Addu'a Takwabin Mumini

Danna nan domin shiga karatu Online

Addu’a shine babban takwabi awurin mumini wanda yafi ko wani irin Makami da zaiyi amfani dashi, babu wani abu da ya kamata mumini ya runguma ya lazimta a kowani lokaci irin addu’a, domin shine ibada, kamar Yadda Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fadi kuma shine hanyar tsira daga kowani irin musiba, da damuwa, da cututtuka, na jiki da na zuciya. sannan babu wani abu mai mayar da Qaddara sai Addu’a, Sannan Allah madaukakin Sarki yana son Masu Rokonsa.
To Amma ya akeyin addu’a? Kuma meye sabuban karban addu’a da sabuban rashin karbansa? Wannan shine zamu tattauna akansa cikin wannan rubutu namu.
1. Sabuban Karban Addu’a da Sabuban Rashin Karbansa:

  • Ikhlasi: Kamar yadda ikhlasi shine kashin bayan ibadodi haka nan yake a addu’a, shima yana bukatar ikhlasi, ka roki Allah shi kadai, ba tare da ka hadashi da kowa.
  • Samun Yaqini: babban sababin karban addu’a shine yaqini, ya zamto cewa kana addu’a kuma kana samun Yaqini acikin zuciyarka cewa Allah Madaukakin Sarki zai amsa maka, kada kana addu’a kana cewa shin Allah zai amsa kuwa? Ko bazai amsa ba. Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Ku roqi Allah kuna masu Yaqinin zai amsa muku”
  • Cin Halal: yana daga cikin sabbuban karban Addu’a Ta’amuli da Halal, ya zamto cewa mutum baya harka da haram, domin cin haram yana sabbaba rashin karban Addu’a.

Daga Cikin Sabuban Rashin Karban Addu’a

  • Guluwwi Cikin Addu’a: Yana daga cikin sabbuban rashin karban Addu’a yin addu’a wanda akwai guluwwi aciki ko kuma tsabon Allah, Allah baya amsa irin wa’innan addu’oin.
  • Zunubai: Yawan zunubi yana hana karban Addu’a,
  • Gafalar Zuciya: gafalar zuciya ma yana sabbaba rashin karban Addu’a, ya zama mutum na rokon Allah amma hankalinsa na wani wiri daban.

Wa’innan Abubuwa kadan kenan daga cikin sabuban rashin karban Addu’a, Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace “ba wani bawa da zai roki Allah, wannan rokon ya zamto babu tsabon Allah aciki ko kuma yanke zumunta face Allah ya bashi adalilin wannan addu’a dayan abu uku, kodai Allah ya bashi abinda ya roka anan duniya, ko kuma Allah ya ajiye masa ita a lahira, ko kuma Allah ya toshe masa wani sharri kwatankwacin wannan addu’a tashi”
Wannan Hadisi yana nuna mahimmancin yin Addu’a, domin koda mutum bai samu biyan bukatan abinda ya roka ba yasan Baiyi a banza ba, akwai alkhairi mai dinbin yawa yana jiransa.
Lokutan Da Ake Karban addu’a

  • Tsakanin Kiran Sallah Da Iqama: Manzon Allah(Sallallahu Alaihi wasallam) yace: “Ba’a Mayar da Addu’ar da akayishi tsakanin Kiran Sallah da iqama”. Wannan lokaci yana farawa ne tun bayan an kira sallah har zuwa tada sallah, duka lokacin mutum zai iya yin addu’a aciki kuma insha’Allah Allah zai amsa masa.
  • Tsakiyar dare ko karshensa: yana daga cikin lokutan karban addu’a tsakiyan dare ko dayan bisa ukunsa, lokacin da Allah yake sauko wa zuwa saman duniya(irin sauko wa da ta dace dashi).
  • Lokacin sujudi: Annabi(Sallallahu alaihi wasallam) yace: “Mafi kusanci da bawa zai kasance zuwa ga ubangijinsa shine lokacin da yake sujudi, ku yawaita addu’a acikinta”
  • Lokacin zaman liman domin Khudbah Ranar Juma’a: tun daga zaman liman har zuwa tada Sallah, shima wannan lokaci ne da ake karban addu’oi.
  • Bayan Tahiya ta Karshe:
  • Karshen Ranar Juma’a Bayan La’asar har zuwa Faduwar Rana

Wannan kadan kenan daga cikin lokuta Masu mahimmanci da mutum ya kamata ya lazimci addu’a aciki, sannan dadi da kari yana da kyau mutum ya zabi addu’oi masu kyawawan lafuza kamar irin addu’oin da annabi ya koyar.
Falalar Suratul Fatiha wurin magance cututtuka: zan rufe wannan rubutu da hakaito maganar ibnul Qayyim yadda yake cewa:

Na zauna a Makka, Cututtuka sukan sameni, bana kuma samun likita ko magani, sai na kasance ina maganin wannan cututtuka da fatiha, kuma ina ganin tasirinta mai matukar ban mamaki, sai na kasance ina baiwa wanda ya kawomin koken wani radadi wannan fatiha, kuma da yawa daga cikinsu sukan warke da sauri.

.
Dalilan yin Magani da Fatiha:
Akwai hadisi ingatacce wadda Bukhari ya rawaito. wasu sahabban Annabi sunyi tafiya sai suka biya ta wani gari, suka nemi mutanen garin su basu masauki sai suka ki, sai Kunama ya sari shugaban wa’innan mutane, sai sukazo wurin sahabban Annabi suka tambayesu ko suna da wani magani, sai sukace eh: amma baku karbi bakoncinmu ba sabida haka kafin muyi masa magani sai dai in zaku saka mana wani abu, sai wa’innan mutane suka amince cewa zasu basu wasu tumakai, sai wani daga cikin sahabbai ya karanta wa shugaban wannan mutane fatiha, Allah kuma ya bashi sauki ya tashi kaman babu wani abinda ya sameshi……… Suka dawo wurin Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) kuma ya tabbatar dasu akan wannan abu da sukayi..
Allah Amsa Mana Addu’oin mu baki daya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates