Babbabn arziki shine,
Na daya : Son Allah, girmama Allah,
kwadayin rahmar Allah, Tsoran
Azabar Allah, a Bautawa Allah da
iklasi, akan tafarkin manzon tsira,
Na biyu : Son Annabi saw, Girmama
shi, biyayya a gareshi, ( Aqidarka, da
ibadarka, da halayenka, da
mu’amalarka, duk kayi koyi da
Annabi saw, fili da boye, zahiri da
badini,)
Na uku : ka yarda ka amince duk
abinda ya sameka mai dadi da mara
dadi duk daga Allah ne,
Na hudu : ka dinka kallon na kasa
dakai a harkar duniya, na sama da kai
a harkar lahira,
Na biyar : duk abinda zaka ci ko ka
sha, ko ka daura, ka tabbatar halal ne.
Na shida : duk abinda zakayi ka
tabbatar kana da hujja, da zaka kare
kanka a gaban Allah taala ranar
alkiyama
.
Na bakwai : Duk sanda abin duniya
dana lahira suka ci karo, ka fifita na
lahira akan na duniya,
Na takwas : kaso ma dan uwan ka
musulmi abinda kake sowa kanka na
alkhairi.
Na tara : Idan zakayi magana ko
rubutu, ka fadi alkhairi ko kayi shiru,
Na goma : ka yawaita karatun
Alkur’ani mai girma, da zikri da
salatin Annabi saw, da istigfari,
Na sha daya : ka dauki kanka ba kowa
ba, ba komai ba, domin farkon yan
wuta, malamai ne, da attajirai, da
mujahidai, da sukayi aiki, ba don
Allah ba, sai don a fada, kuma an
fada, sunji dadi, don haka suka zama
makamashin Jahannama.
Na sha biyu: kada ka kuskura kabar
duniya da hakkin wani a kanka.
Allah rahmar ka ba dan muba.
Leave a Reply