Addu’ar fita daga gida

Danna nan domin shiga karatu Online

Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

An rawaito daga Uwar Muminai Ummu Salma Allah ya ƙara mata yarda tace:

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan zai fita daga gida yana faɗin “Allahumma inni Auzu bika an Adilla au udalla, au azilla au uzalla, au azlima au uzalama, au ajhala, au yujhala alayya

Abu dawud: 5094. Annasa’i: 5486

Fassarar Addu’ar: Allah ina neman ka tsari kada na ɓata, ko na ɓatar da wani, ko in kauce kan tafarki madaidaici wurin aikata saɓo da sani na ko ba da sani na ba, ko nayi zalunci ko a zalunce ni. ko nayi jahilci ko ayi min Jahici,

Wannan Addu’a Annabi yanayin sa ne idan zai fita daga Gida.

An rawaito daga Anas ɗan Malik Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace;

Wanda yace: “Bismillahi tawakkaltu Alallahi wala haula wala ƙuwwata illa billahi” za’a ce masa: an isar maka, an kiyaye ka. Sannan shaiɗan zai kauce ga barin sa.

Sunanut-Tirmidhi: 3426

Sharhin Hadisin: Wanda yace Da sunan Allah, na dogara ga Allah, babu wani iyawa ko ƙarfi sai tare da Allah. Allah maɗaukain sarki zai tsare shi, ya kiyaye shi, sannan shaiɗan zai kauce masa ba zai iya cutar dashi ba.

Wannan zikiri yana da matuƙar mahimmanci, ya dace Kowani Musulmi ya lazimce shi. Allah ya tsare mu yasa mu dace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates