ANNABI MUHAMMDU TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI DA ALAYENSA DA SAHABBANSA(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe)

Danna nan domin shiga karatu Online

Ya dan uwa ka sani son manzon
Allah da son abin da yazo da shi
wajibi ne, duk wanda ya kyamaci
wani abu da Annabi yazo da shi, to
ya kafirta koda yayi aiki da shi.
Kuma soyayya kadai bata
wadatarwa, dole ne sai ya zamo
anfi sonsa fiye da komai, hatta
ranka, dama kuma duk wanda
yake son abu zai fifita shi kuma zai
zabi ya dace da shi.
Mai gaskiya cikin son Annabi shine
wanda alamomin hakan zasu
bayyana a gare shi ta hanyar
biyayya da kwaikwayo da bin
umurnin sa da kuma nisantar abin
da ya hana, da kuma ladabtuwa da
ladubbansa cikin jin dadi da kunci.
Domin biyayya da da’a sune
soyayya yake haifarwa, kuma ba
tare da su ba soyayya bata
gaskatuwa.
Kuma son Annabi tsira mai da
aminci yana da alamomi da yawa,
daga ciki akwai:
-yawan yi masa salati.
-yawan anbatonsa.
-Shaukin (Bege) saduwa da shi.
-Girmama shi da mutunta shi yayin
da aka ambace shi.
Sahabban manzon Allah Mai tsira
da aminci sun kasance duk
sa’adda aka ambaci Annabi sai
kaga sun nutsu jikin su ya nuna
alama.
Daga cikin alamun akwai kin duk
wanda yake kin Annabi SAW, da
kuma gaba da duk wanda yake
gaba da shi, da nisantar duk
wanda ya sabawa sunnarsa ko
kuma ya kago wani abu a cikin
addini wanda ba shi a cikin addini.
Sawa’un cikin yan bidi’ah ko
munafukai.
Daga ciki akwai son duk wanda
Annabi SAW yake so, kamar iyalan
gidansa da matayensa (Ahlul baiti)
da sahabbansa na makkah dana
Madina (Muhajirun da Ansar) da
kuma kin duk wanda yake kinsu.
Ko yake gaba da su, da kuma kin
mai kinsu.
Daga ciki akwai koyi da halayensa
kyawawa, dama kuma shine yafi
kowa kyawun halaye, kuma yafi
kyauta, musamman ma idan watan
ramalana ya kama. Kamar yadda
Nana Aisha tace: “Halayensa gaba
dayansu Al’Qur’ani ne” ma’ana ya
lizamci aikata duk abin da
Al’aqur’ani yayi umurni da shi.
SIFOFIN MANZON ALLAH TSIRA
DA AMINCI SU TABBATA A GARE
SHI.
Manzon Allah SAW ya kasance
yafi kowa jarumta musamman ma
idan an fita filin daga. Yafi kowa
karamci, kyauta tasa tafi yawa a
ramalana, yafi kowa nasiha, yafi
kowa hakuri, baya rama abin da
akayi masa, amma idan an sabawa
Allah to anan yafi kowa zafi, yafi
kowa tawali’u, yafi kowa nutsuwa,
yafi kowa kunya, kuma yafi kowa
kyautatawa iyalansa, yafi kowa
jinkai da tausayi. Da sauran su.
Allah ya bamu ikon koyi da shi ta
hanyar da ta dace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “ANNABI MUHAMMDU TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI DA ALAYENSA DA SAHABBANSA(Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe)”
  1. Sulaiman alhassan Avatar
    Sulaiman alhassan

    Jazakallahu khairan

  2. usman isa el-yazaki, kwandare Avatar
    usman isa el-yazaki, kwandare

    sadaqallahu fiika mallam kabiru gombe mai wargajar da bidi’a da karfin Allah

  3. Allah yatai maki malam

  4. Auwal Aliyu Sara Avatar
    Auwal Aliyu Sara

    Jazakumullah khairan

Leave a Reply

Categories
Latest updates