Abu Huraira Allah ya kara masa yarda ya rawaito hadisi daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:
تُفْتَحُ أبْوابُ الجَنَّةِ يَومَ الإثْنَيْنِ، ويَومَ الخَمِيسِ، فيُغْفَرُ لِكُلِّ عَبْدٍ لا يُشْرِكُ باللَّهِ شيئًا، إلَّا رَجُلًا كانَتْ بيْنَهُ وبيْنَ أخِيهِ شَحْناءُ، فيُقالُ: أنْظِرُوا هَذَيْنِ حتَّى يَصْطَلِحا، أنْظِرُوا هَذَيْنِ حتَّى يَصْطَلِحا، أنْظِرُوا هَذَيْنِ حتَّى يَصْطَلِحا.
رواه مسلم ٢٥٦٥
Ana buɗe ƙofofin Aljannah ranar litini da ranar Alhamis, sai a gafarta wa kowani bawa wanda baya haɗa Allah da wani(Shirka) sai dai mutumin da akwai adawa da gaba tsaƙaninsa da ɗan’uwansa Musulmi, sai ace: ku jira wa’innan har sunyi sulhu tsaƙaninsu kafin a gafarta musu
Muslim: 2565
Wannan hadisi yake nuna falalar Allah ga bayinsa ta yadda ya sawwaƙe musu hanyoyin samun gafararsa, ya sanya kowani Rananr Alhamis da juma’a ranace da ake gafarta wa Mutane.
Sannan kuma wannan hadisi yana nuna mana girman laifin Gaba tsaƙanin Musulmi, musamman kan abinda bai taka kara ya karya ba, ya kamata Musulmi ya zamto mai haƙuri kuma mai yafiya domin da haka ne zai sami wannan gagarumin falala ta gafarar Allah.
Ya kamata mu sani cewa baya halatta Musulmi ya ƙaurace wa ɗan’uwansa fiye da kwanaki uku, duk Tsaɓani da kuka samu da ɗan’uwanka kayi ƙoƙari kuyi sulhu kada ku wuce kwana uku kuna gaba, wannan haramun ne, kuma ba gazawa bane kai ka fara yi masa magana idan shi yaƙi fara yi maka, idan kayi haka zaka fishi alheri a wurin Allah. Allah yasa mudace
Leave a Reply