Abu ne mai wahalar gaske a samu
wata gamayya ta Al’umma ko wata
hadaka ta Al’umma wacce za a ce
ba a tsara wa gudanar da ita
constitution ba: Ko dai a rubuce, ko
kuwa ba a rubuce ba.
Wannan shi ya sa ma a lokacin da
Annabi mai tsira da amincin Allah
ya yi hijira zuwa Madina bai bata
wani lokaci ba, a’a tun a shekarar
farko ta hijira ne ya rubuta wa
jaririyar Daular Islama constitution:
watau abin da tsoffin littattafan
tarihi na Musulunci ke kira: AL-
WATHIIQAH ma’ana: Abin da aka
kyautata shi kuma aka amince da
shi. Wani lokaci kuma suna kiran
shi da suna: AS-SAHIIFAH ma’ana:
Littafi. Sannan sabbin littattafan
tarihin Musulunci kuma suna kiran
shi da suna: DUSTUURUL
MADINAH ma’ana constitution din
Madina.
Ga tarjamar nassin constitution din
kamar yadda ya zo a rubuce cikin
littafin: Siiratu Ibn Hisham 1/503,
da littafin Ar-Raudhul Unuf 2/345,
da littafin As-Siiratun Nabawiyyah
Ardhu Waqaa’i’i Wa Tahliilu Ahdath
1/492:-
((Da sunan Allah Mai rahama Mai
jinkai.
Wannan wani littafi ne daga
Muhammad Annabin nan kuma
Manzon Allah, tsakanin Muminai
da Musulmai daga Quraishawa da
mutanen Yathrib (Madina) da ma
wanda ya bi su ya riske su ya yi
jihadi tare da su.
Lalle su wata Al’umma ce guda
daya koma bayan mutane.
Muhaajirai daga cikinsu
Quraishawa za su ci gaba da zama
a kan al’amarin da suke a kai: za
su rika biyan diyya a tsakaninsu,
za su rika fansar fursunonin yaki
da aka kama daga cikinsu a bisa
tsari na kyautayi da adalci a
tsakanin Muminai.
Banuu Auf za su ci gaba da zama
a kan al’amarin da suke a kai: Za
su rika biyan diyya a bisa diyyarsu
ta farko, ko wace jama’a za ta rika
fansar fursunonin yaki da aka
kama daga cikinta a bisa tsari na
kyautayi da adalci a tsakanin
Muminai.
Banul Haarith Bin Khazraj za su ci
gaba da zama a kan al’amarin da
suke a kai: Za su rika biyan diyya a
bisa diyyoyinsu na farko, ko wace
jama’a za ta rika fansar fursunonin
yaki da aka kama daga cikinta a
bisa tsari na kyautayi da adalci a
tsakanin Muminai.
Banuu Jusham za su ci gaba da
zama a kan al’amarin da suke a
kai: Za su rika biyan diyya a bisa
diyyoyinsu na farko, ko wace
jama’a za ta rika fansar fursunonin
yaki da aka kama daga cikinta a
bisa tsari na kyautayi da adalci a
tsakanin Muminai.
Banun Najjar za su ci gaba da
zama a kan al’amarin da suke a
kai: Za su rika biyan diyya a bisa
diyyoyinsu na farko, ko wace
jama’a za su rika fansar fursunonin
yaki da aka kama daga cikinta a
bisa tsari na kyautayi da adalci a
tsakanin Muminai.
Banuu Amr Bin Auf za su ci gaba
da zama a kan al’amarin da suke a
kai: Za su rika biyan diyya a bisa
diyyoyinsu na farko, ko wace
jama’a za ta rika fansar fursunonin
yaki da aka kama daga cikinta a
bisa tsari na kyautayi da adalci a
tsakanin Muminai.
Banun Nabit za su ci gaba da
zama a kan al’amarin da suke a kai
za su rika biyan diyya a bisa
diyyoyinsu na farko, ko wace
jsma’a za ta rika fansar fursunonin
yaki da aka kama daga cikinta a
bisa tsari na kyautayi da adalci a
tsakanin Muminai.
Lalle Muminai ba za su bar
mutumin da bashi ya ci karfinsa a
cikinsu ba face sai sun ba shi abin
da zai biya tare da kyautayi: Daga
fansa ko diyya.
Sannan Mumini ba zai yi kawance
da ‘yantaccen bawa na wani
Mumini ba koma bayan wancan
Muminin.
Kuma lalle Muminai masu takawa
hannuwansu yana kan dukkan
wanda ya yi zalunci a cikinsu ko ya
nemi samun wata kariya ta hanyar
zalunci, ko zunubi, ko ketare iyaka,
ko yada barna tsakanin Muminai,
lalle hannuwansu suna kansa
gaba daya koda kuwa da ne yake
ga daya daga cikinsu.
Sannan Mumini ba ya kashe
Mumini saboda kafiri, haka nan ba
zai taimaki kafiri a kan Mumini ba.
Kuma amanar Allah daya ce mafi
kankanta a cikin Muminai in ya
dauke ta hakan sai ya lazimce su
(gaba daya).
Kuma lalle Muminai sashinsu
majibinci ne ga sashi koma bayan
sauran mutane.
Kuma lalle dukkan wanda ya bi mu
daga cikin Yahudawa to yana da
hakkin taimako da koyi a bisa halin
suna wadanda ba a zalunta, kuma
ba a taimakon wani a kan cutar da
su.
Kuma lalle zaman lafiyar Muminai
daya ce ba za a kulla zaman lafiya
da wani Mumini ba koma bayan
wani Muminin a cikin yaki cikin
tafarkin Allah face sai a bisa daidai
da adalci a tsakaninsu.
Kuma lalle ko wane yaki da ake
aiwatarwa za a rika karbabbeniya
ne a tsakaninsu (idan wadannan
jama’a suka fita a wannan yakin to
wasu jama’an kuma sai su fita a
daya yakin).
Kuma lalle Muminai sashinsu na
dawowa a kan sashi da abin da ya
sami jininsu cikin tafarkin Allah.
Kuma lalle Muminai masu takawa
suna bisa mafi kyawun shiriya
kuma mafi mikewansa.
Sannan wani mushruki (mai bautar
gumaka) ba zai ba da mafaka ga
wani rai ko dukiya ta Quraishawa
ba, kuma ba zai shiga tsakanin
wani Mumini da shi ba (shi wannan
ran ko dukiyar).
Sannan duk wanda ya yi kisan kai
a bisa zalunci kisa kuma wanda ya
tabbata ta hanyar hujja to za a yi
kisasi ne (ramuwar gayya) a
cikinsa sai dai idan waliyyin wanda
aka kashe ya yarda ya karbi diyya,
sannan dole ne dukkan Muminai
su tsayu a kansu babu abin da zai
halatta gare su sai tsayuwa a
kansa.
Sannan ba ya halatta ga Muminin
da ya yarda da abin da ke cikin
wannan Littafin (constitution) kuma
ya yi imani da Allah da Ranar
Lahira ya taimaki mai laifi, ko ya ba
shi mafaka kuma lalle duk wanda
ya taimake shi ko ya ba shi mafaka
to hakika akwai la’anar Allah a
kansa, da kuma fushinSa a Ranar
Kiyama, sannan ba za a karbi wata
musanya ko fansa daga gare shi
ba.
Sannan duk yadda kuka saba a
cikin al’amari to fa makomarsa
zuwa ga Muhammad mai tsira da
amincin Allah ne.
Lalle Yahudawa za su rika ciyar da
dukiyarsu tare da Muminai matukar
dai ana yakarsu (su Muminan).
Sannan Yahudawa Banuu Auf
wata Al’umma ce tare da Muminai.
Yahudawa suna damar yin
addininsu, Musulmi ma suna da
daar yin addininsu: ‘Yantattun
bayinsu da su kansu sai wanda ya
yi zalunci ya yi zunubi, lalle shi
wannan babu wanda yake
hallakarwa sai kansa da kuma
iyalan gidansa.
Kuma lalle Yahudawan Banuu
Najjar suna da keatankwacin abin
da Yahudawan Banuu Auf suke da
shi.
Sannan Yahudawan Banul Haarith
suna da kwatankwacin abin da
Yahudawan Banuu Auf auke da
ahi.
Sannan Yahudawan Banuu
Saa’idah suna da kwatankwacin
abin da Yahudawan Banuu Auf
suke da shi.
Sannan Yahudawan Banuu
Ju’sham suna da kwatankwacin
abin da Yahudawan Banuu Auf
suke da shi.
Sannan Yahudawan Banul Aus
suna da kwatankwacin abin da
Yahudawan Banuu Auf suke da
shi.
Sannan Yahudawan Banuu
Tha’ala’bah suna da kwatankwacin
abin da Yahudawan Banuu Auf
suke da shi.
Sai fa wanda ya yi zalunci ya yi
zunubi lalle shi wannan babu
wanda yake hallakarwa sai kansa
da kuma iyalan gidansa.
Kuma lalle jama’ar Jafnah wani
yanki ne na Kabilar Tha’ala’bah
saboda su kamar su suke.
Kuma lalle Banuu Sha’tai’bah suna
da kwatankwacin abin da
Yahudawan Banuu Auf suke da
shi.
Sannan aikin kirki ba kamar zunubi
yake ba.
Sannan ‘yantattun bayin
Tha’ala’bah kamar su Tha’ala’bah
ne suke.
Sannan abokan Yahudawa kamar
su kansu Yahudawan ne suke.
Sannan babu daya daga cikinsu da
zai fita ba tare da izinin
Muhammad mai tsira da amincin
Allah ba.
Sannan ba za a sanya kariya ba a
kan daukan fansar wani rauni.
Sannan duk wanda ya yi kisan gilla
to kuwa kansa da iyalansa ya yi
wa’ sai fa wanda ya yi zalunci,
kuma lalle Allah Yana kan magi
kyawun haka.
Sannan wajibi ne Yahudawa su
ciyar da dukiyoyinsu, kuma wajibi
ne Musulmi su ciyar da
dukiyoyinsu.
Sannan lalle akwai taimakon juna
a tsakaninsu a kan dukkan wanda
ya yaki mutanen wannan Littafin
(constitution).
Sannan lalle a tsakaninsu akwai
nasiha da ayyukan kwarai banda
zunubi.
Sannan ba a cewa mutum ya yi
laifi saboda dalilin abokin
kwancensa.
Sannan lalle akwai taimako ga
wanda aka zalunta.
Sannan kuma Yahudawa za su
ciyar da dukiyoyinsu tare da
Muminai matukar dai ana yakarsu.
Sannan garin Yathrib (Madina)
lalle mai alfarma ne ga mutanen
wannan Littafin (Constitution).
Sannan lalle makwabci tamkar
makwabcinsa yake matukar ba mai
cutarwa ba ne ba kuma mai zunubi
ba ne.
Sannan ba a ba wa wata mace
mafaka ba tare da izinin mutanenta
ba.
Sannan dukkan abin da ya
kasance a tsakanin jama’ar
wannan Littafin (constitution) na
wani laifi ko wani jayayya da ake
tsoron barnarsa, to makomarsa
zuwa ga Allah ne kuma zuwa ga
Muhammad Manzon Allah ne mai
tsira da amincin Allah.
Sannan Allah Yana a kan mafi kirki
da takawar abin da yake cikin
wannan Littafin (constitution).
Sannan ba a bai wa Quraishawa
da wadanda suka taimake su
mafaka.
Sannan lalle taimako dole ne a
tsakaninsu a kan dukkan wanda ya
kawo wa Yathrib (Madina) hari.
Idan kuma aka kira su zuwa ga
wani sulhu da za su yi shi kuma su
jibance shi to lalle za su yi sulhun
kuma za su jibance shi, lalle su
idan aka kira su zuwa ga misalin
haka to lalle ne suna hakki a kan
Muminai face wannan da ya yi yaki
cikin Addini.
A kan dukkan mutane akwai kaso
nasu ta bangarensun nan da yake
ta fiskarsu.
Kuma lalle Yahudawan Aus:
‘Yantattun bayinsu da su kansu
suna kan misalin abin da ma’abuta
wannan Littafin (constitution) suke
da shi tare da tsantsar mutumin
kirki daga ma’abuta wannan Littafin
(constitution).
Kuma lalle aikin kirki ba kamar
zunubi yake ba, babu wani mai
aikata wani aiki na barna face a
kan kansa.
Kuma lalle Allah Yana kan mafi
gaskiya kuma mafi kirkin abin da
yake cikin wannan Littafi
(constitution).
Kuma lalle wannan Littafin
(constitution) ba ya ba wa azzalumi
da mai zunubi kariya.
Kuma lalle dukkan wanda ya fita
daga Madina amintacce ne, kuma
dukkan wanda ya zauna cikin
Madina amintacce ne, sai wanda
ya yi zalunci, ko ya yi zunubi.
Kuma lalle Allah Mai ba da mafaka
ne ga wanda ya yi kirki da takawa,
haka ma Muhammad Manzon
Allah mai tsira da amincin Allah)).
Intaha.
*************************
wannan ita ce:-
ﺍﻟﻮﺛﻴﻘﺔ – ﺍﻟﺼﺤﻴﻔﺔ – ﺍﻟﺪﺳﺘﻮﺭ
Da Annabi mai tsira da amincin
Allah ya rubuta wa mutanen
Madina Musulminsu da
Yahudawansu da kafurai masu
bautan gumaka dake tare da su.
Kuma Annabi ya rubuta musu
wannan constitution din ne ba
saboda da yaudara ba a’a saboda
su yi aiki da shi ne.
Ke nan wannan yana tabbatar
mana da cewa duk lokacin da
Musulmi masana Shari’ar
Musulunci suka hadu suka rubuta
constitution saboda gudanar da
kasarsu, ko gudanar da wata
kungiya tasu, ko gudanar da wani
club nasu, to ba daidai ba wani ya
ce zai karya wannan constitution
din saboda biyan wata maslahar
kansa. Kuma wannan shi ne
ma’anar fadar Annabi mai tsira da
amincin Allah cikin hadithi sahihi:
((Musulmi duna bisa sharuddansu
sai fa sharadin da ya haramta hala,
ko ya halatta haram)).
Muna fata Allah Ya nuna mana
gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon
bin ta Ya nuna mana karya karya
ce Ya ba mu ikon guje mata.
Ameen.
Leave a Reply