Daga cikin Alamomin kusantowar tashin Qiyaama

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bukhari Allah yayi masa rahama ya rawaito acikin Sahihinsa. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:

Al-Qiyama baza ta tashi ba har sai an kame ilimi(Ta yadda maluma zasuyi ta mutuwa ba’a samun masu maye gurbinsu) girgizan kasa ta yawaita, sannan kuma lokaci zai zamto kusa(ta yadda lokaci zai rinƙa sauri). fitina zata bayyana, sannan kisa zai yawaita cikin mutane. Kuma dukiya zata kwarara cikin mutane.

Bukhari: 1036

قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لَا تَقُومُ السَّاعَةُ حتَّى يُقْبَضَ العِلْمُ، وتَكْثُرَ الزَّلَازِلُ، ويَتَقَارَبَ الزَّمَانُ، وتَظْهَرَ الفِتَنُ، ويَكْثُرَ الهَرْجُ – وهو القَتْلُ القَتْلُ – حتَّى يَكْثُرَ فِيكُمُ المَالُ فَيَفِيضَ

البخاري ١٠٣٦

Faɗin Annabi cewa zamani zai kusanto: Malamai sunyi magana akansa

suka ce: Albarka ne Allah zai cire daga cikin ranaku da kwanakin sai ya zamto suna wuce wa cikin sauri.


Ga duk mai hankali yasan cewa wa’innan alamu sun bayyana. Ya dace Musulmi yayi ƙoƙari yayi amfani da lokacinsa wurin ribatar sauran alkhairai da suka rage. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories