Daga Rayuwar Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah1(Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Daga Rayuwar Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah (1)
Shi ne Takiyyuddeen, Abul Abbas Ahmad Bin Abdul-Halim bin Abdus-Salam Ibnu Taimiyyah. An yi masa lakabi da Ibnu Taimiyyah ne saboda lakabin kakarsa ne.
Gidansu ibnu Taimiyyah gida ne na ilimi, saboda shi da babansa da kakansa duk malamai ne.
An haife shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah a ranar Litinin, goma ga watan Rabii’ul Auwal, shekarar hijira 661, a wani gari da ake kira Harran.
Mahaifinsa ya yi hijira daga garin Harran zuwa Dimashka a shekarar 667 A.H a lokacin shaikhul Islam yana da shekara shida.
Shaikhul Islam ya yi karatu a wurin malamai da yawa a nan garin Dimashka, daga cikinsu akwai sheikh Zainuddeen Ahmad bin Abdudaa’im, da sheikh Ibnu Abil Yusri, da sheikh Kamal bin Abdu, da Ahmad bin Abil khair da sauransu.
Allah Madaukakin Sarki ya horewa Ibnu Taimiyyah kwakwalwa da kaifin fahimta, tun yana karami har zuwa girmansa, kamar yadda Allah ya bashi nacin karatu da neman ilimi, ya haddace Alkur’ani, ya karanta ilimin fikihu da Arabiyya, ya koyi tafsiri da usulul Fikhi, duka ya yi wannan karatu yana dan shekara goma sha.
Shaikhul islam ya taso cikin kamun kai, da yawan ibada, da tsakaitawa wajen abinci da abin sha da tufafi.
Mahaifinsa ya rasu yana da shekara 20, kuma kasancewar mahaifinsa malami ne sai ya gaji kujerarsa wajen karantarwa da ilmantarwa, mutane na taruwa daga garuruwa da wurare daban daban don sauraron karatunsa da irin baiwar da Allah ya yi masa ta ilimi.
Allah Madaukakin Sarki ya yi masa rasuwa a shekarar 728 A.h a cikin kurkukun da aka kulle shi a daren 22 ga watan Zulka’adah.
An ga turuwar mutane wajen jana’izarsa, wadanda sun kai mutum dubu dari zuwa dubu dari biyu, banda mata wadanda suke lekowa daga gidaje yayin wucewar gawarsa, suna yi masa addu’a da nama masa gafara.
Shaikhul Islam ya mutu ya barwa al’ummar musulmi wagagan littattafai a fannoni da dama na musulunci, wadanda har yanzu ana kan fito da su, da tantance su da gabatar da su ga al’ummar musulmi.
Bayan mutuwarsa mutane da dama sun yi kyakkyawan mafarki da shi. Allah ya yi masa rahama ya gafarta masa kurakuransa. Ameen.
(Mu hadu a kashi na biyu : yabon da malamai gare shi)

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “Daga Rayuwar Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah1(Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
  1. Sadiqufaruruwa Avatar
    Sadiqufaruruwa

    Malam rabi,u umar rijiyar lemo Allah yasaka da alkairi

  2. Shamsi Sani Gumel Avatar
    Shamsi Sani Gumel

    Allah ya kare mallam da sharrin wannan zamani.Allah kasakawa mallamimmu,mal.rabiu r/lemo da aljannar firdausi.Amein.

  3. Aliyu Sulaiman Avatar
    Aliyu Sulaiman

    Allah bada lada.

Leave a Reply

Latest updates
Categories