ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wa Ala Alihi
Wasallam
Fitowa ta 17
Haduwar Dare Daya Tarihin Har
Abada
A cikin tafiye-tafiyensa na neman
arziki, watarana Hashim (Kakan
manzon Allah (S) na biyu ya yada
zango a birnin Madina (Ana kiran ta
Yathrib a wancan lokaci). Sai ya sauka
a gidan wani bawan Allah ana ce ma sa
Amru bn Labid, wanda ya fito daga
shahararren gidan nan na Banuj
Najjar. A gidan ne kuma Allah ya
daidaita kansa da Salma ‘yar wannan
gidan kuma aka daura ma sa aure da
ita. Bayan da ya yi baiko da amaryar
tasa suka samu wani dan lokaci sai ya
wuce zuwa wurin kasuwancinsa, in da
a can ne ya gamu da ajalinsa a birnin
Gaza na kasar Falasdinu. Bai sani ba
ashe ya bar Salma da cikin da namiji
wanda ta sa ma sa suna Shaiba.
Wannan duka ya faru a shekarar
497M. A wata ruwaya kuma an ce ya
zo da ita Makka bayan dawowar sa
daga birnin Sham inda ta samu ciki,
sa’annan ya mayar da ita wurin
iyayenta a Madina bisa sharadin da
ubanta ya gindaya ma sa. Amma
ruwayoyi sun hadu a kan cewa, an
haifi Shaiba bayan cikawar uban nasa,
kuma ita ce ta rada ma sa wannan suna.
Fiqhus Sirah, na Ghazali, shafi na 64.
Daga bisani dan uwan Hashim wato
Muttalib wanda aka san shi da tsananin
ibada da kyawon hali da fada da
zalunci ya yanke shawarar zuwa
Madina domin ya dauko dan kanensa
Shaiba. To, a lokacin da suka isa
Makka Shaiba ya yi kutut-kutut saboda
halin tafiya. Don haka da mutane suka
tambaye shi ina ka samu wannan
yaron? Sai ya ji nauyin ya ce ma su
“dana ne”. Don haka sai ya ce ma su
“bawana ne”. Daga nan ne aka rinka
kiran sa “Abdulmuttalib”. Amma kun
ji asalin sunansa “Shaiba”. Shi ne
kuma mahaifin mahaifin manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam. Ar-Rahiq
Al-Maktum, shafi na 58-59.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates