Wannan Batu Haka Yake
Masu hikimar zance sukan ce
“Mutum makiyin abin da bai sani
ba ne”. Babu ko shakka duk wanda
ya kalli mafi yawan masu fada da
Ahlissunnah, zaka gansu suna
fadan ne akan jahiltar hakikanin
tsarin (wato manhajin)
Ahlissunnah, wanda aka gina shi
akan ilimi gaskiya da adalci, mafi
yawansu suna dogara ne akan
abin da munanan malami suka
fada musu, ko kuma a kan wasu
dabi’u da ta’adu na jahilan
Ahlissunnah.
Alal misali idan mutum ya dauki
bajimin malamin nan na sunnah,
shahararre mai dimbin sani,
shehun musulunci Ibnu Taimiyyah,
zai ga da yawa daga cikin masu
zaginsa da kafirta shi da munana
shi, basu san komai a kan tarihinsa
ba, basu karanta littattafansa ba,
kawai suna daukar abin da
makiyansa suka rubuta a kanshi na
karya da taawilin maganganunsa
su shiga yadawa da jayayya a kai,
amma duk wanda yake karanta
littattafansa da idon basira zai yi
mamakin irin adalci da tausasa da
fadin gaskiya na wannan bawan
Allah, Allah ya jikan wani
malaminmu a Jami’ar Musulunci ta
Madinah, ya kasance yana cewa,
“Mafi yawancin mutane suna
karanta littattafan Ibnu Taimiyyah
amma basa daukar ladabinsa da
halayensa” Don haka dan uwa
zama mai adalci wajen yin hukunci
ga wani mutum ko kungiya ko
wasu mutane, karanta abin da
suka rubuta da kansu, koma cikin
jiga-jigan littattafansu, tana nan ne
zaka gane gaskiya, Allah ya raba
mu da son zuciya.
Leave a Reply