Babu Alheri cikin zagin shuwagabanni

Danna nan domin shiga karatu Online

Maqala

Sau da dama talakawa wa’inda ake mulka sukan riƙi zagin shuwagabanni da ci musu zarafi a matsayin wata hanya ta huce fushinsu, Sai kaga mutum a kullum bashi da wani aiki sai tsine wa shuwagabanni da cin zarafinsu. Toh haƙiƙa wannan tafarki ne da ka iya kai mutum zuwa ga wuta.

Domin kada ka ɗauka Allah bazaiyi hisabi tsaƙaninka da wa’innan shuwagabanni da kake zagi ba, zai iya yiwuwa ku tashi ranar tashin Al Qiyama Allah yayi maku hisabi kaga cewa Kai zaluncin da kayi akansu yafi wa’inda sukayi akanka, a lokacin babu wani abu da za’ayi sai dai a ɗebi ayyukan ka na Alheri a Zuba musu, in kuma babu sai a ɗebi nasu zunuban a lafta maka.

Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya bada labari cewa Za’a samu wani wanda zaizo ranar tashin Al Qiyama da tarin ayyuka na alheri, amma duk za’a kwashe a baiwa mutane da ya kasance yana zagi da ci wa mutunci da zalunta a duniya. Annabi ya kirashi da suna Al-muflis. Wanda shine talaka futuk a ranar tashin Al Qiyama.

Sabida haka ba tafarki na Musulunci bane zagin koma waye ballantana shuwagabanni. Abinda ya dace ayi wa shuwagabanni shine addu’ar shiriya, idan mutum bazai iya ba toh ya kame bakinsa shine yafi masa alheri.

Abubuwa da suke faruwa a yanzu na zaluncin shuwagabanni abu ne wanda Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya bada labarin zai auku, sabida haka ya faɗa wa Musulmi abinda ya dace suyi idan hakan ta faru.

Abdullahi ibn Mas’ud ya rawaito hadisi daga Annabi yace:

A bayana zaku fuskanci son kai daga shuwagabannin ku, sannan kuma zaku ga abubuwa wanda bakuso, sai Sahabbai suka tambayi Annabi me ya dace wanda wannan zamani ya riska yayi sai yace: ku basu haƙƙi da yake akanku, ku kuma ku roƙi Allah haƙƙin da yake naku

Muslim: 1843

Wannan yake nuna zage zage da aibata shuwagabanni ba tafarkin Annabi bane. Ya kamata mu guje wa yin haka. Domin cigaba da yiwa shuwagabanni mummunan Addu’a babu abinda zai ƙara musu sai daɗa lalacewa. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates