Baya Halatta ayi yanka wa Aljanu

Danna nan domin shiga karatu Online

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.

Bismillahir-Rahmanir-Raheem.

Tambaya: Shin ya halatta ayi yanka wa Aljanu ko aci yankan?

Amsa: Baya halatta musulmi yayi yanka wa aljanu ko yaci yankan da akayi wa Aljanu.

Dalili: An rawaito daga Aliyu bin Abi dalib Allah ya ƙara masa yarda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace: Allah ya tsine wa wanda yayi yanka wa wanin Allah. Sahih Muslim: 1978.

Wannan hadisi ya shafi Aljanu da wasunsu, baya halatta Musulmi yayi yanka abisa umarnin aljani.

Ana samun wasu daga cikin musulmi wanda suke da matsalar shafa ta aljanu, sai Aljanun su rinƙa magana ta bakin mara lafiya suce a yanka musu dabba iri kaza mai launi kaza, sannan su faɗi abinda za’ayi da namar ko jinin, Wannan baya halatta a amsa musu.

Shafan aljanu abu ne tabbatacce, yana faruwa amma idan Allah ya jarrabi Mutum akaran kansa ko wani nasa toh abinda zaiyi shine ya rinka karanta masa Alkur’ani da Addu’oi na kariya da sukazo daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, sannan ya guje amsa wa buƙatun wa’innan Aljanu domin zasu jashi su kaishi harzuwa ga shirka. Allah ya tsaremu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates