Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Allah madaukakin Sarki yace:
Wa’incan Manzannin Mun fifita sashin su akan sashi, daga cikinsu akwai wanda Allah yayi musu magana
Suratul Baqara: 253
Wannan Aya tana nun cewa acikin Manzanni akwai wa’inda Allah yayi Musu magana ba tare da shamaki ba ko ɗan aike a tsaƙani.
Ga sunan Kamar haka:
1. Annabi Adam Alaihissalam: Annabi Adam shine farkon wanda Allah yayi masa magana ba tare da shamaki ba ko ɗan aike
An rawaito hadisi daga Abu Umamatal Bahili Allah ya ƙara masa yarda yace Wani Mutum ya tambayi Annabi yace Masa Shin Adamu Annabi ne? Sai yace eh ƙwarai Kuma wanda Allah yayi masa magana. Sai yace masa nawa ne tsaƙanin sa da Annabi Nuhu? Sai yace ƙarni 10
Ibnu Hibban: 14/69
2. Annabi Musa Alaihissalam: Shine na biyu cikin Wanda Allah yayi Musu magana ba tare da shamaki ko ɗan aike ba.
Allah maɗaukakin sarki yace:
Kuma Allah yayi magana wa Annabi Musa Magana
Suratun-Nisa’: 164
3. Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi: Shine na uku kuma na ƙarshe da Allah yayi wa Magana ba tare da shamaki ko ɗan aike ba.
Hadisin Mi’iraji shi yake Tabbatar da cewa Allah yayi magana da Annabi Muhammad tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi lokacin da yaje ya karɓo Sallah, Annabi Musa yace masa ya koma wurin Allah ya nemi ragi domin Al’ummar sa baza su iya ba.
Hadisin Bukhari ya rawaito shi: 3674. Muslim ya rawaito shi: 162
Alhafiz Ibnu Hajar Allah yayi masa rahama yace:
Hadisin Mi’iraji yana daga cikin mafi ƙarfin dalilai da suke nuna cewa Allah yayi magana da Annabi ba tare da shamaki ba.
Fathul Bari: 7/216
Wa’innan sune Annabawa da Sukayi magana da Allah ba tare da shamaki ba ko ɗan aike.
Ɗaya daga cikinsu shine Allah ya ambace shi a Alqur’ani. Shine Annabi Musa Alaihissalam.
Sheikh Abdurrahman Mahmud yace:
Wataƙila (ilimi na wurin Allah) dalilin da yasa Allah ya ambaci Maganar da yayi wa Annabi Musa bai ambaci na Annabi Adam da Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare su ba a Alqur’ani shine:
Allah yayi magana da Annabi Musa ne a ban ƙasa, yana yanayin sa na ɗan Adam, tsaɓanin Maganar da yayi wa Annabi Adam wanda yayi shi ne lokacin yana sama, haka nan Annabi Muhammad, yayi magana dashi ne lokacin da yayi Mi’iraji zuwa sama,
Taisir Lam’atul itiqad: 152
Leave a Reply