mai tsira da amincin Allah yana yin sadlu a cikin sallarsa ba, a’a, sai dai  a fassara shi da cewa: yana nufin bayan Annabi mai tsira da amincin Allah ya daga hannayensa daura da kunnuwansa a lokacin kabbarar harama to ya kan sake hannayen nasa ne zuwa kirjinsa. Dole ne a yi irin wannan fassarar saboda hadithin ya dace da sauran hadithai ingantattu da suka zo cikin wannan babi na inda Annabi yake sanya hannayensa a halin tsayuwa bayan kabbarar harama. Wannan shi ne ma ya sa babban masanin ilmin hadithi Alhaafiz Ibnu Hajar ya ce cikin littafinsa mai suna Talkhiisul Habiir 1/554:-
((تنبيه: قال الغزالي: سمعت بعض المحدثين يقول: هذا الخبر انما ورد بانه يرسل يديه الى صدره، لا انه يرسلهما ثم يستأنف رفعهما الى الصدر. حكاه ابن الصلاح في مشكل الوسيط)).
Ma’ana: ((Fadakarwa: Gazaalii ya ce: Na ji sashin malaman hadithi na cewa: Wannan hadithi ya zo ne a kan cewa yana sake hannayensa ne zuwa girjinsa, ba wai yana sake su ba ne, sannan daga baya ya daga su zuwa girji ba. Ibnus Salaah ne ya hikaito shi cikin “Mushkilul Wasiit”)). 
Da wannan ne Al’umma za su kara fahimtar cewa ba daidai ba ne a kafa hujja da hadithin karya na Khaseeb domin a guje wa yin aiki da ingantattun hadithan umurni, da aiki, da tabbatarwa na sanya dama a kan hagu a lokacin da Musulmi yake yin salla ba.
 Muna rokon Allah Madaukakin Sarki muna kaskantar da kai a gabanSa da ya taimake mu Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories