DALILAN DA YA SA TA’ADDANCI ZAI DADE BA A DAINA BA A WANNAN KASA TA NIGERIA(Dr Ahmad Gumi)

Danna nan domin shiga karatu Online

Duk wanda ya kasance hanyar da
cimma manufofinsa ita ce ta
hanyar zubar da jini da kisa to lallai
wannan mutumin dan ta’addane.
Daga yanzu ya bayyana cewa
harkar ta’addanci ba kwai ya
takaita ga wani dan gungun
samarin musulmai ba ne wadanda
suka zabi zubar da jini a matsayin
hanyar cimma burinsu ko kuma
ramuwar gayya a kan rashin
adalcin da aka yi musu, ko ga
musulmi kamar yadda suke fadi.
A’a ayyukan ta’addanci sun fi karfin
haka kuma basu takaitu ga
wadannan samari ba kawai. Babu
wanda ya san iyakan ayyukan
ta’addanci, domin a cikin addini da
kabilanci da wariyar launin fata da
dai sauransu duk ana samun
ayyukan ta’addanci a cikin su.
Mu dai a musulunci mun yi sa’a
cewa, wasu ‘yan tsirarun samari ne
suka riki wannan gurbatacciyar
fahimta, domin musulunci yayi
kakkausar suka da gargadi kan
kashe rai ba da hakkin shari’aba.
Kuma yin haddi na tabbata ne
kadai idan al’umma suka hadu
suka zabi shugaba ta hanyar
shawara (shurah). To, irin wannan
shugaba shi kadai ya ke da ikon
zartar da haddi. In ba kadan da
muke gani ba a yanzu, ya na da
wuya musulmi kaga ya yi kisan kai.
Yawan kashe-kashe da ya yadu a
kasashen yammaci, hakan ya faru
ne a sakamakon rayuwa ta rashin
da kuma rashin kula da yaduwar
makamai a tsakaninsu. Akwai
makamai ma su yawa a kasar
Yamen a hannun mutane, amma
saboda addini da kuma sani da
suka yi na cewar addinin
musulunci ya hana kashe rai ba da
hakkinta ba, musulmi da wand aba
musulmi ba sai ya kasance kasar
bata da yawan kisa da zubar da
jinni. Wannan kuwa ba haka ya ke
ba a wani bangaren addini wanda
ba musulunci ba.
Ayyukan ta’addanci da yafi muni a
wannan kasa shine irin yadda
jami’an tsaro na gwamnati suke
amfani da damarsu suke kashe
mutane ba tare da ji ko gani ba
wadanda basu da laifi. Suna yin
haka ne domin cimma wata
manufa ta tabbatansu a kan mulki
ko kuma domin cimma manufar
siyasa.
Kamar a Najeriya mun ga yadda
wadansu kiristoci suka kashe
shuwagabannin musulmi don
cimma manufarsu ta siyasa.
Wadannan mutane sun fi hatsari
fiye da ‘yan boko haram.
Manufarsu shine su rusa
musulunci gaba dayansa ta hanyar
karkashe shuwagabannin mu,
domin su bar sauran al’ummar
musulmi a matsayin bayi. Wannan
shine dalilan da ya sa Abubakar
Tafawa Balewa da Sardauna da
Akintola da Gen. Murtala
Muhammad suka rasa rayukunsu
ta hanyar wadannan ‘yan ta’adda.
Wadannan ‘yan ta’adda su ne a
yau wai su ke jagorancin fada da
ta’addanci ko yaki da boko haram.
Wannan yaki da suke yi sun fake
ne da guzuma suna saran karsana.
Domin sun kashe mana
shuwagabanni a baya, yanzu
kuma suna sake binsu tare da
samarinmu suna kashe su lokaci
guda. Ga yadda suke kara karfi a
soja da madafun iko. Suna yi wa
musulmai na kwarai ritaya don
tabbatar da manufofinsu na
ta’addanci da suka faro tun daga
1966.
Suna zaton suke da wuka da
nama, don sun riga sun makance a
cikin kiyayya tare da hassada da
kuma ta’addanci. Har ba sa iya
ganin cewa mugun aikinsu yana
bayyana da manufofinsu tare da
hujjoji. Ba sa iya ganin cewar Allah
da kanSa ya dauki yakin da suke yi
da musulumi da musulunci, yakin
yanzu ya koma shi da su, saboda
miyagun manufofinsu. Kaduna ma
anso a mayar da ita kamar garin
Maiduguri ne sai Allah ya shiga
tsakani.
Sun manta cewar baka iya
tabbatar da rayuwarka ko mulkin
ka ta hanyar kashe wani, kana iya
tsare rayuwar ka ne idan ka bar
wani ya rayu kuma ya zauna lafiya
(Kowa ya ce wutar kara ta kwana,
to, shine ya kwana bai yi barci ba).
Suna zaton cewar suna iya tabbata
a mulki ta hanyar amfani da
muggan makamai, sun manta
cewa dukkan karfi ya tabbata ga
Allah ne? Najeriya zata tabbata ne
kuma ta zauna lafiya idan ire-iren
wadannan mugayen mutane an
kore su daga tsarin gwamnati da
jami’an tsaro. A ka maye su da
mutane na gari, wannan shine
bangare mafi hatsari wanda
mutane suka kau da kai daga gare
shi, wanda wajibi ne mutane su
lura su sa ido akai.
Miyagun ayyuka da muggan dabi’u
ba za su kai ga nasara ba Insha
Allah.
Allah ya tsare mu daga dukkan
sharri.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “DALILAN DA YA SA TA’ADDANCI ZAI DADE BA A DAINA BA A WANNAN KASA TA NIGERIA(Dr Ahmad Gumi)”
  1. Bashir musa Avatar
    Bashir musa

    Addinin muslinci bai yar da kazamo cima zauneba sa dai adakko abaka, wajibine duk wani musilimi yazamo ya dogara dakansa. Kuma karyasa aransa lalle sai yayi kudi wanda yin haka zai jasa ga hallaka

Leave a Reply

Categories
Latest updates