Shimfida: Annabi (saw) yana cewa “ musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi, kada ya wulaƙan ta shi, kada ya miƙa shi ga abokan gaban shi. Sannan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: tsoron Allah anan yake (ya nuna kirjinsa har sau uku). Ya ce ” ya isa mutum sharri ya wulaƙan ta ɗan uwan shi musulmi. Kowani musulmi akan musulmi haramun ne dukiyansa, da jininsa, da mutuncinsa”
Tambayoyi dake ciki:
- Hallacin sanya riga mai ɗauke da munanan kalaman shirka ko batsa.
- Hukuncin ruwa ko jinin da yake fitowa bayan tsarki?
- Wanda yayi wutri a farkon dare, yaya zai yi idan zai yi a ƙarshen dare?
- Ya hallata mutum yayi addua a “post” watau saƙon mutuwa da a ka sa a “Facebook” ko da mutum bai san mamacin mutumin kirki ne ko ba haka ba?
- Idan uba yayi kyautar gidaje ma ‘ya’yanshi daga baya sai ya haifi wasu lokacin da bayi da wasu gidajen da zai iya kyauta ma ‘ya‘yansa na baya yaya hukuncinsa?
- Yaushe aka fara tattara hadithan Annabi (saw)?
- Hukuncin wanda ya riski tahiyya a sallar jum’a.
- Hukuncin ɗan achaɓa mai ɗaukan fasinjoji zuwa chochi!
- Shawara ga miji mai tafiye-tafiye da mata ɗaya, ya bar ɗayan!
- Mutum zai iya haɗa shanun sa da na iyalansa domin fitar da zakka?
- Matsayin musulmi ya shiga maƙabartan kafirai domin binne ɗan’uwan shi kafiri
- Ma’anar “khunnas” da “kunnas” da su ka zo aya 15-16 na sura- At-Takwir).
- Shin mutum zai iya kyauta ta bajinta wa matar shi da ta kasa iya girki da sauransu, domin sawwakƙe mata?
- Menene hallacin yi ma jariri kiran sallah ko huɗuba?
- Mutum zai iya karanta littafin ɗan uwanshi ba tare da iznin shi ba?
Download
Leave a Reply