DALILAN DA SUKE KUBUTAR DA BAWA DAGA UKUBAR AIKATA LAIFUKA DA ZUNUBAI

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Mai rubutu: Abdurrahman Muhammad Sani Umar


Mumini idan ya aikata zunubi to ukubar wannan zunubin tana kauce mai da wasu dalilai goma:

  1. Ya tuba sai Allah ya karbi tubarsa domin wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bashi da zunubi ne.
  2. Ko yayi istgfari sai agafarta mai.
  3. Ko ya aikata ayyukan alheri sai su shafe wadannan zunuban domin ayyukan alheri suna shafe zunubai.
  4. Ko yan uwansa muminai su mai addu’a su nema mai gafara yana raye ko yana mace.
  5. Ko su sadaukar mai da ladan ayyukan su wanda Allah zai amfaneshi da shi.
  6. Ko annabin sa Muhammd (SAW) ya cece shi.
  7. Ko Allah (SWT) ya jarrabe shi da musibu a duniya wanda zasu kankaremai laifukansa.
  8. Ko ya jarabce shi a barzakhu da tsawa sai ya kankaremai laifukan sa da ita.
  9. Ko ya jarbce sa a ranar alkiyama da wahalhalunta wanda zasu kankaremai laifukansa.
  10. Ko kuma wanda yafi kowa rahama yayi mai rahama ya ji kansa.

Wanda wadannan goman suka kubuce mai to kar ya zargi kowa sai kansa
Kamar yanda Allah ya fada a abinda Manzon Allah (SAW) ya raiwato daga gareshi cewa “yaku bayina lallai wadannan sune ayyukan ku zan kiyaye muku su in kuma saka muku da su wanda yaga alheri to ya godewa Allah wanda kuma yaga sabanin haka to kar ya zargi kowa sai kansa”

[Shaikhul Islam Ahmad Ibnu Taimiyya]

Leave a Reply

Latest updates
Categories