SHUBUHOHIN SHI’A A KAN HADISIN SAYYADINA UMAR (RA) NA BADA SHAWARAR HANA RUBUTA TAKARDA LOKACIN RASHIN LAFIYAR MANZON ALLAH (SAW). DA WARWARE SU DA DALILAI GAMSASSU(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa)

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Bismillahir Rahmanir Rahim
Darasinmu na yau zaiyi Magana
ne akan hadisin rubuta takarda: –
—-Shin wace takarda Manzon
Allah (S.A.W) zai rubuta ?
—–Rubutun wajibi ne ko
mustahabbi ko rubutu ne na
masalaha ?
—–Shin wa Manzon Allah (S.A.W)
yaso ya rubutawa takardar wasilci
——Shin Manzon Allah (S.A.W)
yayi wasiyya ga sayydina Ali (R.A)
SHUBUHOHIN SHI’A A KAN
HADISIN SAYYADINA UMAR (RA)
NA BADA SHAWARAR HANA
RUBUTA TAKARDA LOKACIN
RASHIN LAFIYAR MANZON
ALLAH (SAW). DA WARWARE SU
DA DALILAI GAMSASSU.
Daga cikin Shubuhar da ‘Yan Shi’a
suke yadawa a cikin al’umma
akwai Hadisin Abdullahi dan
Abbas (R.A), ya ce: – Lokacin da
rashin lafiyar Manzon Allah
(S.A.W) ta yi tsa nani sai ya ce: –
“ku kawomin abin rubutu na rubuta
muku wata takarda da baza ku
bata ba a bayana” Sai ra’a yin
sahabbai ya saba, wasu suka ce a
bashi takarda ya rubuta. Wasu
suka ce kada a wahalar da shi a
kyale shi tun da yana cikin rashin
lafiya. Sai Sayyadina Umar ya ce: –
Rashin lafiya ta yi tsa nani ga
Manzon Allah (S.A.W.) a tare da
mu akwai Littafin Allah ya isar
mana. Da maganganu suka yi
yawa sai Manzon Allah (S.A.W) ya
ce: – “Ku tashi ku kyale ni bai
kamata a dinga jayayya a gaban
Annabin Allah ba”
‘Yan Shi’a suna fakewa da wannan
Hadisin don su soki Sayyadina
Umar (R.A) da Sahabban da suke
da ra’a yin a kyale Manzon Allah
(S.A.W), kada a wahalar dashi da
yin rubutu tunda ya na cikin tsa
nanin rashin lafiya, a bangare
guda. A daya bangaren kuma
sukan yi da’awar cewa Manzon
Allah (S.A.W) zai rubuta wasiyyar
halifanci ne ga Sayyadina Ali (R.A)
amma wasu daga cikin Sahabbai
suka hana shi.
Jawabi a kan wannan Hadisi shi ne
ta fuskoki kamar haka: –
1) Cikin wannan Hadisin ba a
fayya ce abin da Manzon Allah
(S.A.W) zai rubuta ba. Da’awar
cewa zai rubuta wasiyya ga
Sayyadina Ali (R.A) tana bukatar
ingantaccen dalili. Tunda ko ba
komai akwai dalilai ingantattu
kuma tabbatattun Hadisai dake
nuna cewa Manzon Allah (S.A.W)
bai yiwasiyyar halifanci ga
Sayyadina Ali ba (R.A) kamar
yadda bayani zai zo nan gaba.
2) Yan Shi’a suna kawo riwayoyi
na karya wadanda suke nuni da
cewa Manzon Allah (S.A.W) tun a
Makka da gurare daban-daban ya
bayyana Sayyadina Ali (R.A) a
matsayin halifansa. Amma abin
mamaki sai ga ‘Yan Shi’a suna
Da’awar cewa wai Sayyadina
Umar (R.A) da wasu Sahabbai su
ne suka hana Manzon Allah
(S.A.W) ya rubutawa Sayyadina Ali
(R.A) wasiyya.
To a kan wannan da’awa dole ne a
samu dayan abubuwa guda biyu: –
Na daya: Ko dai Manzon Allah
(S.A.W.) bai taba ayyana
Sayyadina Ali (R.A) a matsayin
halifansa ba kafin rashin lafiyarsa
ta ajali. Sai ya zamo da’awar ‘yan
Shi’a cewa tuntuni Manzon Allah
(SAW) ya ayyana Sayyadina Ali
(RA) a matsayin halifa karya ce.
Na biyu: Ko kuma dama can
Manzon Allah (S.A.W) ya ayyana
Sayyadina Ali (RA) a matsayin
halifansa kamar yadda ‘Yan Shi’a
suke da’awa. To a nan rashin
rubutun wannan takarda ba zai
shafe wasiyyar da aka yi masa tun
da farko ba. Duk ta inda aka kalli
lamarin za a ga cewa akwai tufka
da warwara a cikin maganganun
‘Yan Shi’a.
3) Akwai kungiyoyin Shi’a daban-
daban da suke da’awar cewa na
su limamin Manzon Allah (S.A.W)
zai rubutawa wannan wasiyya ba
Sayyadina Ali (R.A) ba. Da’awar
wa ce kungiya daga cikinsu za a
karba?
4) Akwai dalilai tabbatattu kuma
ingantattu daga Sayyadina Ali
(R.A) da suke tabbatar da cewa
Manzon Allah (S.A.W.) bai
yiwasiyyar halifanci ga Sayyadina
Ali (R.A) ba, kuma bai kebance
Ahlu Al-Baiti da wani ilimi na
musamman ba.
Imam Al-Bukhari ya rawaito Hadisi
daga Abu Juhaifa (R.A.) cewa ya
tamba yi Sayyadina Ali (R.A) Shin
ku Ahlu Al-Baiti Manzon Allah
(S.A.W) yakebance ku da wani abu
ne na ilimi, wanda bai sanar da
ragowar al’umma ba? Sai
Sayyadina Ali (R.A) ya ce: na
rantse da Ubangjin da yake halitta,
yake fitar da kwaya daga
Zangarniya, Manzon Allah (S.A.W)
bai kebance mu da komai ba
wanda bai sanar da ragowar
al’umma shi ba. Sai dai Allah yana
fifita wanda yaga dama wajen
fahimtar Ma’anonin Alkur’ani’
A wata riwayar ta Ahmad dan
Hambal, Ashtar ne ya tamba yi
Sayyadina Ali (R.A). Shin Manzon
Allah (S.A.W) ya yi muku wasiyya
da wani abu ne? Sai Sayyadina Ali
(R.A) ya ce: Manzon Allah (S.A.W.)
bai mana wasiyya da komai ba .
A wata riwayar ta Imam Muslim
daga Abu Al-DDufail (R.A) ya ce:
Na kasance a gurin Sayyadina Ali
(R.A), sai wani mutum ya zo ya ce:
“Me Manzon Allah (S.A.W.)
yakebance ka da shi? Sai
Sayyadina Ali (R.A) ya yi fushi ya
ce: ya ya Manzon Allah (S.A.W.)
zai kebance ni da wani abu wanda
bai sanar da al’umma ba!
Imamu Al-Nawawi ya ce: a kan
wannan Hadisin “Wannan bayani
ne karara daga Sayyadina Ali (R.A)
dake ruguje karyar ‘Yan Shi’a ta
da’awar da suke yi cewa wai
Manzon Allah (S.A.W) ya
yiwasiyyar Halifanci ga Sayyadina
Ali (R.A) da wasiyyar wasu ilimai
da yakebance Ahlu Al-Baiti da shi”.
Ni kuma na ce Hadisin raddi ne a
kan ‘Sufaye, ‘yan koren Shi’a da
suke riya cewa akwai ilimi na boye,
suke kuma danganta Darikunsu
izuwa ga Sayyidina Ali da Ahlu Al-
Baiti. Sannnan raddi ne gare su da
suke dogara da mafarki da ire-
irensu wajen bautawa Allah da
ibadu sababbi, wadanda ba su da
tushe da asali.
Haka nan Imamu Bukhari ya fitar
da Hadisi Daga Abdullahi dan
Abbas (R.A) ya ce: – “Hakika
Sayyadina Ali (R.A) ya fito daga
gurin Manzon Allah (S.AW.)
lokacin Manzon Allah (S.A.W.)
yana cikin rashin lafiyar ajali. Sai
Sahabbai suka tambaye shi, ya
baban Hasan ya ya Manzon Allah
(S.A.W) ya wa yi gari? Sai ya ce: –
“ya wa yi gari da sauki cikin
godiyar Allah. Sai Abbas dan Abdu
Al-Muddalib (R.A) ya kama hannun
Sayyadina Ali (R.A) ya ce: da shi
wAllahi ni ina ganin Manzon Allah
(S.A.W) ba zai tashi daga wannan
rashin lafiyar ba, domin na kan
gane alamun ajali, a fuskar ‘ya’yan
Abdul Al-Muddalib. Mu je gurin
Manzon Allah (S.A.W.) mu
tambaye shi, shin waye zai karbi
lamarin halifanci a bayansa. Sai
Sayyadina Ali (R.A) ya ce: “Hakika
idan muka tamba yi Manzon Allah
(S.A.W.) Sai ya ce: ba mu bane. To
mutane ba za su taba yarda da mu
ba koda a gaba. Na Rantse da
Allah ba zan tambaye shi ba”
Wadannan Hadisai da ire-irensu
duk suna zama martani a kan
karaira yin ‘Yan Shi’a na cewa wai
Manzon Allah (S.A.W.) ya
yiwasiyyar halifanci ga Sayyadina
Ali (R.A) ko yakebance Ahlu Al–
Baiti da wani ilimi na boye, irin
da’awar da ta kutso kai cikin
Darikun Sufaye daga baya. Idan
‘yan Shi’a suka ce: wadannan
maganganu na Sayyadina Ali (R.A)
ya fade su ne a halin Takiyya wato
(Bayyana Sabanin abin dake cikin
Zuciya).
Sai mu ce: Sam ba haka lamarin
yake ba. Dalili kuwa shi ne Imamu
Al-Suyudi ya rawaito a littafinsa
Tarikhu Al-Khulafa daga Hasanu
Al-Basari cewa: “Lokacin da
Sayyadina Ali ya Shigo garin
Basra, wani mutum da ake kira da
Ibn Kawwa’i da Kai’su dan Abbad
sun tamabaye shi, ba mu labarin
wannan fitowar taka. Ga shi kai ne
shugaba amma ka bar al’ummar
musulmi suna kashe juna. Shin
akwai wata wasiyya da Manzon
Allah (S.A.W) ya yi maka ne?
Sanar da mu lallai kai amintacce
ne kuma abin amincewa kan duk
abin da zaka fada.
Sai Sayyadina Ali (R.A) ya ce: –
maganar cewa Manzon Allah
(S.A.W) ya yi min wasiyya babu ita.
WAllahi ni ne farkon wanda na
bada gaskiya da shi, ba zan kuma
kasance farkon wanda zai masa
karya ba.
Da a ce Manzon Allah (S.A.W.) ya
yi min wasiyya ta halifanci, da ba
zan taba kyale wani mutum daga
Banu Taimin ba (Abubakar R.A) ko
wani mutum daga bani Adiyu ba
(Umar R.A) su hau kan minbarin
Manzon Allah (S.A.W.) a matsayin
halifofinsa ba. Da kuma na yake su
da duk abin da zan iya wajen
karbar hakki na ko da ni kadai ne.”
Wannan shi yake karyata maganar
‘yan Shi’a cewa wai Sayyadina Ali
(R.A) yana Takiyya ko ya kasa
karbar hakkinsa ne saboda babu
yadda zai yi.
Wani abu da yake tabbatar da
wannan maganar, yake kuma
ruguje da’awar ‘yan Shi’a ta wasilci
shi ne – ya zo a Nahaju Al-Balaga
cewa lokacin da mutane suka nemi
Sayyadina Ali (R.A) ya zama halifa
bayan kisan gillar da aka yiwa
Sayyadina Usman (R.A). Sai ya ce:
“Ku kyale ni a matsayin mabiyi ku
nemi wani daban ba ni ba ya zame
muku halifa…. Ku rabu da ni na
zamo mabiyi, hakika zan zamo
mafi ji da biyayya ga duk wanda
kuka zaba a matsayin halifa.
Saboda na zamo mataimaki mai
bayar da shawara shi ya fiye muku
fiye da a ce na zamo muku halifa”
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita
ce: – ina Da’awar da ‘Yan Shi’a
suke yi cewa Manzon Allah
(S.A.W.) ya yiwasiyya ta halifanci
ga Sayyadina Ali?
Me yasa Sayyadina Ali (R.A) ya
zabi da ya zamo mabiyi ba halifa
ba? Ina maganar cewa halifancin
limaman Shi’a goma sha biyu zabi
ne daga Allah kamar yadda yake
zabar Annabawa, kamar yadda
wani Malamin Shi’a mai suna
Muhammad Husaini ya Fada a
littafinsa Al-Shi’a Wa-Usuluha?
Shin a cikin Annabawan Allah
akwai wanda mutane suka hadu
suka zabe shi a matsayin Annabi
ko ya yi Takiyya ya kasa bayyana
gaskiya? Ba ma Annabawa ba,
shin Sayyadina Abubakar da Umar
(RA) sun taba yin Takiyya tun daga
rayuwar su ta Makkah har suka
koma ga Allah?
5). Duk Malamai sun hadu a kan
cewa wannan rubutu da Manzon
Allah (S.A.W.) ya so ya yi, ba abu
ne na wajibi ko na mustahabbi ba.
Abu ne na zabi da masalaha. Shi
yasa lokacin da Sayyadina Umar
(R.A.) ya ce: Alkur’ani ya ishe mu,
Manzon Allah (S.A.W.) bai yi masa
inkari ba.
6) Ba wannan ne karo na farko da
sahabbai suka saba a kan wata
shawara da Manzon Allah (S.A.W.)
ya nema ba. A lokuta da dama irin
wannan ya kan faru tsakaninsu da
Manzon Allah (S.A.W.) Sau tari
idan ya yi nufin yin wani abu ya
kan shawarce su. Kuma sukan
bada shawarwari mabambanta
juna. Manzon Allah (S.A.W.) ya
kan yi haka ne cikin abin da bai
zama dole ba, yana mai aiki da
Fadin Ubangiji (S.W.T.) “Kuma ka
yi shawara da su (Sahabbai) cikin
lamarin Addini. Amma idan ka
yanke aiwatar da wani abu, to sai
ka dogara ga Allah ka aiwatar da
shi ba ja da baya.” Don haka
Manzon Allah (S.A.W.) ya kan fasa
aikata wani abu don masalahar
Al’umma, ko don gudun kada ya
aikata abin a mayar da shi wajibi.
Misali a kan haka shi ne janyewar
da Manzon Allah (S.A.W.) ya yi na
ayyana daren Lailaitul Kadari,
yabar al’umma da su neme shi a
goman karshe na watan
Ramadana.
Abin da yake dada fito da abin da
muka ambata a fili shi ne abin da
ya faru a lokacin yakin Uhud.
Bayan Manzon Allah (SAW) ya yi
shawara da Sahabbai, kan a fita
wajen gari a tari kafirai ko a zauna
a yake su ta cikin ganuwar Madina.
Wasu suka ce a fita a tare su.
Wasu kuma suka ce a yake su ta
cikin ganuwar Madina. Amma
bayan da Manzon Allah (S.A.W.)
ya sanya kayan yaki bai saurari
ra’a yin da Sahabbai suka hadu a
kai daga baya ba, na zama a cikin
gari, sai ya ce: “magana ta kare
saboda na riga na sanya kayan
yaki.”
Wani misali shi ne na abin da ya
faru lokacin da Nana Aisha da
Hafsa (R.A) suka ba shi shawarar
kada ya sanya Sayyadina
Abubakar (R.A) a matsayin
limamin da zai wa mutane Sallah.
Saboda Sayyadina Abubakar (R.A)
yana da sassanyar zuciya. Sai
Manzon Allah (S.A.W.) ya ce: – ku
ce da Abubakar ya yiwa mutane
Sallah. Suka sake Fadar
maganarsu ta farko, shi kuma sai
ya kara nanata musu irin abin da
ya fada a farko. A karshe yake
cewa da su: – “ku fa mata mutanen
Annabi Yusuf (A.S) ne”.
7) Akwai Hadisi tabbatacce da ya
bayyana a fili cewa: – Manzon Allah
(S.A.W.) ya yi nufin rubuta
wasiyyar Halifanci ne ga
Sayyadina Abubakar (R.A), don
gudun kada wani ya ce: shi ya fi
cancanta ko wani ya yi burin
samun shugabanci, a samu sabani
da rikici cikin al’umma. Kamar
yadda Imamul Bukhari ya rawaito
Hadisi daga Nana Aisha (R.A) ta
ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
-“Ina so a tura gurin Abubakar da
dansa Abdurrahaman su zo na
rubutawa Abubakar wasiyyar
(halifanci) don kada wani ya ce: shi
yafi cancanta ko ya yi burin
Halifanci. Allah da Manzonsa da
muminai kuwa ba za su yarda da
kowa ba sai Abubakar” . A wata
riwayar ta Muslim Manzon Allah
(S.A.W) cewa ya yi da Nana Aisha:
– “ki yi min kiran Abubakar na
rubuta masa wasiyya ta Halifanci
domin ina jin tsoron wani mai buri
ya yi burin (halifanci). Allah kuma
da Muminai ba zasu yarda da
kowa ba sai Abubakar”
Malamai suka ce: Manzon Allah
(S.A.W.) ya yi nufin ya rubutawa
Abubakar wasiyya ne, don
karfafawa ga abin da ya sha nuni
da shi na halifancin Sayyadina
Abubakar a bayansa. Ganin
Sahabbai sun yi sabani kan
wannan rubutun da ya so ya yi a
lokacin rashin lafiyarsa, sai ya
fasa. Dalili kuwa shi ne wasu za su
iya cewa Manzon Allah (S.A.W.) ya
rubuta takardar ne a halin rashin
lafiya su haifar da shakku da
sabani a kan ingancinta.
Hikimar kin rubutun kuwa sai ta
bayyana, saboda ba’a samu wani
Sabani ba a lokacin Sayyadina
Abubakar (R.A) ya zama halifa. Sai
sabanin da ba a izina da shi.
Don haka dukkan malaman Sunna
sun hadu a kan cewa Manzon
Allah (S.A.W.) bai yiwasiyya ga
Sayyadina Ali (R.A.) ba, a zahiri ko
a boye. Amma malamai sun yi
Sabani a kan Sayyadina Abubakar
(R.A), shin Manzon Allah (S.A.W)
ya yi masa wasiyya ta zahiri ne ko
ta hanyar nuni?
Wasu malaman suka ce Manzon
Allah (S.A.W.) bai yi masa wasiyya
ta zahiri ba sai ta hanyar nuni.
Wasu kuma suka ce Manzon Allah
(S.A.W.) ya yi masa wasiyya ne ta
zahiri.
Wadanda suka ce Manzon Allah
(S.A.W.) bai yiwa Sayyadina
Abubakar wasiyya ta zahiri ba,
suna dogara ne da maganar
Sayyadina Umar (R.A.) lokacin da
aka bukaci da ya sanya halifa a
bayansa sai ya ce: – “Idan na
yiwasiyya to wanda ya fi ni ya
yiwasiyya yana nufin Sayyadina
Abubakar (R.A). Idan kuma ban yi
ba, to wanda ya fi ni ma bai yi ba.
Yana nufin Manzon Allah (S.A.W)”
Amma wadanda suka ce Manzon
Allah (S.A.W.) ya yiwa Sayyadina
Abubakar (R.A.) wasiyya ta zahiri,
suna ba da amsa ne da cewa: –
Abin da Sayyadina Umar (R.A)
yake nufi shi ne Manzon Allah
(S.A.W.) bai yiwasiyya ga
Sayyadina Abubakar (R.A) ba ne a
rubuce amma ya fada da baki.
Wani abu da ya kamata a sani shi
ne – Kungiyoyin Shi’a kansu sun yi
sabani a kan cewa shin Manzon
Allah (S.A.W.) ya yiwasiyya ga
Sayyadina Ali (R.A) ne a zahiri ko
ta hanyar nuni?
Kungiyar Shi’a Imamiyya suna
da’awar cewa Manzon Allah
(S.A.W.) ya yiwa Sayyadina Ali
(R.A) wasiyya ne ta zahiri. Amma
kungiyar Shi’a Jarudiyya da
Zaidiyya suna ganin cewa ya yi
masa wasiyya ne ta hanyar nuni .
Dukkan wadannan ra’ayoyin na
‘yan Shi’a kuwa, ba su da tushe
balle asali. Amma mun hakaitosu
ne kawai don mai karatu ya san
cewa kungiyoyin Shi’a ba su hadu
a kan wata akida guda daya ba,
har ta asalin akidarsu wato Imama.
(8) Kudirce cewa Manzon Allah
(S.A.W) ya fasa rubuta wani abu
da zai hana mutane ba ce wa a
bayansa, ya bar mutane da Al-
Kur’ani da Hadisi kawai, babban
suka ne da Allah da Manzonsa.
Sannan kuma suka ne da shi
kansa Alkur’anin. Saboda abin da
wannan mummunar akida ta ‘yan
Shi’a take nunawa shi ne Allah da
ManzonSa sun kyale al’umma a
cikin bata, kuma Alkur’ani ba littafi
ne na shiriya ba.
Idan ‘Yan Shi’a suka ce: me yasa
Sahabbai suka ki bin Umarnin
Manzon Allah (S.A.W.) da ya ce: su
kawo takarda ya yi musu rubutu?
Sai mu ce: amsa a kan wannan ta
gabata. Wani kari a kan haka shi
ne – Sahabbai ba su fahimci
wannan umarnin a matsayin
umarni na dole ba. Misalin irin
wannan shi ne -Sayyadina Ali
(R.A.) bai goge sunan Manzon
Allah (S.A.W.) ba, lokacin da ya
umarce shi ya goge sunansa a ya
yin sulhun Hudaibiyya saboda bai
fahimci umarnin a umarni na dole
ba.
Kamar yadda Sayyadina Ali (R.A)
da Nana Fadima (R.A) ba su bi
umarnin Manzon Allah (S.A.W.) ba,
lokacin da ya ce: da su, su tashi su
yi Sallah. Sai suka ce da shi
rayukansu yana hannnun Allah duk
sanda yaga dama ya tashe su sai
ya tashe su. Da Manzon Allah
(S.A.W.) ya ji wannan maganar ta
su sai ya fito daga gurinsu yana
cewa: – “Lallai dan Adam ya fi
komai jayayya daga cikin halittun
Allah” Don haka idan a wancan
gurin Sahabbai sun yi jayayya a
gaban Manzon Allah (S.A.W.) a
kan umarnin da ya yi, to a nan
gurin ma Sayyadina Ali (R.A) da
Nana Fadima sun yi jayayya da
umarnin Manzon Allah (S.A.W.)
kuma duk ya kyale su, saboda ya
san umarnin da ya yi musu ba na
dole ba ne. .
9) Wani abu mai mahinmanci da ya
kamata a sani shi ne . Manzon
Allah (S.A.W.) ya ci gaba da
rayuwa bayan faruwar wannan
al’amarin na neman a ba shi
takarda, don yin rubutu har izuwa
safiyar ranar Litinin din da ya koma
ga Allah. Ba wai a wannan rana ta
Alhamis ya rasu ba. Saboda shi
wannan lamari na rubutun takarda
ya faru ne ranar Alhamis kamar
yadda ya tabbata daga Abdullahi
dan Abbas (R.A). Shi kuwa
Manzon Allah (SAW) ya rasu ne da
hantsin ranar Litinin. Don haka
bayan faruwar wannan lamarin,
Manzon Allah (S.A.W.) ya ci gaba
da rayuwa har kwana hudu. Kuma
a tsakanin wannan kwanaki ya
bayyanar da hukunce-hukunce
masu yawa, tare da yin wasiyyoyi
daban-daban, wadanda ba su kai
hadari ko muhimmancin halifanci
ba. Kamar wasiyyar kulawa da
mata da fitar da Yahudu da Nasara
daga yankunan Larabawa
Hasali ma dai duk wani abu da
Manzon Allah (S.A.W.) yake gudun
faruwarsa na sabani a cikin
al’ummarsa, to bai koma ga Allah
ba har sai da yaga tabbacin rashin
faruwarsa.
Domin ya tabbata a cikin Bukhari
daga Hadisin Anas (R.A) cewa:
“Musulmai suna cikin Sallar
Asubahi ta ranar litinin, (Wacce
Manzon Allah (S.A.W.) ya rasu a
cikinta ba su yi zato ba, sai suka ga
Manzon Allah (S.A.W.) ya bude
labulan tagar dakin Nana Aisha
(R.A). Sai ya kalle su a halin
dukkaninsu sun yi sawu suna
Sallah a bayan Sayyadina
Abubakar (R.A). Sai ya yi
murmushi da dariya. Sayyadina
Anas dan Malik (R.A) ya ce, har
mutane sun kusa rudewa saboda
farin cikin ganin Manzon Allah
(S.A.W). Sai Manzon Allah
(S.A.W.) ya yi musu nuni da su ci
gaba da Sallarsu. Sannan ya saki
labulan dakin kuma ya rasu, a
hantsin wannan ranar…” .
Saboda haka, Manzon Allah
(S.A.W) ya rasu ne yana mai farin
ciki da yarda da Sahabbansa,
bayan ya gansu kansu a hade
yake suna Sallah a bayan
halifansa Sayyadina Abubakar
(R.A). Suma Sahabbai suna masu
farin ciki da yarda da Annabinsu
kan tsarin da ya dora su na yin
biyayya ga halifansa. Sabanin abin
da ‘Yan Shi’a suke yadawa na
karaira yi da kage wai cewa kan
sahabbai ba a hade yake ba

7 responses to “SHUBUHOHIN SHI’A A KAN HADISIN SAYYADINA UMAR (RA) NA BADA SHAWARAR HANA RUBUTA TAKARDA LOKACIN RASHIN LAFIYAR MANZON ALLAH (SAW). DA WARWARE SU DA DALILAI GAMSASSU(Mal. Aminu Ibrahim Daurawa)”
  1. Mohammed Auwal Garba Avatar
    Mohammed Auwal Garba

    Mal. Daurawa yaya zakayi da wadannan hadisai, wadda suka tabbatar da wasiycin MANZON ALLAH KAN ALIYU NE KHALIFA BAYANSA. 1. Al hakim alnaysaburi, almustadrak ala al-sahihayan(Beirot) Vol.3, pp.109.110,133,148,533. 2.Ibn hajar al-asqalani, Fath al bari bi sharh sahih al bukhari(Beirot) Vol.7 p61. 3.Al suyuti, al-durr al-manthur Vol.2 p259 & 298. 4.Ibn kathir, tafsir QUR’AN AL AZIM (Beirot) Vol.2 p14 5.Ibn kathir, al-bidayah wal nihaya.(cairo,1932) Vol.7 p340 Vol.5 p213.

  2. JM Avatar

    hmmmm wannan duk tatsuniya ce dan ba haka bane ya faru

    1. Mohammed Auwal Garba Avatar
      Mohammed Auwal Garba

      Amma mallam menene matsayin wadda ya karyata hadisi mutawatur?

  3. MANZON ALLAH (SAWA) ALLAH (S) YA SANYASHI RAHAMANE TA TALIKAI KUMA BAYA MAGANA HACE WAHAYINE. TO YAYA ZA’AYI YACE KU KAWO ABIN RUBUTAWA IN RUTAMUKU ABINDA BAZAKU KAUCE HANYABA WANI HAR YAYI INKARIN UMARNINSA. YANZU ANNABI MUHAMMADU (SAWA) AKA AIKO DA ADDININ MUSULNCI KO UMAR . SANNAN MAGANA AKAN WASIYAR ANNABI YAYI WASIYA WAZAI GAJESHI, YAYA AKAYI ABUBUKAR YAYI WASIYCI UMAR YA GAJESHI KANA MUFIN ABUBAKAR YAFI ANNABI KAIFIN TUNANI DA SANIN YA KAMATA. KUMA WANE ANNABINE YAZO YABAR AL’UMMARSA BAIYI MUSU NUNI GA WADDA ZASUBASHI A BAYANSABA.

    1. Nura Tahir Abu A'isha Avatar
      Nura Tahir Abu A’isha

      Maganar ka ta cewa Manzon Allah S.A.W.W rahama ne wannan haka yake kuma baya magana a shari’ance face wahayi ku hankalin ku ya kasa sawa ku gane cewa irin wannan umurni shine Annabi S.A.W.W yaba Sayyidi Ali R.A a Sulhun Hudaibiyya amma duk duniya babu wanda ya isa ya ce Sayyidi Ali yaki bin umarnin shugaba S.A.W.W kuma shi Sayyidi Ali shi kadai aka bawa wancan umarni anan kuwa cikin dalibansa S.A.W.W ya ke kuma su duka yake bawa umarni ba wai Sayyidi umar da kuka raina ba cikin su harda shi Sayyidi Alin

  4. Sadiq Ahmad Avatar

    Allah yakyauta

Leave a Reply

Latest updates
Categories