DARASI NA GOMA (10)SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI’A(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

SHUBUHOHIN SHI’A A KAN
ALKUR’ANI, TARE DA WARWARE
SU A BISA FAHIMTAR
MAGABATA NA KWARAI.
Mabiya Shi’a masu limamai goma
sha biyu sukan dogara da wasu
Hadisai wadanda kamar a zahiri
suna nuni da cewa Alkur’ani bai
cika ba.
‘Yan Shi’a sukan yada irin
wadannan Hadisai a cikin
al’umma, domin su nuna cewa
mummunar akidar nan ta su ta
ganin rashin ingancin Alkur’ani dai
dai ce, kuma litattafai na Sunna
sun yi nuni da hakan.
Daga cikin irin Hadisan da suke
yadawa akwai Hadisin Sayyadina
Umar dan Khaddab (R.A.) da yake
magana a kan hukuncin jefe
mazinaci. Inda Sayyadina Umar
(R.A) yake cewa: – “Daga cikin abin
da Allah (S.W.T) ya saukar na
Alkur’ani akwai ayar da ta yi
magana a kan hukuncin jefe
wanda yai zina, mun karanta
wannan ayar, kuma mun kiyaye ta.
Hakika Manzon Allah (SAW) ya
jefe mazinaci, mu ma mun jefe
mazinaci. Ba don gudun mutane
zasu ce na kara wani abu a cikin
Alkur’ani ba, da na sa an rubuta
ayar, domin ina gudun kada
zamani ya yi nisa mutane su ce ba
su ga ayar jefe mazinaci a cikin
Alkur’ani ba, sakamakon hakan su
bata saboda barin wajibi daya da
Allah ya dora mu su” .
‘Yan Shi’a sukan ce wannan
Hadisin da ire-irensa na nuni da
cewa, Alkur’ani bai cika ba.
Sannan kuma daga cikin littattafan
Sunna suke, kamar Bukhari da
Muslim. Don haka ba Shi’a kadai
suke da ra’a yin cewa Alkur’ani bai
cika ba.
Jawabi a kan wannan shubuha shi
ne ta fuskoki kamar haka: –
1-Babu wani Hadisi ingantacce,
sananne a gurin Malaman Sunna
dake nuna cewa Alkur’ani bai cika
ba.
Hakan ne yasa Malaman Sunna
suka yi ijma’i kan cewa, wannan
Alkur’anin dake hannun mutane,
shi ne Alkur’anin da Allah ya aiko
Manzon Allah (S.A.W.) da shi, ba
ragi ba kari, ba jirkitawa ba
canjawa.
2- Hadisin Sayyadina Umar (R.A)
abin da yake nunawa shi ne , lalle
Alkur’ani ya cika ya kammala, ta
yadda ba zai karbi kari ko ragi ba
ta wacce fuska.
Abin da ke nuna haka shi ne –
Fadin Sayyadina Umar (R.A): – “Ba
dan kada a ce na yi kari a cikin
Alkur’ani ba, da na rubuta ayar
rajamu”.
Sai wannan magana take tabbatar
da cewa, sanannen abu ne a gurin
Sahabbai da sauran musulmi cewa
Alkur’ani a cike yake, ta yadda ko
ya ya wani ya kara wani abu zasu
gane.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce. To idan
Al-kur’ani ya cika me yasa babu
ayar da take Magana a kan
hukuncin jefe mazinaci a cikinsa,
bayan kuma ya tabbata cewa an
saukar da ita?
Bayani dangane da wannan shi ne
– sanannen abu ne a gurin
malaman Alkur’ani cewa, akwai
babi dake bayani a kan ayoyin da
aka shafe hukuncinsu ko kira’arsu.
(Wato karatunsu) ko aka shafe
hukuncinsu da karatunsu.
A kan haka malamai suke kasa
wadannan ayoyi guda uku:-
Na daya: – Ayoyin da aka shafe
hukuncinsu da karatunsu.
Na biyu: – Ayoyin da aka shafe
hukuncinsu amma, suna nan ana
karantasu.
Na Uku: – Ayoyin da aka shafe
karatunsu amma hukuncinsu yana
nan, kamar ayar jefe mazinaci, da
hukuncin raino. Don haka ita
wannan ayar tana karkashin
wannan kaso na uku.
Idan wani ya ce :- Ta ya ya za’a ce
an shafe karatun wata aya amma
hukuncinta yana nan?
Sai mu ce wannan tambaya ta yi
dai dai da irin abin da Yahudawa
suka tuhumi Manzon Allah (SAW)
da shi, lokacin da Allah (S.W.T) ya
umar ce shi da fuskantar Alkibla
lokacin Sallah, bayan a da yana
fuskantar Baitu Al-Mukaddas.
Sai Allah (S.W.T) ya ba su amsa
da cewa “Ga ya musu cewa Allah
ne yake da mallakin mabullar rana
da mafadarta”.
Don haka a nan, sai mu ce wannan
wani lamari ne da Allah (S.W.T) ya
ga damar zartar da shi, don ya
jarrabi ba yinsa.
Shi kuwa Ubangiji ya kammala a
ilimi da hikima, babu mai ikon
tambayarSa mai yasa ya aikata
wani abu.
Kari a kan wannan shi ne , idan har
an yarda cewa, akwai ayoyin da
ake karantasu amma ba’a aiki da
hukuncinsu, to yarda da cewa
akwai ayoyin da aka shafe
karatunsu, amma hukuncinsu yana
nan, shi yafi cancanta. Domin shi
Alkur’ani manufar saukar da shi,
shi ne a yi aiki da shi ba wai
karanta shi ba kawai.
3) Tun bayan rasuwar Manzon
Allah (S.A.W) yau fiye da shekara
dubu da dari hudu har izuwa
yanzu, babu wani Alkur’ani da
al’ummar musulmi tare da
sabaninsu, suke amfani da shi
banda wannan Alkur’anin da yake
hannunsu a yau.
Wannan abin da muka fada ya
hada da dukkan Ahlu Al-Baiti cikin
Bani Hashim da Bani Al-Muddalib
da matayen Manzon Allah (S.A.W)
da zuriyarsa.
‘Yan Shi’a ne kadai suke da’awar
cewa akwai wani Alkur’ani na
daban, a gurin limamansu wanda
ya saba ta kowa ce fuska da
Alkur’anin dake hannun al’ummar
musulmi.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce da wane Alkur’ani Sayyadina Ali
(R.A) da dansa Sayyadina Hasan
dan Ali (R.A) suka yi amfani
lokacin halifancinsu?
Wane Alkur’ani ragowar limaman
Shi’a suka karantar da al’umma?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Alkur’anin
dake hannun al’ummar musulmi.
Sai mu ce ina Alkur’anin da ‘Yan
Shi’a suke da’awar yana boye a
gurin limamansu, me yasa ba su
koyar da shi ba?
4) Da’awar cewa wannan
Alkur’anin bai cika ba, suka ne ga
hikimar Ubangiji, ta yadda ya bar
duniya kara zube, ba shi da wani
littafi na shiriya a bayan kasa.
Dalili kuwa shi ne , hakan zai bayu
da cewa dukkan littattafan da Allah
(S.W.T) ya saukar babu wanda ya
rage da ba’a canja shi ba.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce barin
duniya babu littafin shiriya na
gaskiya ba zai zama suka ga
hikimar Allah ba, tun da al’umma
sun taba zama ba tare da
hakikannin littafi saukakke daga
Allah (S.W.T) ba, tsakanin dauke
Annabi Isa (A.S) zuwa sama, har
izuwa aiko da Manzon Allah
(S.A.W).
Sai mu ce, ba dukkannin Attaura
da Injila dake hannun Yahudawa
aka canja ba. Bari dai akwai
Attaura da Injila ingantattu wanda
suke hannun wasu mutane kadan
cikin Yahudawa kamar yadda
Malamai suka tabbatar.
Sabanin da’awar da ‘Yan Shi’a
suke yi cewa, babu Alkur’ani na
gaskiya a hannun al’umma tun
bayan wafatin Manzon Allah
(S.A.W) har izuwa yanzu.
Kari a kan haka, Allah (S.W.T) ya
yiwa Manzon Allah (S.A.W)
alkawarin cewa, zai kare Alkur’ani.
Kuma ya tabbata a Hadisi cewa
har duniya ta tashi ba za a taba
rasa wasu mutane cikin
al’ummarsa ba suna kan gaskiya.
Dadin dadawa shi Alkur`ani sako
ne na duniya, sabanin Attaura da
Injila da suka shafi Yahudawa
kawai.
5) Idan har akwai kari da ragi a
cikin Alkur’ani kamar yadda ‘Yan
Shi’a suke da’awa, ashe Alkur’ani
bai da bambanci da sauran
litattafan da Allah (S.W.T) ya yi
bayanin cewa, an yi kari da ragi a
cikinsu kamar Attaura da Injila.
Yarda da wannan akida kuwa,
ruguje addini ne baki daya. Tun da
hakan zai bayu izuwa sukan duk
wani hukunci ko kissa ko bayani na
asalin imani da ya zo a cikin
Alkur’ani, ta hanyar sanya kokonto
a cikin zukata, a kan wata kila an yi
kari ko ragi a gurin.
6) Allah (S.W.T) shi ne da kansa ya
dauki nauyin kare wannan
Alkur’anin, kamar yadda ya ce: –
“Hakika mu ne muka saukar da
Ambato wato (Alkur’ani), kuma
hakika muna rantsuwa cewa mu ne
zamu kare shi”
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce, shin Allah (S.W.T) ya cika
wannan Alkawarin da ya dauka ko
bai cika ba?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Allah
(S.W.T) ya cika.
Sai mu ce ina da’awar ‘Yan Shi’a
cewa an yi kari da ragi a cikin
Alkur’ani?
Idan kuwa ‘Yan Shi’a suka ce,
Allah (S.W.T) bai cika wannan
Alkawari ba.
Sai mu ce, mai ya hana shi cikawa,
gajiyawa, sakaci, ragwanci ko
rashin yadda zai yi?
Idan suka ce babu ko daya.
Sai mu ce, lallai dole a samu daya.
Ko dai Ubangiji ya cika
alkawarinsa ko bai cika ba. Idan
kuma bai cika ba, to dole akwai
dalili.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce: Canja
Alkur’ani ko yin kari da ragi a
cikinsa, ba ya bayuwa izuwa
gajiyawar Allah (S.W.T), kamar
yadda canja Attaura da Injila
(Bible) bai bayu ga gajiyawarsa ba.
Sai mu ce, canja Alkur’ani yana
bayuwa izuwa gajiyawar Ubangiji,
domin shi ne ya yi alkawari, kuma
ya yi rantsuwar cewa zai kare shi.
Amma canja Attaura da Injila ba ya
bayuwa izuwa gajiyawar Ubangiji,
domin bai dauki alkawarin kare
Attaura da Injila ba, ballantana a
ce ya gajiya. Ya bar nauyin kare
Attaura da Injila ne ga Malaman
Yahudawa, su kuwa suka kasa
kare su, domin gajiyawar su da
son zuciyar su. Kamar yadda Allah
(S.W.T) ya ce: “Hakika mun saukar
da Attaura wacce a cikinta akwai
haske da shiriya. Kuma Annabawa
masu mika wuya ga Allah (S.W.T)
sun kasance suna hukunci da ita a
tsakanin Yahudawa, kamar yadda
malaman Yahudawa da masu
ibadar su suke hukunci da ita,
saboda nauyin da aka dora musu
na su kare littafin Ubangiji, kuma
suka zamo sheda a kan haka” .
Idan ‘Yan Shi’ar yanzu suka yi
da’awar cewa sun yarda da
wannan Alkur’anin da ke hannun
Musulmi. Ko suka ce ‘Yan Shi’a
masu shige gona da iri, su ne ba
su yarda da cikar Alkur’ani ba.
Sai mu ce wannan da’awa ce
kawai, saboda dalilai kamar haka: –
Na daya: – ‘Yan Shi’a sun shahara
Takiyya.
Na biyu: – Dukkan Malaman Shi’a
na wannan zamani da na zamanin
da ya wuce sun yi Ijma’i a kan
cewa Alkur’ani an canja shi.
Kamar yadda wani babban
malamin Hadisi na Shi’a ya fada a
littafinsa, mai suna “Rarrabe
magana kan tabbatar da canja
littafin Ubangijin ba yi”. A cikin
littafin ya kawo riwayoyi sama da
dubu biyu da suke nuna cewa: –
wannan Alkur’anin an canja shi.
Sannan ya tattaro maganganun
malaman Shi’a na Fikihu da Hadisi
da suke tabbatar da hakan.
Kan wannan ne wani babban
malamin Shi’a mai suna
Ni’imatullahi Al-Jaza’iri yake cewa
“Yarda da cewa Alkur’ani waha yi
ne na Allah da kowa ya san shi, da
kuma yarda da cewa shi ne
Alkur’anin da Mala’ika Jibrilu ya
saukar da shi izuwa ga Manzon
Allah (S.A.W) zai bayu izuwa watsi
da Hadisai (na ‘Yan Shi’a) masu
yawa da suka tabbatar da cewa
Alkur’ani bai cika ba, kuma ga shi
dukkan Malamanmu (na Shi’a) sun
yadda da ingancin wadannan
Hadisai kuma sun gasgata su” .
Haka ma Ayatullahi Khumaini ya
nuni da wannan kazamar akidar a
cikin littafinsa mai suna Kashful
Asrar, ta yadda ya dinga tuhumar
Sahabbai da cewa duk wani laifi da
Allah (S.W.T) ya zargi Yahudawa
da shi na canja Attaura da Injila,
irin wannan laifin da zargin ya
tabbata a kan Sahabban Manzon
Allah (S.A.W) saboda su ma sun
aikata irin abin da Yahudawa suka
aikata.
Saboda haka, yanzu hukunci ya
rage ga ‘Yan Shi’a ko dai su yi
imani da Allah su yarda cewa ya
kare littafinsa kamar yadda ya yi
Alkawari, su yiwatsi da maganar
malamansu.
Ko kuma su yi imani da
Malamansu masu ganin Alkur’ani
bai cika ba, su karyata Allah
(S.W.T). Dabara dai ta rage ga mai
shiga rijiya!
7) Da a ce Sahabbai sun caccanja
Alkur’ani kamar yadda ‘Yan Shi’a
suke da’awa, to da sun barwa ‘yan
baya, wata mummunar Sunna. Ta
yadda duk wanda ya ga dama
daga cikinsu, sai ya canja abin da
ya ga bai da ce da son zuciyarsa
ba daga cikin Alkur’ani.
Irin yadda malaman Yahudawa
suka barwa na bayansu
mummunan Sunna ta canja duk
abin da bai da ce da son zuciyarsu
ba daga cikin Attaura da Injila.
Da ko haka abin yake, to da babu
abin da zai rage na gaskiya a
hannun jama’a. Kuma da an samu
kai cikin mafi munin jahiliyya a
tarihin wanzuwar dan Adam a
bayan kasa.
8) Allah (S.W.T) ya yi Alkawarin
halakar da duk wanda ya kara ko
ya rage wani abu daga cikin
Alkur’ani kamar
yadda Allah (S.W.T) yake cewa
“Da a ce (Manzon Allah (S.A.W) ya
kirkiri wata magana ya danganta ta
da mu. Hakika da sai mun yi masa
kamu na karfi.
Sannan mu tsinke masa jijiyar
gadon bayansa. Kuma babu wani
daga cikinku da zai iya ba shi
kariya”134
Amma a maimakon hakan, sai
Allah (S.W.T) ya tabbatar da
Sahabbai, a bayan kasa, ya ba su
rinjaye da galaba a kan dukkan
abokan gaba. Suka kai Addini
mabullar rana da mafadarta. Sai
wannan ya nuna tabbacin cewa ba
su canja Alkur’ani ba.
Da kuwa sun canja, da Ubangiji
halakar da su kamar yadda ya yi
Alkawari.
9) Idan ‘Yan Shi’a suka tsaya
tsayin daka, a kan cewa sun yarda
da Alkur’ani.
Sai mu ce,wata kila sun yadda da
Alkur’ani ne a matsayin wucin gadi.
Domin akwai maganganun
malaman Shi’a da suke nuni da
cewa, ya halatta ‘Yan Shi’a su yi
amfani da Alkur’ani a matsayin
wucin gadi, kafin bayyanar
Alkur’ani na gaskiya wanda
Mahadi zai zo da shi.135
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Mus-Hafu
Fadima, ba wani sabon Alkur’ani
ba ne. Sai dai Kur’ani ne kawai da
zai zo da bambancin kira’a ba, irin
bambancin dake tsakanin Kira’ar
Hafsu da Warshu.
Sai mu ce wannan ba haka yake
ba, saboda riwayoyin da aka samo
daga littattafan Shi’a sun siffanta
Mus-Hafu Nana Fadima da cewa
ya sha ban-ban da Alkur’anin dake
hannun muslmi ta kowa ce fuska.
Kari a kan haka dole ne kowa ce
Kira’a ta cika sharuda guda uku
kafin ta zama karbabbiya a gurin
malamai.
Sharudan su ne kamar haka: –
Na daya: – Ta zamo Kira’a ce
mutawatira wato wacce dubban
al’umma suka rawaito ta.
Na biyu: – Ta da ce da Ka’idojin
larabci sa nannu.
Na uku: – Ta da ce da rubutun
Alkur’anin da Sahabbai suka
rubuta.
Tambaya ga ‘yan Shi’a a nan ita ce
ta ya ya al’ummar musulmi za su
yarda da wani sabon Alkur’anin da
wani mutum daya kawai ya kawo
shi, wanda bai cika wannan
sharuda guda uku da muka
ambata ba?
Wani abu da ya zama cikakken
sheda dake nuna cewa ‘Yan Shi’a
ba su yarda da Alkur’anin dake
hannun musulmi ba, shi ne wata
tattaunawa da ta faru tsakanin
wani malamin Sunna mai suna
Sheikh Ar’ur na kasar Siriya da
wasu malaman Shi’a wadanda
suka yi da’awar
cewa su almajiran Mahdi ne kuma
harma suna saduwa da shi.
A ya yin wannan tattaunawa sun
kawo wata takarda wacce take
kunshe da sabuwar Ayatul
Kursiyyu, suna masu da’awar cewa
wani bangare ne na Alkur’anin
gaskiya da yake hannun
Mahdi.136
Wata tambaya da take da
mahimmanci ga ‘Yan Shi’a ita ce,
ta ya ya ‘Yan Shi’a za su yarda da
wannan Alkur’anin, bayan abu ne
sa nanne cewa, Sayyadina
Abubakar da Usman (R.A.) sune
suka tattara wannan Alkur’anin,
alhalin suna yi musu kallon kafirai
wadanda suka bar addini?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce sun yarda
da Alkur’ani ne a bisa larura,
saboda babu wani Alkur’anin sai
shi. Sannan kafircin Sayyadina
Abubakar da Umar da Usman
(R.A) bai kai munin na ragowar
kafirai ba.
Sai mu ce wannan ya karyata, abin
da yake cikin littattafan Shi’a, da
suke cike da la’antar Sahabbai da
kafirta su, irin la’antar da ‘Yan Shi’a
ba sa yiwa Yahudawa da Kiristoci.
Ta yarda har ta kai da saboda
tsananin kin da ‘Yan Shi’a suke
nunawa Sahabbai har wani lazimi
suke yi safe da yamma na la’antar
Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) da ‘ya’yansu mata guda biyu
wato Nana Aisha da Nana Hafsat
(R.A).
Amma abin mamaki ‘Yan Shi’a ba
su da lazimin la’antar Yahudawa
da Kiristoci.
Irin wannan kiyayyar ce ma tasa a
tarihin Shi’a, ba su taba goyon
bayan duk wani abu dake da alaka
da Sahabbai ba.
Sabanin kafirai da tarihin Shi’a
yake cike da goyon bayansu da
taimaka musu wajen yakar
al’ummar musulmi tun daga
zamanin da ya wuce har izuwa
yanzu. Kuma a iyaka tarihn ‘Yan
Shi’a ba su taba yakar kafirai ba
sai don wata manufa ta siyasa
kawai.
‘Yan Shi’a su gaya mana wani gari
guda daya na kafirai suka taba
yaka suka kai musu Musulunci a
da ko a yanzu.
A kullun babu abin dake gaban
‘Yan Shi’a sai cin zarafin Sahabbai
da kafirta su da da’awar cewa sun
yi ridda sun bar addini bayan
rasuwar Manzon Allah (S.A.W).
Idan wani ya ce, don me ake
tuhumar ‘Yan Shi’a da taimakawa
kafirai, bayan ga shugabannin
kasashen musulmi nan mabiya
tafarkin Sunna, suna taimakawa
kafirai suna kuma kaunar su, a
bangare guda kuma kasar da take
bin tafarkin Shi’a kamar Iran kullun
ana jinsu suna kira da a yaki
kafirai ?
Sai mu ce, wannan tunani shi ne
babbar shubuhar da take rudar
wasu daga samarin Sunna masu
kishin addini. Har suke dauka
cewa ‘Yan Shi’a su ne a kan dai-
dai, bayan abin ba haka yake ba.
Da farko ya kamata a fahimci
cewa, akwai banbanci tsakanin
abin da shugabannin musulmi
mabiya tafarkin Sunna suke
aikatawa da abin da Sunna ta
koyar.
Ba duk abin da mai bin tafarkin
Sunna yake aikatawa ba ne addini,
kamar yadda ba duk abin da
musulmi yake aikatawa bane yake
zama musulunci.
Akwai bambanci tsakanin aikin
Ahlu Al-Sunna da koyarwar Sunna,
kamar yadda yake akwai bambanci
tsakanin musulmi da koyarwar
Musulunci.
Fahimtar wannan zai taimaka
kwarai da gaske a wajen tantance
tsakanin kwaya da tsakuwa.
Karancin wannan fahimtar ne yasa
wasu suke kallon ayyukan
azzaluman shugabanni tamkar
koyarwar Sunna.
Irin wannan mummunar fahimtar
ce ta sa ‘Yan Shi’a suke kawo
ayyuka na azzaluman sarakunan
Banu Umayya da Banil Abbas da
sauran sarakuna azzalumai masu
bin tafarkin Sunna, suke danganta
hakan da koyarwar Sunna.
Wannan kuwa babban kuskure ne!
Abin da ya kamata a sani shi ne
duk Malaman Sunna sun hadu a
kan wajabcin aiki da Alkur’ani da
Hadisi a cikin dukkan sha’anin
rayuwar al’umma musulmi. Babu
wani Sabani tsakaninsu a kan
wannan. Sannan kuma sun hadu a
kan haramcin zalunci da wajabcin
kawar da shi daga doron kasa
gwargwadon ikon kowa da damar
da yake da ita.
Saboda haka kada wani ya fassara
aikin azzaluman Shugabanni da
jahilan ‘yan boko wadanda su ke
ganin Alkur’ani ya tsufa ko kuma
ya kalli son zuciya na Malaman
Gwamnati a matsayin koyarwar
Sunna.
Kari a kan haka, yakin da ‘Yan
Shi’a suke da’awar da a kaddamar
a kan kafirai yaki ne kawai na
cacar baka ba yaki na gaskiya ba.
Suna da’awar jihadi ne kawai don
yada farfaganda da kokarin farauto
samarin Sunna wadanda suke da
shauki na ganin tabbatuwar addini
a bayan kasa. Hakan ne ma yasa
samari da yawa na Sunna suka
fada tarkon Shi’a a garuruwa da
dama kamar yadda muke gani.
Kuma malaman Sunna da dama,
sun yi rubuce-rubuce a kan haka
don jan hankalin musulmi.
Banda wannan ma, a lokacin da
‘Yan Shi’a suke zargin kasashe
mabiya Sunnah, da yin kawance
da kafirai. Sai ga shi a hannu guda
suna kawance da kasashen
maguzawa kamar tarayyar Rasha,
wadanda ta’addancin su ya fi muni
fiye da kasashen Kiristoci.
Musulunci kuwa ya bambance
tsakanin Maguzawa da Kiristoci a
hukunce-hukunce masu yawa.
Kamar yadda koyarwar Manzon
Allah (SAW) ta bambance
tsakaninsu, da alakar da ya
kamata a yi da kowannensu.
11- Kudurce cewa: – akwai wani
boyayyen Alkur’ani a gurin Mahdi
Limamin ‘Yan Shi’a na sha biyu ya
saba da abin da ya tabbata daga
jagororin Ahlu Al-baiti, wato
Sayyadina Ali da Abdullahi dan
Abbas (R.A). Domin ya tabbata
daga gurinsu cewa: – Manzon Allah
(S.A.W.) bai bar musu komai ba,
kuma ba su da wani Alkur’ani in
banda wanda yake hannun
mutane.
Kamar yadda hakan, ya saba da
abin da dukkan Ahlu Al-Baiti suke
a kai, domin rayuwarsu cike take
da misali, wajen aiki da wannan
Alkur’anin da karantar da shi da
kiran mutane kan su yi aiki da shi.
Saboda haka, dangantawa Ahlu
Al-baiti wani Alkur’ani na
musamman banda wanda yake
hannun mutane, sharri ne kawai da
kage ga Ahlu Al-baiti.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce canje-
canjen da Sahabbai suka yiwa Al-
kur’ani ya shafi lafazinsa ne kawai
amma bai shafi asalin ma’anarsa
ba.
Sai mu ce wannan Tawili ne mara
tushe da asali da malaman Shi’a
suka saba yi don su kare kansu
daga kallon da al’umma suke yi
musu na rashin Imani da Alkur’ani
Kari a kan haka, wannan Tawili ba
zai samu karbuwa ba saboda
dalilai kamar haka: –
Na daya:- Allah (S.W.T) ya yi
Alkawarin kare Al-kur’ani hakan
kuwa ya shafi lafazinsa da
ma’anarsa.
Na biyu: – Duk sanda aka canja
wani lafazi a wata jumla to ba
makawa sai ma’anar wannan
jumla ta canja.
Na uku: – Riwayoyi da suka zo
cikin litattafan Shi’a suna karyata
wannan Tawili, dalili kuwa suna
nuni da cewa Sahabbai sun canja
Alkur’ani ta lafazinsa da
Ma’anarsa.
Na hudu: – Da a ce a yanzu wani
zai canja lafazin Alkur’ani da
gangan ba cikin kuskure ba, to da
malamai sun hadu wajen yi masa
inkari koda kuwa lafazin da ya
musanya yafi wanda ya canja fadin
ma’ana. Misali mutum ya canja
lafazin Al-Nabiyyu da Al-Rasulu
tare da cewa lafazin Al-Rasulu ya fi
fadin ma’ana.
Shi yasa ya tabbata cewa lokacin
da Bara’u dan Azib (R.A) ya
canjawa Manzon Allah (S.A.W)
lafazin da ya koya masa na Addu’a
wato ya fadi lafazin Al-Rasulu a
maimakon Al-Nabiyyu, sai Manzon
Allah (S.A.W) ya ce: – masa “Al-
Nabiyyu na ce da kai ba Al-Rasulu
ba.” Don haka canja Alkur’ani ta
kowa ce fuska, yana rushe
manufar saukar da shi, yana kuma
bayuwa ga suka izuwa wanda ya
saukar da shi, ya kuma yi
alkawarin kare shi. Kuma kokari ne
na ruguza addini baki daya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

6 responses to “DARASI NA GOMA (10)SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI’A(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. Ahmad Yusuf Assqalaini Avatar
    Ahmad Yusuf Assqalaini

    Ashe ka yarda Imam Ali (as), da Imam Hassan, limaman shi’ane, to me yasa kuma kake masu kazafi? Me kake gani ranar kiyama idan aka tayardakai cikin makiyan mabiyansu? Kuma bari kajiya shi’a KADAN KENAN, don wallahi saita mamaye duniya baki daya, gwargwadon sukarda kukeyi gwargwadon habakarta. Sai dai ku mutu amma mazhabar iyalan gidan annabta KADAN KENAN !!!

  2. Abu Hanifa Avatar

    KAI AHMAD KA MAKARA YANZU YAN SHI’A SUKE MUSULUNTA SABO DA QAZANTAR DAKE CIKINTA DA MUGUNYAR ADDUA’AR DA IMAM ALI R.A YA MATA MUSAMMAN NA CIKIN NAHJ BALAGA KHUDUBA TA 34 KAMAR HAKA: ومن خطبة له عليه السلام
    أُفٍّ لَكُمْ (1) ! لَقَدْ سَئِمْتُ عِتَابَكُمْ! أَرَضِيتُمْ بِالْحَيَاةِ الدُّنْيَا مِنَ الْآخِرَةِ عِوَضاً؟ وَبِالذُّلِّ مِنَ الْعِزِّ خَلَفاً؟ إِذَا دَعَوْتُكُمْ إِلَى جِهَادِ عَدُوِّكُمْ دَارَتْ أَعْيُنُكُمْ (2) ، كَأَنَّكُمْ مِنَ الْمَوْتِ فِي غَمْرَةٍ (3) ، وَمِنَ الذُّهُولِ في سَكْرَةٍ، يُرْتَجُ (4) عَلَيْكُمْ حَوَارِي (5) فَتَعْمَهُونَ (6) ،فَكَأَنَّ قُلُوبَكُمْ مَأْلُوسَةٌ (7) ، فَأَنْتُمْ لاَ تَعْقِلُونَ. مَا أَنْتُمْ لي بِثِقَةٍ سَجِيسَ اللَّيَالي (8) ، وَمَا أَنْتُمْ بِرُكْنٍ يُمَالُ ( 9

  3. Ali Salisu Avatar
    Ali Salisu

    NI HAR RANA MAI KAMAR TA YAU, BANGA Al-Qur’anin DA KUKE CEWA ‘Yan Shi’a SUNA DA SHI BA!
    A MATSAYIN KU NA Mallamai, YA KAMATA KU DINGA FA’DAR ABIN DA YAKE NA ZAHIRI BA SHACI FA’DI BA.
    KO DA BABU KUMAI, SAI ALLAH YA TAMBAYEMU AKAN ABUBUWAN DA MUKA AIKATA NA ZAHIRI, DA WA’YAN DA ZUCIYOYIN MU SUKA RAYA MANA!
    ALLAH YA KYAUTA.

  4. Mungode Allah Ya Saka Da Alheri

  5. […] Source: DARASI NA GOMA (10)SHUBUHOHIN SHI’A AMAHANGAR SHARI’A(Malam Aminu Ibrahim Daurawa) […]

  6. Yan Shi’a Allah Ya Shiryaku

Leave a Reply

Categories
Latest updates