Cukurkuɗaɗɗun takardu 5 (gyaran zuciya)

By: Hamza Diso

Babban malamin mu Sheikh Ɗaha Rayyan -Allah ya gafarta masa- yana cewa:

Shi ɗan Adam haɗaka ce ta abu biyu; damƙa daga yumɓu da kuma busa daga ruhin Allah maɗaukaki

Na taɓayin ishara kan yadda ruhi yake kama da gangar jiki ta wasu ɓangarori, kamar yadda jiki yake bukatar abinci haka shima ruhi yake bukatar irin nasa abincin, idan ka kula da gangar jikinka sai ta yi kyau, haka shima ruhi yake, idan ka sabawa jiki da ɗaukar nauyi sai ya ƙara ƙarfi to shima ruhi idan ka shagalta da bashi horo na gari sai ya ƙara aminci da lafiya.Ruhi idan aka tsaftace shi sai yayi garai-garai ta yadda zai iya ɗaukar duk wani abu mai kyau cikin sauƙi, ya kuma cika da hasken imani wanda zai jawo masa zurfin ilimi da tunani da hangen nesa, da kuma abu mafi muhimmanci wanda shine samun yardar Allah da soyayyar Allah mai rahama, ka taɓa auna girman ace yau kai, Eh kai, Allah yana sonka? Ya zakaji idan akace yau Allah ya kira sunanka yace da Jibrilu (AS) Ina son wane ɗan wane!!!!

Ilimin da yake bayar da muhimmanci a ɓangaren gyaran zuciya ana kiransa da sunaye daban-daban

  1. Ilimin Suluki
  2. Ilimin Zuhudu da abubuwa masu tausasa rai
  3. Attasawwuf Assunny Da ma wasu sunayan bayan waɗannan, shi wannan ilimi aikin sa shine ɗora mutum akan turbar kula da haƙƙoƙin Allah a zuci da zahiri, kuma tushensa shine Alƙur’ani da Hadisi da aikin magabata na ƙwarai.

Dukkanin ayoyi da suke motsa zuciya da saka tsoron Allah ko kwaɗaitar da mutum zuwa rahama ko bada labarin mutanan kirki da sakamakon su da kuma mutanan banza da sakamakon su, duk suna shiga cikin wannan ilimi, sannan mafi yawan littattafan hadisi suna ware wani ɓangare don kawo hadisan Zuhudu da abinda yayi kusa dashi.Wasu malaman ma sukan rubuta littafi mai zaman kansa a wannan babin, akwai littattafai dayawa da suke da sunan الزهد, kamar littafin Ibnul Mubarak wanda ya ƙunshi sama da hadisi 1200 da littafin Baihaƙi mai sama da hadisai 900(marfu’ai da wasunsu) da sauran littattafai.Ga littafin Almunziri, ga littattafan Ibnu Abiddunya, ga Riyadhussalina, sannan akwai littattafai wadanda ba iya riwaya ake a cikinsu ba, kamar littattafan Ibnul Jauziy masu yawa a wannan babin da Ibnul Ƙayyim, musamman Madariju, Adda’u wad dawa’u, da Alfawa’id da sauransu.Shi Zuhudu mataki uku ne

  1. Gudun duniya (abubuwan da aka haramta da kuma kayan shagala) amma kuma – a wannan matakin- ana matukar son duniyar, sai dai ana ƙoƙarin dannewa ne kawai, kuma ana shan wahalar dannewar.
  2. Gudun duniya cikin sauƙi ba tare da shan wahalar barinta ba, tare da jin cewa kai mai gudun duniyar kai kafi kowa morewa, don ka bayar da ƙwandala ne an baka ƙwandala biyu, sai dai – a ranka – kasan duniya ta na da kima amma bata kai zuhudun ka ba.
  3. yin Zuhudu akan Zuhudun kansa, ta yadda mai yi baya ganin yana yin wani abu mai muhimmanci don kullum raunin ayyukan sa yake kalla, yana kallon duniya a matsayin wani wulaƙantaccen abu, don haka shi yabar wani abun banza ne ya sami mai ƙima.

Ita duniya kamar ƙanƙara ce zata narke da wuri, ita lahira kuma kamar zinare take, kullum yana nan.Wanda yayi watsi da duniya don neman yardar Allah kamar mutumin da kare – mai haushin tsiya – ya hana shi shiga fadar sarki ne, sai ya hurgawa karen bushashshiyar gurasa, sai karen ya shagalta da ita, shi kuma mutumin ya shige cikin fada ya sami karamci, shi shaiɗan shine wannan karen, hurga masa duk abubuwan da aka hanaka, ka wuce ka shiga fadar Allah maɗaukaki.Allah ya tanadar maka dukkanin wani nau’i na karamci, kayi masa ɗa’a ka bi dokokin sa, wallahi zaka rabauta, kayi bauta don samun lahira ba don biyan buƙatar duniya ba.Akwai mutanan da suna son rayuwa ne kawai don su sami damar ƙara yin bauta da samun kusanci ga Allah, kai menene burin ka na rayuwa?Wasu tuni sun sami gurbi a gidan hutu, shin kai ka sayi filoti? Hurul Eini sun caɓa ado shin kana cikin manema?Ya Allah, bamu da kyawawan ayyuka masu yawa, amma muna kwaɗayin rahamarka, mu musulmi ne muna ƙaunarka muna ƙaunar Annabinka mun yarda da musulunci a matsayin addinin mu, ya Allah ka da ka sanya mu gurin da zaka sanya maƙiyanka wallahi mu muna sonka, ka gafarta mana ka bamu ikon aikata daidai.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: