005 Fatawowin Rahama By Dr. Sani Umar Rijiyar Lemu 25th January 2020

Shimfida: Annabi (saw) yana cewa “ musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi, kada ya wulaƙan ta shi, kada ya miƙa shi ga abokan gaban shi. Sannan Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: tsoron Allah anan yake (ya nuna kirjinsa har sau uku). Ya ce ” ya isa mutum sharri ya wulaƙan ta ɗan uwan shi musulmi. Kowani musulmi akan musulmi haramun ne dukiyansa, da jininsa, da mutuncinsa”

Tambayoyi dake ciki:

 1. Hallacin sanya riga mai ɗauke da munanan kalaman shirka ko batsa.
 2. Hukuncin ruwa ko jinin da yake fitowa bayan tsarki?
 3. Wanda yayi wutri a farkon dare, yaya zai yi idan zai yi a ƙarshen dare?
 4. Ya hallata mutum yayi addua a “post” watau saƙon mutuwa da a ka sa a “Facebook” ko da mutum bai san mamacin mutumin kirki ne ko ba haka ba?
 5. Idan uba yayi kyautar gidaje ma ‘ya’yanshi daga baya sai ya haifi wasu lokacin da bayi da wasu gidajen da zai iya kyauta ma ‘ya‘yansa na baya yaya hukuncinsa?
 6. Yaushe aka fara tattara hadithan Annabi (saw)?
 7. Hukuncin wanda ya riski tahiyya a sallar jum’a.
 8. Hukuncin ɗan achaɓa mai ɗaukan fasinjoji zuwa chochi!
 9. Shawara ga miji mai tafiye-tafiye da mata ɗaya, ya bar ɗayan!
 10. Mutum zai iya haɗa shanun sa da na iyalansa domin fitar da zakka?
 11. Matsayin musulmi ya shiga maƙabartan kafirai domin binne ɗan’uwan shi kafiri
 12. Ma’anar “khunnas” da “kunnas” da su ka zo aya 15-16 na sura- At-Takwir).
 13. Shin mutum zai iya kyauta ta bajinta wa matar shi da ta kasa iya girki da sauransu, domin sawwakƙe mata?
 14. Menene hallacin yi ma jariri kiran sallah ko huɗuba?
 15. Mutum zai iya karanta littafin ɗan uwanshi ba tare da iznin shi ba?

Download

Click Here to Support our work

One Comment

Leave a Reply

%d bloggers like this: