DARASI NA GOMA SHA DAYA(11) A CIKIN LITTAFIN SHUBUHOHIN 'YAN SHI'AH(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)

Bismillahir Rahmanir Rahim
Jama’ar wannan zaure namu mai
albarka, zamu ci gaba daga inda
muka tsaya a littafin mu na
“SHUBUHOHIN SHI’A A
MAHANGAR SHARI’A” na Hamza
Uba Abubakar Kabawa gabatarwar
Muhammad Aminu Ibrahim
Daurawa.
Yau zamu tashi : –
ADAWAR SHI’A DA KIYAYYAR
SU GA SAHABBAI, HAR YA KAI
DA SUNA KAFIRTA SU.
Shubuha ta takwas wacce ‘Yan
Shi’a mai limamai goma sha biyu
suke yadawa ita ce: – Sahabban
Manzon Allah (S.A.W) dukkaninsu
sun yi ridda, sun bar Addini bayan
rasuwar Manzon Allah (S.A.W) in
banda mutum hudu ko shida.
Mutanen kuwa su ne Sayyadina
Ali, Ammaru ibn Yasir, Abu Zarril-
Gifari, Mikdar Ibn Aswad, Salmanul
Farisi da Huzaifa (R.A).
Shubuhohi mafi shahara da suke
amfani da su, su ne kamar haka: –
Na daya: – Sahabbai sun ki su yi
aiki da wasiyyar da Manzon Allah
(S.A.W) ya yi musu cewa
Sayyadina Ali (R.A) shi ne Halifa a
bayansa.
Na biyu: – Fadin Ubangiji (S.W.T)
“Muhammad bai kasance ba fa ce
Manzo daga Allah, kuma Manzanni
da yawa sun shude gabanninsa.
Yanzu idan aka ce ya mutu ko an
kashe shi sai ku bar Addini?
Wanda duk ya bar Addininsa ba
zai cutar da Allah komai ba. Kuma
da sannu Allah (S.W.T) zai sakawa
musu godiya”
Na uku: – Hadisi ya tabbata cewa:
Ranar Alkiyama, Manzon Allah
(S.A.W) zai ga wasu mutane cikin
al’ummarsa sun gane shi, shi ma
kuma ya gane su.
A wannan lokacin zai dinga kiransu
izuwa shan ruwan Alkausara. Sai
Mala’iku su dinga korarsu.
Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: –
“Sahabbai na ne”
Sai Mala’iku su ce: – “Ai sun canja
bayanka.”
Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “A
yi nesa da su, a yi nesa da su”
Jawabi a kan wannan shubuha shi
ne ta fuskoki kamar haka: –
1) Dalilai sun gabata a kan cewa
babu wata ayar Alkur’ani ko
ingantaccen Hadisi, dake nuni da
cewa Manzon Allah (S.A.W) ya yi
wasiyya ga Sayyadina Ali (R.A) a
matsayin halifansa, balle a ce
Sahabbai sun sabawa wannan
wasiyyar.
2) Alkur’ani mai girma cike yake da
sheda ta imani, alkawarin Aljanna
da sheda ta arziki ga dukkan
Sahabban Manzon Allah (S.A.W).
Idan ‘Yan Shi’a suka ce duk wata
aya ko Hadisi dake yin shaidar
arziki ga sahabbai ta shafi iyaka
Sahabban da suka rasu ne lokacin
da Manzon Allah (S.A.W) yake a
raye.
Sai mu ce babu inda Alkur’ani ya
iya kance nau’in Sahabban da
Allah (S.W.T) ya gafartawa. Bari
ma dai Alkur’ani ya yi magana ne a
kan dukkan Sahabban Manzon
Allah (S.A.W) baki daya, daga cikin
wadanda suka yi Hijra da mutanen
Madina da wadanda suka yi Jihadi,
suka kuma ciyar da dukiyarsu kafin
sulhun Hudaibiyya da bayansa.
Kari a kan haka, duk san da Allah
(S.W.T) ya yi Alkawarin Aljanna ga
wani mutum, to hakan ya kunshi
abubuwa kamar haka: –
Na daya: – Tabbacin zartar da
wannan alkawarin saboda Allah
(S.W.T) ba ya saba alkawari, kuma
babu wanda ya isa ya hana shi
zartar da abin da yake so.
Na biyu: – Tabbacin mutuwar
wannan mutumin da imani, saboda
ilimin Allah (S.W.T) ya kewaye da
komai, babu abin da yake buya
gare shi a kowane lokaci.
Na uku: – Tabbacin cewa wannan
mutumin ba zai aikata wani aiki da
zai hana shi shiga Aljanna ba,
kamar Shirka, Kafirci ko Munafunci.
Maganganun Sayyadina Ali
(R.A) da irin yadda ya yi mu’amula
da Sahabbai sun karyata da’awar
‘Yan Shi’a cewa Sahabbai sun yi
ridda. Saboda ya yi mu’amula da
su ta ‘yan uwantaka da son juna.
Ya kuma yi musu sheda ta imani
da tsoron Allah. Hasali ma ya yi
surukantaka da su, ya kuma
sanyawa ‘ya’yansa sunayensu.
Sabanin ‘Yan Shi’a wadanda
Sayyadina Ali ya dinga yi musu
sheda ta tsiya da kangarewa.
Misali Sayyadina Ali (R.A) ya
siffanta ‘Yan Shi’a da cewa “Duk
irin jinkirin da Allah (S.W.T) ya
yiwa Azzalumi, to ba zai gujewa
kamun Allah ba. Ubangiji yana
madakata yana jiransa. Duk
hanyar da zai bi, zata kai shi ne
zuwa ga Allah.
Na rantse da wanda raina yake a
hannunsa, sai mutanen Sham sun
yi rinjaye a kanku, ba wai don su
ne suka fi ku kusanci da gaskiya
ba, sai don kokarinsu wajen bin
shugabansu ko a kan kuskure ne,
da yadda ku kuma kuke ja da baya
kan umarni na.
Al’ummomi sun wa yi gari suna
tsoron zaluncin shugabanninsu, ni
kuwa na wa yi gari ina jin tsoron
zaluncin mabiya na.
Na yi umarni da a fito jihadi kun ki
fitowa, na gaya muku gaskiya kun
ki binta. Na kiraye ku a fili da boye
amma kun ki amsawa. Na yi muku
nasiha kun ki karbarta.
Kun kasance kuna tare da ni
amma gwara a ce ba ku ne tare da
ni ba, ga ku mabiya amma kun
mayar da kanku tamkar
shugabanni.
Ina karanta muku hikimomi, amma
kuna gudunsu. Na yi muku
gamsashshen wa’azi amma kun
watse.
Na kwadaitar da ku jihadi a kan
‘yan tawaye, amma kafin na kai
karshen magana ta duk kun gudu,
kun koma guraren zamanku kuna
yaudarar junanku.
Na mikar da ku da safe, amma
kafin yamma kun tankware kamar
yadda macijiya ke tattankwarewa.
Na gaji da mikar da ku, kullum
kuna kaucewa.
Ya ku wadanda nake tare da
jikinsu, amma tunaninsu yana wani
gurin, zuciyarsu kuma ta rarraba.
Ya ku wadanda suka zama bala’i
ga shugabanninsu.
Ni ina biyayya ga Allah, amma
kuna saba min. Shugaban Sham
yana Sabawa Allah, amma
mabiyansa suna yi masa da’a.
Wallahi na yi burin a ce Mu’awiyya
(R.A) ya musanya min wasu da ku
kamar yadda ake canjin kudi, ya
dauki mutum goma daga cikinku ya
bani mutum daya a maimakonsu.
Ya ku mutanen Kufa, ga ku da
kunnuwa amma bakwa ji, ga ku da
bakuna amma bakwa magana ta
gaskiya, ga idanuwa amma bakwa
ganin gaskiya. Ga ku makaryata
lokacin haduwa da abokan gaba,
ga ku wadanda suke mayaudara a
lokacin bala’i. Hakika kun tabe.
Ya ku wadanda suke kamar
rakuman da ba su da mai kula da
su, duk sanda aka tattaro su ta
nan, sai su watse ta can…”
Kun ji fa irin yadda Sayyadina Ali
(R.A) yake siffanta mabiyansa.
Tabbas Sayyadina Ali (R.A) ya yi
gaskiya, saboda duk irin yadda ya
siffanta su haka suke, tun daga
zamaninsa har izuwa yau.
Duk wani bala’i su ne suke jefa
Ahlu Al-Baiti ciki. Sai su yaudare
su, su ce suna tare da su, za su
taimake su amma da an fito filin
daga, sai su watse, su kyale a
hallaka su, kamar yadda suka yiwa
Sayyadina Husaini da Zaid dan
Aliyu dan Husaini (R.A), Allah ya
karbi Shahadarsu.
Amma a daya bangaren ga irin
yadda Sayyadina Ali (RA) yake
siffanta Sahabbai da cewa “Hakika
na ga Sahabban Manzon Allah
(S.A.W) ban taba ganin wani
mutum a duniya da ya yi kama da
su ba.
Sun kasance ma’abota kan-kan da
kai da gudun duniya. Ga su koda
yaushe suna kwana cikin sujjada
da tsayuwa saboda tsoron Allah.
Kai ka ce a kan garwashi suke
saboda tunanin makomarsu.
Guiwoyinsu sun yi kaushi saboda
yawan Sujjada. Duk sanda aka
tunasar da su Allah sai idanunsu
ya cika da hawaye, har sai
rigunansu sun jike. Ga su masu
biyayya da mika wuya kamar
yadda bishiya take mika wuya ga
iskar da ke kada ta. Duk suna yin
haka ne saboda tsoron azabar
Allah da kwadayin rahamarsa”.
Alherin Allah ya gaida Sayyadina
Ali (R.A) zakin Allah, kun ji fa
yadda yake siffanta mabiyansa da
muna nan siffofi da kuma yadda
yake siffanta Sahabbai da
kyawawan siffofi. Kamar yadda
Allah (S.W.T) ya siffanta su da su.
Wannan ayar ta cikin suratu Ali-
Imran wato Fadin Ubangiji (S.W.T)
“Muhammad bai kasance fa ce
Manzo daga Allah, kuma Manzanni
da yawa sun shude gabanninsa.
Yanzu idan aka ce ya mutu ko an
kashe shi sai ku juya baya a kan
duga duganku? Wanda duk ya
juya baya a kan dugadugansa ba
zai cutar da Allah komai ba. Kuma
da sannu Allah (S.W.T) zai sakawa
masu godiya” Ta sauka ne saboda
jita-jitar aka watsa cewa an kashe
Manzon Allah (SAW) a yakin Uhud.
Don haka, ba ta da wata alaka da
wafatin Manzon Allah (S.A.W).
Domin Ubangiji (S.W.T) yana jan
hankalin Sahabbai ne da cewa:
“To yanzu idan an ce an kashe
Manzon Allah (S.A.W.) ko ya mutu
sai ku gudu? Ai koda Manzon Allah
(SAW) ya mutu ko an kashe shi, to
ba kansa farau ba. Domin
Annabawa da yawa sun mutu kafin
shi, kuma wasu da yawa daga
cikinsu an kashe su a filin daga.
Amma mabiyansu ba su ja da baya
ba, ba su kuma gudu ba, ba su
bada kai bori ya hau ba, ba su
kuma bar Addini ba.
Saboda haka, kuma ku tsaya a kan
Addini, ku dage kada ku ja da
baya, koda an ce Manzon Allah
(S.A.W) ya mutu ko an kashe shi.
Saboda Addini na Allah ne, kuma
shi ne zai kare kayanSa.
Shi yasa godiya ta tabbata ga
Allah, ba’a samu wani daga cikin
masu Hijira ko mutanen Madina,
wanda ya yi ridda bayan Manzon
Allah (S.A.W) ya rasu ba. Hasali
ma, su ne suka yaki dukkan
wadanda suka yi ridda, suka dawo
da su kan Addini, marasa rabo
kuma aka kashe su ba tare da sun
tuba ba.
Su ne alkawarin Ubangiji (S.W.T)
ya gasgatu a kan su na cewa, duk
sanda mutane suka yi ridda, to zai
zo da wasu mutane da za su yake
su, yana son su kamar yadda suke
son Sa. Basa jin tsoron zargin mai
zargi.
Da kuwa a ce Sahabbai ne suka yi
ridda kamar yadda ‘Yan Shi’a suke
da’awa, to lallai da Ubangiji
(S.W.T) ya zo da mutanen da zasu
yake su kamar yadda ya yi
alkawari.
5) Sayyadina Ali (R.A) bai taba
kafirta wani ko ya ce ya yi ridda ba,
saboda bai yi masa mubaya’a ba.
Tare da cewa akwai mutane da
yawa da ba su yi masa mubaya’a
ba, kamar mutanen Sham da
Khawarijawa wadanda suka yi
masa bore har ta kai da suka yake
shi, amma duk da haka bai taba
cewa sun kafirta ba.
Kalmar Sahabi dake cikin
wancan Hadisin da ‘Yan Shi’a suke
kafa hujja da shi kan riddar
Sahabbai, bata shafi Sahabbai na
mahangar shari’a ba.
Saboda ita kalmar Sahabi tana da
gamammiyar ma’ana da
kebantacciya a gurin malamai.
A gamammiyar ma’ana kalmar
Sahabi tana nufin abokin alaka,
duk daya ne, na gari ne ko ba na
gari ba, mutum ne ko dabba mai
rai ne ko mara rai.
A takaice dai, duk wani abu da
wata alaka ta hadaka da shi ana
iya cewa da shi sahibinka wato
abokinka. Shi yasa a gamammiyar
ma’ana, Allah ya ce da kafiran
Makka Sahabbai wato abokan
zaman Manzon Allah (S.A.W) a
gari, ko dan uwansu na jini. Kamar
yadda Allah ya ce: – “Sahibinku
wato abokinku ko dan uwanku bai
kasance batacce ba, kuma bai
ketare iyaka ba”
Kamar yadda Allah (S.W.T) ya ce
da Annabi Yunus (A.S.), abokin
kifi . Kuma ya ce da mutanen nan
da suka fake a kogo abokan kogo .
Kai ko sau daya, wata alaka ta
hada ka da wani, a kan ce masa
abokinka, ko da kuwa wata alaka
bata sake hada ku da shi ba.
Saboda haka ne ake cewa abokin
tafiya Sahibi .
Amma a wajen Malaman Hadisi,
kalmar Sahabi tana da wata
ma’ana ta musamman.
Sahabi a gurin Malaman Hadisi shi
ne , wanda ya hadu da Manzon
Allah (S.A.W), kuma ya yi imani da
shi, sannan ya mutu da Imani.
A kan haka, duk wanda ya hadu da
Manzon Allah (S.A.W) amma bai yi
imani da shi ba, a fili da boye ko
kuma ya yi imani da shi a fili amma
bai yi imani da shi a boye ba, to
ba’a ce masa Sahabi.
Haka nan wanda ya hadu da shi,
ya yi imani da shi, amma daga
baya ya canja, shi ma ba’a ce
masa Sahabi.
Saboda haka a wannan Hadisin,
Manzon Allah (S.A.W) yana
magana ne, a kan mutanen da
suka gan shi, suka yi imani da shi,
amma daga baya suka canja.
Kamar galibin Larabawan
garuruwa da kauyuka da suka zo,
suka yi masa mubaya’a bayan
bude Makka, amma rasuwarsa ke
da wuya sai suka canja .
Wasu suka ce sun daina ba da
Zakka. Wasu suka ce su sun koma
kan Addinisu na da (wato na
gargajiya). Wasu ma daga cikinsu
suka yi da’awar Annabta.
Kamar yadda wannan hukunci ya
hada da munafukan da suka rayu
da Manzon Allah (S.A.W) amma
Allah (S.W.T) bai sanar da shi
sunayensu ba. Saboda ba dukkan
sunayen munafukai, Allah (S.W.T)
ya sanar da Manzon Allah (S.A.W.)
ba. Kamar yadda Allah (S.W.T) ya
ce: “Daga larabawan kauyukan
dake kewaye da Madina akwai
munafukai, haka ma daga mutanen
Madina sun kware a cikin
munafunci, kai baka sansu ba
amma mu mun sansu” .
Duk wadannan bangarori da muka
ambata ana ce musu Sahabbai a
gamammiyar ma’ana. Kuma
Manzon Allah (S.A.W.) a Sahabbai
ya sansu, har ya koma izuwa ga
Allah (S.W.T). Amma bayan
rasuwarsa bai san wasu sun bar
Addini ba, shi yasa ya ce:
Sahabbansa ne. Ya kuma ce ya
gane su. Amma sai Mala’iku suka
ce, da shi ai sun canja a bayanka.
Da Manzon Allah (S.A.W.) ya ji
haka sai ya ce: a yi nesa da su.
Abin da yake tabbatar da haka shi
ne , a wata riwayar Manzon Allah
(S.A.W) cewa ya yi “Sai na fadi irin
abin da Annabi Isa (A.S.) ya fada
“Na kasance mai sheda a kansu
lokacin da nake raye a cikinsu,
amma bayan ka karbi raina kai ne
kadai mai kulawa da kiyaye al-
almarinsu, kuma lallai kai mai
sheda ne a kan komai.”
Ma’ana, Annabi Isa (AS), a lokacin
rayuwarsa babu mai cewa da shi
dan Allah, ko Allah, ko dayan ukun
Allah.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce lallai
wannan Hadisin yana magana ne
a kan Sahabbai irin su Sayyadina
Abubakar, Umar da Usman (R.A)
da ragowar masu Hijra da
Mutanen Madina.
Sai mu ce me ‘Yan Shi’a za su ce
dangane da Hadisan da suka zo
suka tabbatar da cewa wadannan
mutane ‘yan Aljanna ne? har wasu
ma Manzon Allah (S.A.W.) ya bada
labarin irin gidan da Allah ya gina
musu a Aljanna, har ma ya ce: ya
so ya leka, kamar Sayyadina Umar
(R.A) .
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Manzon
Allah (S.A.W.) ya ce: musu ‘yan
Aljanna ne kafin su yi ridda.
Sai mu ce ba haka lamarin yake
ba, domin abin da aka rawaito
daga jagoran Ahlu Al-baiti wato
Sayyadina Ali (R.A) ya karyata
hakan.
Misali, lokacin da Sayyadina Umar
(R.A) ya rasu Abdullahi dan Abbas
(R.A) ya ce: ina tsaye, sai na ji
wani mutum ya dafa min kafada ta,
ta baya. Da na juyo sai na ga
Sayyadina Ali (R.A) ne.
Sai Sayyadina Ali (R.A) ya ce: –
“Allah ya yi maka rahama (ya
Umar) lallai nasan cewa Allah zai
riskar da kai da abokanka guda
biyu (Wato Manzon Allah (S.A.W.)
da Sayyadina Abubakar (R.A).
Domin sau tari na kan ji Manzon
Allah (S.A.W.) ya ce: – “Na kasance
tare da Abubakar da Umar (R.A),
na aikata tare da Abubakar da
Umar (R.A), na fita tare da
Abubakar da Umar (R.A)”. A wata
riwayar ma Sayyadina Ali (R.A)
cewa ya yi: – “Babu wani mutum da
ya rage a duniya da nake fatan na
tsaya a gaban Allah da irin aikinsa
sai Sayyadina Umar (R.A)”.
Kuma Hadisi ya tabbata daga
Ammar dan Yasir (R.A) lokacin da
Sayyadina Ali (R.A) ya aike shi
Kufa tare da dansa Hasan (R.A)
don neman goyan bayan su (Wato
mutanen Kufa).
A cikin hudubarsa Ammar (R.A) ya
ce: – “Na tabbata har ga Allah
Nana Aisha (R.A) matar Annabi ce
a duniya kuma matarsa ce har a
Lahira” .
Haka ma ya tabbata daga
Abdullahi dan Abbas (R.A) ya ce:
da Nana Aisha (R.A) lokacin da
bata da lafiya “ya babar muminai
za ki koma ga magabata na
gaskiya wato Manzon Allah
(S.A.W.) da Abubakar (R.A) “
Idan ‘Yan Shi’a suka ce Sayyadina
Ali (R.A) yaki fadar gaskiya ne,
saboda yana tsoron kada a cutar
da shi.
Sai mu ce ba haka lamarin yake
ba. Saboda Sayyadina Ali (R.A) bai
gushe ba a iyaka rayuwarsa yana
yin shaida ta arziki ga Sahabbai a
fili da boye.
Akwai kungiyoyin Shi’a da
Khawarijawa da suke kafirta
Sayyadina Ali (R.A) suna masu
da’awar cewa ya yi ridda kuma duk
wata falala da ta tabbata a kansa
ta ruguje. Kwatankwacin da’awar
‘Yan Shi’a a kan Sahabbai.
Kuma wani abin mamaki shi ne ,
daga cikin irin dalilan da suke
dogara da su, akwai wannan
Hadisin na Tabki da ‘Yan Shi’a
suke dogara da shi.
Don haka, kungiyoyin bidi’a da
yawa, sukan fake da wannan
Hadisin, don kafirta wanda suka ga
dama.
‘Yan Shi’a su fake da wannan
Hadisin, su kafirta junansu, ko su
kafirta Sahabbai.
Khawarijawa su fake da wannan
Hadisin, su kafirta Sayyadina Ali
(RA) da Sayyadina Mu’awiya da
mabiyansu.
Kowace kungiya dai, suna kallon
Hadisin yadda ya dace da son
zuciyarsu.
Don haka, zai yi wuya, ka samu
wani Hadisi ko aya da ‘Yan Shi’a
ke amfani da su, wajen kafirta
Sahabbai. Fa ce sai ka samu
cewa, wasu kungiyoyin bidi’a, suna
amfani da wannan Hadisin ko ayar,
wajen kafirta Sayyadina Ali (RA)
da Ahlu Al- Baiti.
Sabanin Ahlu Al-Sunna da suke
tabbatarwa da Sahabbai da Ahlu
Al-baiti falalar da Allah ya ba su,
suke yi musu shaida ta alheri, tare
da yi musu addu’ar gafara, a kan
kura-kuransu kamar yadda ayoyin
Alkur’ani da Hadisai suka umarce
mu. Da wannan ne Ahlu Al-Sunna
suka fi kowa karfin hujja, kuma
babu tufka da warwara a cikin
maganganunsu.
8) Daga abin da yake dada
tabbatar da gaskiyar abin da muka
fada cewa, Sayyadina Ali (R.A) da
Limaman Ahlu Al-baiti, ba su taba
kallon Sahabbai a matsayin kafirai
ba, shi ne abin da duk littattafan
Shi’a suka kawo cewa Sayyadina
Ali (R.A) ya aurawa Sayyadina
Umar (R.A) ‘yarsa wacce suka
haifa da Nana Fadima (R.A) ‘yar
Manzon Allah (S.A.W) wato
Ummu-Khulsum (R.A).
Dadin dadawa Malaman Shi’a sun
kawo a littattafansu cewa: –
Sayyadina Abubakar da Umar
(R.A) su ne suka shawarci
Sayyadina Ali (R.A) da yaje ya
nemi auren Nana Fadima (R.A) a
wurin Manzon Allah (S.A.W).
Sayyadina Usman (R.A) Kuma shi
ne ya biya sadakin auren. Sannan
Sayyadina Abubakar, da Umar da
Usman, da Zubairu, da Dalhatu
(R.A), Sune wanda Manzon Allah
(S.A.W) ya tura Sayyadina Anas
(R.A) da ya je ya kirawosu, sannan
ya ce: da su “ku zamo shaida na
aurawa Sayyadina Ali (R.A) Nana
Fadima (R.A)”.
Wani abin dake karyata
maganganun ‘Yan Shi’a cewa wai
Sahabbai sun yi ridda, bayan
rasuwar Manzon Allah (S.A.W.)
idan ban da mutum hudu ko shida
shi ne fadin Ubangiji cikin suratul
Waki’a, yana mai kawo mana
hoton yadda al’umma zasu
kasance a ranar Alkiyama: –
“Akwai ma’abota dama, wa ya
sanar da kai, su waye ma’abota
dama (Muminai). Da kuma
ma’abota hagu, wa ya sanar da kai
su waye ma’abota hagu? Sai
wadanda suke ‘yan aji na farko na
can gaba, wadannan su ne
makusanta (Allah). Cikin Aljanna ta
ni’ima, daga cikinsu akwai
mutanen farko masu yawa
(Sahabbai) da kuma mutanen
karshe ‘yan kadan”
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce su waye muta nan farko idan ba
Sahabbai ba?
Kuma yanzu a ce da mutane shida
masu yawa kamar yadda ‘Yan
Shi’a suka ce su kadai ne ba su
kafirta ba?
Abin da yake fito da wannan fili shi
ne , Hadisin Ukashetu dan Mihsan
(R.A) wanda ya bada labari cewa: –
Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: – “An
nuna min yadda kowa ce al’umma
zata zo ranar Alkiyama. Sai na ga
wani Annabi da mutanen da ba su
fi goma ba.
Wani Annabin da mutane biyu.
Wani Annabin da mutum daya.
Wani Annabin shi kadai.
Daga nan sai na ga wata al’umma
masu yawa, har na yi zaton ko
al’umma ta ce.
Sai aka ce wannan Annabi Musa
(A.S) ne tare da al’ummarsa.
Daga nan sai ga wata al’umma
tana ketowa ta ko ina.
Sai aka ce ga al’ummarka nan a
cikinsu akwai mutane dubu saba’in
wanda zasu shiga Aljanna ba tare
da hisabi ba. Sai Ukashe ya ce: –
“ya ma’aikin Allah roka min Allah
ya sanya ni daga cikinsu” sai
Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: –
“kana cikinsu”
Wasu ruwayoyin ma sun nuna
cewa Manzon Allah (S.A.W), ya
roki Allah ya kara masa, sai a ka
kara masa dubu saba’in sau dubu
saba’in.
Abin lura a nan shi ne Ukashe dan
Mihsan (R.A) ya yi Shahada ne
lokacin halifancin Sayyadina
Abubakar (R.A), a yakin da aka
gwabza tsakanin rundunar
Musulmi karkashin jagorancin
Khalid bin Walid da sojojin
Dulaihatul Asadi wanda ya yi
da’awar Annabta shekara ta sha
biyu da hijira.
Shi kuwa Ukashet (R.A) baya daga
cikin mutane shidan da ‘Yan Shi’a
suke da’awar su kadai ne ba su yi
ridda ba, bayan wafatin Manzon
Allah (S.A.W).
Idan mai karatu ya hada tsakanin
wannan Hadisin da wannan ayar,
sai ya sha mamakin son zuciyar
‘Yan Shi’a da karfin halinsu da
suke da’awar cewa dukkan
Sahabbai sun yi ridda in ban da
mutane shida.
Kuma wannan shi yake dada
tabbatar da abin da muka fada tun
da farko cewa, ‘Yan Shi’a sun bata
ta rashin ingantaccen dalili da
rashin fahimtarsa.
A kan haka Sheikhul Islam ibn
Taimiyyah da ragowar malaman
Sunna suke cewa, duk a cikin
kungiyoyin bidi’a babu kungiyar da
suke da son zuciya, makaryata,
kuma wadanda ba su fahimci
shari’a ba, irin ‘Yan Shi’a.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce wannan
ayar da Hadisin duk suna nuni ne
izuwa ga mabiya Sayyadina Ali
(R.A), domin su kadai ne ‘yan
Aljanna.
Sai mu ce wannan ba haka yake
ba, saboda dalilai kamar haka: –
Na daya: – Duk cikin Sahabbai da
Tabi’ai da Tabi’un – Tabi’un da
sauran Salihai ba yi na gari da
tarihi ya dawwamar da sunayensu,
cikin malaman Hadisi da Fikhu
dana Alkur’ani da jagoririn Jihadi
da shuwagabanni musulmi masu
adalci babu wanda yake da akidar
Shi’a kuma babu dan Shi’a.
Na biyu: – Duk cikin Ahlu Al-baiti
tun daga Bani Hashim da Banil
Muddalib da Matayen Manzon
Allah (S.A.W) da zuriyarsa, babu
wani dan Shi’a, kuma babu mai
akidar Shi’a ko daya. Babu kuma
wanda yake da’awar shi ma’asumi
ne, ballanta ya yi da’awar cewa
akwai wasu Ma’asumai goma sha
biyu.
Na uku: – Abubuwan da aka
rawaito daga Ahlu Al-baiti suna
karyata wannan maganar, domin
ba su taba cewa Sahabbai kafirai
ba ne, hasali ma suna yi musu
shaida ta alheri ne.
Na hudu: – Sayyadina Ali (R.A) da
kansa ya tabbatar da nagartar
Sahabbai a bangare guda, a daya
bangaren kuma ya siffanta masu
akidun Shi’a da bata da halaka.
Don ya tabbata daga Sayyadina Ali
(R.A) cewa ya kona wasu daga
cikin ‘Yan Shi’a, ya kori wasu daga
gurinsa, ya kuma la’anci wasu, ya
yi alkawarin horo mai tsanani ga
duk wanda ya fifita shi a kan
Sayyadina Abukakar da Umar
(R.A).
Ya kuma tabbata daga Muhammad
dan Ali dan Abi Dalib (R.A) cewa: –
“Na tamba yi mahaifi na, wato
Sayyadina Ali (R.A) a halin yana
halifa, na ce: – shin wane ne ya fi
kowa daraja cikin wannan al’umma
bayan Manzon Allah (S.A.W)? Sai
Sayyadina Ali (R.A) ya ce,
Sayyadina Abubakar (R.A) ne. Na
ce sai kuma wa? Sai Sayyadina Ali
(R.A) ya ce: – Sai Sayyadina Umar
(R.A). Sai na yi gudun kada na
sake tambayarsa ya ce: Sayyadina
Usman (R.A). Sai na yi sauri na ce:
– sai kuma kai ko? Sai ya: – ce a’a
ni dai mutum ne daga cikin
muslimai kawai”
Na biyar: – Ayar da Hadisin sun
nuna cewa ‘yan Aljannar suna da
yawa, Yan Shi`a kuwa da mutum
hudu ko shida kawai, suka yarda
daga cikin mutanen farko.
Na shida: – Duk wani alkawarin da
Allah ya yiwa wannan al’umma, da
bushara da Manzon Allah (S.A.W)
ya yi mata na samun rinjaye a kan
daulolin duniya kamar Farisa da
Rum, da daukakar da addini zai
samu da irin karfin da zai yi, duk
wadannan sun tabbata ne a
hannun Sahabbai da mabiya
tafarkin Sunna.
Domin tafarkin Shi’a bai taba
samun rinjaye ba, ballantana ya
jagoranci duniya.
Sahabbai ne da masu bin
tafarkinsu, suka yada wannan
Addini, suka kai shi mabullar rana
da mafadar ta.
Su ne suka yaki duk wani kafirci na
duniya, suka kawar da zalunci da
bautar wanin Allah, suka shinfida
adalci da gaskiya, tutar ‘yanci ta
kada a ko ina.
Su ne kuma suka daukaka kalmar
Tauhidi, tutar Musulunci ta daga.
10) Akwai wani lafazi na wannan
Hadisin da Manzon Allah (SAW) ya
ce: – “Al’umma ta ce”. A maimakon
Sahabbai na ne”
Wannan sai yake fassara abin da
kalmar sahabi take nufi, a daya
riwayar. Wato Hadisin yana
magana ne, a kan al’ummar
Musulmi baki daya.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce, Manzon
Allah (SAW) ya fada a Hadisin
cewa “sun gane ni, na gane su”
Sai mu ce: – akwai alamomi da
kowane Annabi, da al’ummarsa,
suke gane juna da su a ranar
Alkiyama. Kamar sofanen Sallah,
kamar yadda Hadisi ya tabbatar.
Kuma al’ummar kowane Annabi, a
kan ce musu, sahabbansa a
gamammiyar ma’ana, kamar yadda
ya gabata a Hadisin Ukashetu dan
Mihsan (R.A).
Banda wannan ya tabbata a Hadisi
cewa, farkon wadanda zasu sha
ruwa daga Tabkin Manzon Allah
(SAW) su ne, talakawan masu
hijira, wadanda suka bar
gidajensu, iyalansu da dukiyarsu
saboda Allah.
Kamar yadda Manzon Allah (SAW)
ya ce da mutanen Madina “Ku yi
hakuri a kan zaluncin da zaku gani
a bayana, har sai mun hadu da ku
a Tabki na”

6 responses to “DARASI NA GOMA SHA DAYA(11) A CIKIN LITTAFIN SHUBUHOHIN 'YAN SHI'AH(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)”
 1. Billy Avatar
  Billy

  To Allah ya rabamu da shi a

  1. Abubakar Sulaiman Avatar
   Abubakar Sulaiman

   Allah ya tsare mu daga shi’a.

 2. Murtala yusuf Avatar
  Murtala yusuf

  Allah yakaremana malam daga murtala yusuf barnawa kaduna

  1. jidda aminu Avatar

   amin ya allah.

 3. gazali jibril Aliyu Avatar
  gazali jibril Aliyu

  Allah ya ganar damu.

 4. Adamu Nafada Avatar
  Adamu Nafada

  Best wishes

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: