ALKAKI DA RUWAN ZUMA
Ingantaccen Tarihin Fiyayyen Halitta
Sallallahu Alaihi Wasallam
Fitowa Ta 19
Aure Mafi Albarka
Bayan da Allah cikin ikonsa ya kubutar
da Abdullahi daga kaifin wuka ne sai
tauraruwarsa ta fara dagawa,
mahaifinsa kuma ya ga ya dace ya
nema ma sa aure. Take aka yi matsaya
a kan hada aurensa da wata mata ‘yar
babban gida, mai kwarjini, irin wacce
ake cewa “son kowa, kin wanda ya
rasa”. Sunanta Aminatu ‘yar Wahbu
dan Abdumanafi. Ta fuskar dangantaka
ta fi shi kusa da gwarzon kabila;
kakanta na farko Abdumanafi, shi ne
kakan mahaifinsa.
Bayan da aka yi baikon ta ne da wani
dan lokaci sai Abdullahi ya kama
hanyarsa ta zuwa fatauci sana’ar da ya
gada ga iyayensa. A kan hanyarsa ne
kuma ya gamu da ajalinsa a birnin
Madina gurin kawunnen mahaifinsa
kuma a can aka yi ma sa jana’iza.
Allah sarkin sarauta! Abdullahi ya tafi
amma ya fitar da ajiyar Allah da ke
cikin jikinsa wacce aka kaddara zata
fito da dan Adam ma fi daraja da
girman matsayi a bayan kasa.
Abdullahi ya tafi ya bar amaryarsa
dauke da cikin fiyayyen halitta
Sallallahu Alaihi Wasallam. (Zad Al-
Ma’ad, na Ibn Al- Qayyim (1/17).
Leave a Reply