DARASI NA GOMA SHA BIYU (12)SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI’A(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)

Da ikon Allah yau zamu tashi sabon darasi wato darasi na goma sha biyu. Malam Bismillah: –
SHIN WAYE YA KASHE SAYYADINA HUSAINI (RA), SHI’A KO AHLU-AL-SUNNAH?
Shubuha ta tara da ‘Yan Shi’a masu limamai goma sha biyu suke yadawa, kuma tana daga mafi girman shubuhohinsu da suke amfani da ita wajen yaudarar musulmi da neman goyan bayansu ita ce, kissar kashe Sayyadina Husaini dan Aliyu dan Abi Dalib (R.A).
‘Yan Shi’a masu limamamai goma sha biyu, sun kirkiro bikin bakin ciki na tunawa da wannan ranar, wanda suke yi duk ranar goma ga watan Muharram.
Su kan sanya bakaken kaya, su fito suna dukan jikinsu, a wasu guraren ma har zubar da jininsu suke yi, wai don kishin Sayyadina Husaini (R.A) da tunawa da abin da ya same shi. Sannan su karanta kissar yadda aka kashe shi su hakaito maganganu da yawa na karya, a kan hakikanin abin da ya faru.
Daga cikin abubuwan da suke hakaitowa akwai abubuwa kamar haka: –
i. An yi ruwan jini daga sama lokacin kashe Sayyadina Husaini (R.A).
ii. Duk wani dutse da aka daga ana ganin jini a wannan ranar.
iii. Sama ta yi wani irin ja wanda ba’a taba ganin irinsa ba, tsahon wani lokaci.
Daga nan kuma sai su kawo labarin cewa, bayan an kashe Sayyadina Husaini (R.A) da wadanda suke tare da shi, an ciccire kawunansu aka dinga kewayawa da su cikin gari.
Shi kuwa kan Sayyadina Husaini (R.A) sai da aka kai shi gaban Yazidu dan Mu’awiya, ya dinga zungurinsa da sanda.
Wadanda suka yi saura kuwa, aka daddauresu da sasari aka dinga kewayawa da su a cikin gari. Matansu kuma aka mai da su tamkar ba yi.
Sannan sai su hakaito tarihin Yazidu, su siffanta shi da shan giya da laifuka iri-iri. Suna la’antarsa da iyayensa, suna nuna cewa: – Yazid da Banu Umayya sun kashe Husaini (R.A) ne don daukar fansar abin da Manzon Allah (S.A.W) ya yiwa kafiran Makka a yakin Badar.
Sannan su hakaito cewa, Yazidu yasa an kashe mutane dubbai a Madina, wanda saboda yawan jini da yake zuba a wannan lokacin, sai da Masallacin Manzon Allah (S.A.W.) ya jike da jini.
Su kan kara da cewa, Yazidu ya kona Ka’aba har wani bangarenta ya ruguje.
Su kan fake da cewa Imam Ahmad dan Hambal, yana daga cikin masu la’antar Yazidu.
Jawabi a kan mas’alar kashe Sayyadina Husaini (R.A) shi ne ta fuskoki kamar haka: –
1. Da farko dai zamu ce Innalillahi Wa’inna ilaihi raji’un! Allah ya karbi shahadar Husaini (RA), ya girmama ladansa. Amma mafiya yawan hikayoyin da ake kawowa na abin da ya faru ranar kashe Sayyadina Husaini (R.A), hikayoyi ne na karya marasa tushe da asali.
Babu wani Malami daga Malaman Sunna, da ya yarda da kashe Sayyadina Husaini (R.A), bari ma dai, dukkan Malaman Sunna sun hadu a kan cewa kashe shi, zalunci ne da ta’addanci. Kamar yadda suka hadu a kan cewa, kashe Sayyadina Umar (R.A) da Usman (R.A) da Aliyu (R.A) zalunci ne da ta’addanci.
3. Me ya sa ‘Yan Shi’a suke murna da farin ciki, kan kashe Sayyadina Umar da Usman (R.A) ta yadda har biki suke yi na nuna farin cikin ranar tunawa da kashe su. Suna Addu’a ta alheri ga wandanda suka kashe su?
4. Zalunci da ta’addacin dake cikin kashe Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A) yafi muni da fitowa fili, fiye da zaluncin dake cikin kashe Sayyadina Husaini (R.A). Duk da cewa dukkanin kisan zalunci ne da ta’addaci.
Za a gane wannan duba da dalilai kamar haka: –
Na daya: – Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A) su ne Halifofin da Jama’a suka yi musu mubaya’a, shi kuwa Sayyadina Husaini (R.A) bai hau kan halifanci ba. Kashe shugaba kuwa yafi hadari da jefa al’umma cikin fitina, fiye da kashe wanda ba shugaba ba. Domin abu ne sananne fitintunan da suke faruwa, tsakanin al’ummar musulmi tun daga da, har izuwa yanzu suna da alaka da kisan da aka yiwa farkon shugaban musulmi wato Uthman dan Affan (RA).
Na biyu: – Sayyadina Umar da Usman (R.A) har cikin Madina aka zo a kashe su. Shi Sayyadina Umar (R.A) an kashe shi ne yana jagorantar mutane Sallah, a cikin Masallacin Manzon Allah (S.A.W).
Shi kuma Sayyadina Usman (R.A) an kashe shi ne a cikin gidansa, bayan an yiwa gidan kawanya aka hana shi fita dai-dai da Sallah wajen wata daya. Daga baya aka haura katangar gidansa, aka yanka shi yana karatun Alkur’ani, yana Azumi.
Shi kuwa Sayyadina Ali (R.A) an kashe shi ne a garin Kufa, yana hanyarsa ta zuwa masallaci domin yin sallar Asuba.
Sayyadina Husaini (S.A.W) kuwa babu wanda ya biyo shi inda yake ya kashe shi.
Na uku: – Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A) ba su nemi shugabanci a gurin kowa ba, hasali ma su ne shuwagabanni a lokacin da aka kashe su.
Sayyadina Husaini (R.A) kuwa an kashe shi ne a lokacin da ya tafi Kufa don a yi masa mubaya’a ta Halifanci.
Shi yasa dukkan al’umma suka hadu a kan cewa, kashe Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A) zalunci ne in ban da wadanda ba’a dogara da sabaninsu.
Amma al’umma sun yi sabani a kan kashe Sayyadina Husaini (R.A).
Wasu suka ce, kisan da a kai masa daidai ne, kamar kungiyar Nasibiyya da Marwaniyya.
Suna masu da’awarsu cewa Sayyadina Husaini (R.A), ya fito ne don ya karbi mulki, ya raba kan jama’a. Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: – “Wanda duk ya zo gurinku a halin kuna da shugabanku, da ku ka yi masa mubaya’a, yana so ya raba kanku to ku kashe shi”
Wasu suka ce: an kashe shi ne, kisa na ta’addanci da zalunci, saboda daman shi ne shugaban da ya wajaba al’umma su yiwa mubaya’a da nassin Alkur’ani da Hadisi. Don haka, ya fita ne domin karbar hakkinsa.
Wannan shi ne ra’a yin mafiya yawa daga kungiyoyin Shi’a.
Wasu suka ce: an kashe shi ne kisan ta’addanci da zalunci. Amma ba shi ne shugaban da al’umma suka yiwa mubaya’a ba. Kuma ba dan tawaye ba ne.
Wannan shi ne ra’a yin malaman Sunna. Kuma shi ne mafi inganci saboda dalilai kamar haka: –
Na daya: – Hadisan da suka yi umarni da a kashe wanda ya yi bore, ba zai shafi Sayyadina Husaini (R.A) ba. Saboda tun da farko, bai fita da nufin yin bore ba.
Na biyu: – Bayan ta bayyana cewa, mutanen Irak sun yaudari Sayyadina Husaini (R.A) ne, ya yi kokarin su ba shi dama ya komo Madina ko ya tafi Sham gurin Yazidu ko ya tafi wani gari daga cikin garuruwan musulmai.
Mutanen Irak suka hana shi ko daya daga cikin wadannan abubuwa da ya nema.
Suka ce: sai dai in ya yarda su kama shi a matsayin fursunan yaki, shi kuma ya ce: ko alama. A kan haka har yaki ya faru tsakaninsu.
Na uku: – Wani gama gari ma, wanda bai kai darajar Sayyadina Husaini (R.A.) ba. Idan ya nemi da a kyale shi, ya janye daga abin da ya fito saboda shi, to dole ne a kyale shi, ballantana Sayyadina Husaini (R.A.) jikan Manzon Allah (S.A.W) dan Nana Fadima (R.A.) dan Sayyadina Aliyu (R.A.) zakin Allah.
Na hudu: – Sayyadina Husaini (R.A) bai kira yi kowa izuwa bore da tawaye ba, bai kuma yi da’awar shi ne shugaba ba kamar yadda ‘Yan Shi’a suke riyawa. Bari dai ya ta fi garin Kufa ne don masalahar al’umma. Saboda mutanen garin sun rubuto masa wasiku suna masu da’awar cewa, ba su da shugaba, don haka ya zo ya shugabance su. Shi kuma ya kalli masalahar zuwa ya shugabance su, saboda zaman al’umma babu shugaba babbar matsala ce.
Na biyar: – Shubuhar dake cikin kashe Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A) ta fi rauni fiye da shubuhar dake cikin kashe Sayyadina Husaini (R.A).
Idan `Yan Shi`a suka ce suna yin bikin bakin ciki na tunawa da ranar kashe Sayyadina Husaini (R.A.) ne, saboda jikan Manzon Allah (S.A.W) ne.
Sai mu ce: ba Sayyadina Husaini (R.A) kadai aka taba kashewa ba daga cikin jikokin Manzon Allah (S.A.W).
Idan gaske ne `Yan Shi’a suna bakin ciki ne don an zubar da jinin Sayyadina Husaini (R.A.), to me yasa basa tuna ranakun da aka zubar da jina nan da suka fi na Sayyadina Husaini (R.A.) daraja a haduwar Ahlu Al-Sunna da Shi’a.
Domin an kashe Annabawan Allah da yawa, wasu kuma an zubar musu da jininsu a lokuta daban-daban.
Me yasa `Yan Shi’a basa tunawa da wadannan ranakun?
Sau nawa aka zubar da jinin Manzon Allah (S.A.W) da Sahabbansa, tun a Makka da Da’if da Badar da Uhud da guraren yaki daban-daban?
Me yasa `Yan Shi’a basa tunawa da wannan? Ko jinin Sayyadina Husaini (R.A) ya fi na Manzon Allah (S.A.W) ne?
Idan `Yan Shi’a suka ce: Shi Manzon Allah (S.A.W) ba’a kashe shi ba. Ragowar Sahabbansa kuwa ba Ahlu Al-Baiti ba ne?
Sai mu ce: Ahlu Al-Baiti nawa aka kashe amma `Yan Shi’a basa tuna ranar da aka kashe su?
Misali: – An kashe Ubaidullahi dan Harith dan Abdul Al-Muddalib (R.A) a Badar.
An kashe Sayyadina Hamza dan Abdul Al-Muddalib (R.A), shugaban shahidai a Uhud.
An kashe Ja’afar dan Abi Dalib (R.A), ma’abocin fuka-fukai guda biyu a yakin Mu’atata.
Shi kansa Sayyadina Ali (R.A) kashe shi aka yi a Kufa. Kamar yadda aka kashe Sayyadina Hasan dan Ali (R.A) dan uwan Sayyadina Husaini (R.A), ta hanyar guba.
Me ya sa `Yan Shi’a basa tuna, ranar kashe wadannan shugabanni na Ahlu Al-Baiti? Ko jinin Sayyadina Husaini (R.A) ya fi na wadannan ne?
6) Duk cikin Sahabbai da Tabi’ai na gari da suka rage, lokacin kashe Sayyadina Husaini (R.A) babu wanda bai yi inkarin kisan da a kai masa ba, kuma duk cikin wadanda suka kashe Sayyadina Husaini (R.A) babu Sahabi ko daya ko wani daga cikin tabi’ai na gari. Bari ma dai, dukkannin wadanda suka kashe shi ‘Yan Shi’a ne masu da’awar son Ahlu Al-Baiti.
Hasali ma Ubaidullahi dan Ziyad gwamnan Irak, wanda ya turo sojojin da suka kashe Sayyadina Husaini (R.A) yana daga cikin gwamnonin da Sayyadina Ali (R.A) ya nada tun a lokacin halifancinsa.
Banda wannan ma, wadanda suka kashe Sayyadina Husaini (RA) kai tsaye su ne: –
Na daya: – Shamir dan Zil-Jaushan.
Na biyu: – Hussain dan Numair.
Na uku: – Zur’atu dan Sharik.
Na hudu: – Sinan dan Anas dan Amr.
Na biyar: – Malik dan Nusair.
Wadannan kuwa dukkanninsu ‘Yan Shi’a ne
7) Idan ‘Yan Shi’a sun kafa hujja da cewa, dalilai sun tabbatar da zaluncin Sayyadina Hussain (R.A).
Sai mu ce: hakama dalilai sun tabbatar da zaluncin kashe Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A).
Misali a nan shi ne Hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: “Wata rana Manzon Allah (S.A.W) ya ambaci wata fitina da zata faru”. A dai dai wannan lokacin da yake wannan maganar wani mutum ya zo wucewa.
Sa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Za’a kashe wannan mutumin mai wucewar a lokacin wannan fitinar, kisa na zalunci”
Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: “Sai na duba don na ga ko wanene wannan mutumin mai wucewa. Sai na ga Usman dan Affan ne.
Idan ‘Yan Shi’a sun kafa hujja da cewa, dalilai sun tabbatar da zaluncin Sayyadina Hussain (R.A).
Sai mu ce: hakama dalilai sun tabbatar da zaluncin kashe Sayyadina Umar, Usman da Ali (R.A).
Misali a nan shi ne Hadisi ya tabbata daga Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: “Wata rana Manzon Allah (S.A.W) ya ambaci wata fitina da zata faru”. A dai dai wannan lokacin da yake wannan maganar wani mutum ya zo wucewa.
Sa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Za’a kashe wannan mutumin mai wucewar a lokacin wannan fitinar, kisa na zalunci”
Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: “Sai na duba don na ga ko wanene wannan mutumin mai wucewa. Sai na ga Usman dan Affan ne.”
8) Maganar cewa an kai kan Sayyadina Husaini (R.A), gaban Yazid dan Mu’awiya, har ya dinga zungurinsa da sanda, bata tabbata ba.
Maganar da ta tabbata ita ce: an kai kan Sayyadina Husaini (R.A) ne, gaban Ubaidullahi dan Ziyad, kamar yadda ya zo a cikin Bukhari daga Anas dan Malik (R.A) cewa: “An kawo kan Sayyadina Husaini dan Ali (R.A) gurin Ubaidullahi dan Ziyad (Gwamnan Iraki) aka sanya shi a cikin wata tasa, sai ya dinga zungurinsa da sanda, yana fadar irin kyansa.
Sai Anas dan Malik (R.A) ya ce: – Husaini (R.A) ya kasance daga mafi kama da Manzon Allah (S.A.W).
A wata riwayar ta Dabarani daga Zaid dan Arkam (R.A) cewa ya yi: – “Sai na ce dauke sandarka, ka daina zungurinsa, na ga bakin Manzon Allah (S.A.W) yana sumbatar wannan kan.”
A kan wannan Sheikhul Islam bn Taimiyya yake cewa: –
“Hakika an rawaito da wani Isnadi, wanda ba shi da asali cewa: – an kai kan Sayyadina Husaini (R.A) gurin Yazidu, har ya dinga zungurin kan da sanda. Tare da cewa wannan maganar Malaman Hadisi sun karyata ta, a cikin Hadisin ma akwai abin dake nuna cewa maganar an kai, kan Sayyadina Husaini (R.A) gaban Yazidu karya ne.
Domin Sahabban da aka yi abin a gabansu, ba su kasance a kasar Sham ba, sun kasance ne a kasar Iraki.
Abin da Malamai da yawa suka rawaito ma shi ne – Yazidu bai yi umarni da a kashe Husaini (R.A) ba, kuma ba shi da wata bukata cikin kashe shi, abin da ya fi so ma shi ne , ya girmama Sayyadina Husaini (R.A) ya kuma mutunta shi, kamar yadda Babansa Mu’awiyya (R.A) ya umarce shi. Don haka a lokacin da Sayyadina Husaini (R.A) ya zo Iraki ya fahimci cewa lallai mutanen Iraki, sun yaudare shi, kuma ba zasu taimake shi ba, sai ya nemi da su kyale shi ya tafi gurin Yazidu kasar Sham, ko ya koma gida ko ya tafi wani garin.
Sai mutanen Iraki suka ki yarda da abin da Sayyadina Husaini ya nema, suka ce lallai sai dai, idan ya yarda su kama shi a matsayin fursunan yaki, a kan haka suka yake shi, har suka kashe shi, ya yi Shahada suna masu zaluntarsa.
Kuma Malamai da yawa sun fada cewa: – Lokacin da labari ya je gurin Yazidu da iyalansa cewa an kashe Sayyadina Husaini (R.A), sun yi matukar bakin ciki, suka fashe da kuka sakamakon jin hakan.
A wannan lokaci Yazid ya ce: – “Allah Ya la’anci dan Murjanatu wato Ubaidullahi dan Ziyad na rantse da Allah da a ce Husaini (R.A) dan uwansa ne, na jini da bai kashe shi ba.
Na yarda da mubaya’ar da mutanen Iraki suka yi min, ba sai sun kashe Husaini (R.A) ba.
Kuma Malamai sun fada cewa, Yazidu, ya karrama iyalan Husaini (R.A) ya yi musu goma ta arziki, sannan yasa aka rako su Madina (Bayan ya ba su zabin in su na so su zauna a gurinsa).
Sai dai duk da wannan, Yazidu bai dauki fansa a kan wadanda suka kashe Sayyadina Husaini (R.A) ba, bai kuma sa an kashe su ba.
Abin kuwa da (`yan Shi’a) suke fada cewa: – An kama matan Sayyadina Husaini (R.A) a matsayin ba yi, an dinga kewayawa da su cikin garuruwa bayan an daure su (da sasari) a kan rakuma, wannan karya ce: mara tushe.
Godiya ta tabbata ga Allah, a cikin Musulmi, babu wanda ya taba kama Bani Hashim a matsayin bayi, babu kuma wani cikin al’ummar Manzon Allah (S.A.W.) da ya halatta hakan.
Banda wannan ma, Sahabbai irin su Abdullahi dan Umar da Usama dan Zaid (R.A) sai da suka yi iyaka kokarinsu wajen hana Sayyadina Husaini (R.A) zuwa kasar Iraki, domin sun san cewa lallai wasikun da aka aiko masa na karya ne, kuma mutanen Iraki zasu kwaye masa baya ne, kamar yadda suka kwayewa mahaifinsa baya.
Maganar cewa Yazidu yasa an kashe mutane sama da dubu goma a Madina, ta yadda har sai da jini ya jika Masallacin Manzon Allah (S.A.W), da kuma cewa ya kona tare da ruguje Ka’aba.
Sai mu ce: gaskiya ne akwai manya-manyan fitin-tinu, da suka faru lokacin mulkin Yazidu. Daga ciki akwai fitinar da ta faru a Madina da wacce ta faru a Makkah. Amma yana da kyau, a fahimci cewa akwai karin gishiri mai yawa a kan hakikanin abin da ya faru. Misali maganar cewa an yi yinkurin rushe Ka’abah, da maganar cewa, an kashe dubban mutane a Madina, har jini ya jika Masallacin Manzon Allah (SAW), malamai da yawa sun karyata riwayoyin dake nuni da hakan.
Domin galibin riwayoyin, sun zo ne ta hanyar ‘Yan Shi’a. kamar Abi Mikhnaf Lud dan Yahaya. Saboda haka ne ma, Ibn Kathir (RH) yake cewa: a cikin littafin sa BIDAYA “Mafiya yawan abin da ake rawaitowa, na kissar kashe Sayyadina Husaini da fitinar da ta faru a Madina da wacce ta faru a Makkah. ‘Yan Shi’a sun yi kare-kare da yawa a cikin su. Ba don wasu daga cikin manyan Malamai kamar Ibn Jarir sun hakaito kissoshin ba. Da ban rubuta su a cikin littafi na ba. Saboda mafiya yawa an samo hikayoyin ne daga Abi Mikhnaf, shi kuwa dan Shi’a ne, wanda Malamai suka hadu a kan cewa ba a karbar Hadisin sa”
Kuma kamar yadda aka sani ‘Yan Shi’a sun shahara da kirkiro abin da dukkan Malamai suka tabbatar da cewa bai faru ba. Ko kuma su karyata abin da dukkan malamai suka tabbatar da cewa ya faru.
Misali a kan haka shi ne – An samu wasu daga cikin ‘Yan Shi’a suna da’awar cewa Nana Fadima (R.A) ce kadai ‘yar Manzon Allah (S.A.W). Ragowar `ya`yansa kuwa wai Agololi ne, ba shi ne ya haife su ba.
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita ce: wacce alkunya aka san Manzon Allah (S.A.W) da ita?
Idan ‘Yan Shi’a suka ce baban Fadima.
Sai mu ce: Gaskiya ne Mahaifi ne ga Nana Fadima. Amma da wacce alkunya ya fi shahara?
Sanin kowa ne cewa, alkunyar da Manzon Allah (S.A.W) ya fi shahara da ita, ita ce “Abu Al-Kasim” wato mahaifin Alkasim. Shin Manzon Allah (S.A.W) zai danganta dan wani ne izuwa gare shi, bayan yasan cewa Shari’a ta hana?
Idan `Yan Shi’a suka ce Manzon Allah (S.A.W) ya danganta Alkasim izuwa gare shi ne, kamar yadda ya danganta Zaidu dan Harith (R.A) izuwa gare shi. Saboda shi ma Zaidu dan Harith (R.A) ana ce masa Zaidu dan Muhammad (R.A).
Sai mu ce: gaskiya ne cewa a farkon musulunci Manzon Allah (S.A.W) ya mayar da Zaid dan Harith tamkar dansa. Amma babu wani guri da aka taba rawaitowa cewa an yiwa Manzon Allah (S.A.W) alkunya da Abu Zaid.
Kari a kan haka tun bayan da aya ta sauka, ta hana kowa ya danganta kansa izuwa ga wani, idan ba mahaifinsa ba, Manzon Allah (S.A.W) da dukkan Sahabbai ba su sake kiran Zaidu da dan Muhammad ba.
Sabanin Alkasim, har Manzon Allah (S.A.W) ya bar duniya ana yi masa alkunya da mahaifin Alkasim, kuma kawo izuwa yanzu Malaman Musulunci baki daya, da wadanda ma ba Musulmi ba, suna yi masa alkunya da mahaifin Alkasim.
10) Mafi yawan abin da `Yan Shi’a, suke dangantawa Yazidu na shan giya da makamantansu, akwai karin gishiri a ciki. Domin ya tabbata a cikin Bukhari cewa, lokacin da aka dinga yada jita-jita a Madina cewa, Yazidu yana shan giya, baya kula da Sallah aka kuma yi masa bore ta hanyar korar gwamnansa na Madina.
Abdullahi dan Umar ya yi watsi da dukkan wannan jita-jitar, ya kuma tabbatar da mubaya’ar da ya yi masa tun da farko.
Kamar yadda daga cikin Ahlu Al-Baiti ma, Muhammad dan Ali dan Abi Dalib (R.A) wato kanin Sayyadina Husaini (R.A), ya karyata wadannan maganganu. Ya kuma shaidi Yazidu da cewa, ya zauna tare da shi, amma bai taba ganinsa ya sha giya ba, ya kuma kara da cewa ya ga Yazidu yana kula da Sallah yana lazimtar Sunna, yana bibiyar ilimi.
Wani abu da ya kamata a sani a nan shi ne, ba ma Yazidu ba, duk wani wanda ya shugabanci al’ummar Musulmi, babu wanda `Yan Shi’a basa yi masa sharri iri-iri. Wacce irin karya da kage ne `Yan Shi’a ba sa yiwa Sahabbai?
Sun ce musu kafirai, makaryata, masu cin amana. Sun jefi wasu da sata da zina kamar Nana Aisha (R.A). Sun jefi Sayyadina Umar (R.A) da neman maza, kamar yadda wani Malaminsu ya fada wai shi Ni’imatullahi Al’jaza’iri.
Mutanen Kufa kuwa, sun shahara da zargin shugabannni, kamar yadda suka tuhumi Sa’ad dan Abi Wakas da Sa’id dan Zaid (R.A). da rashin iya Sallah da zalunci. Su kansu Ahlu-Al-Baiti ba su sha, a gurin ‘Yan Shi’a ba.
Maganar cewa Imamu Ahmad dan Hambal Allah ya ji kansa, yana daga cikin masu la’antar Yazidu, bata inganta ba. Saboda a mazahabin Imamu Ahmad bai halatta a la’anci azzulumi ba kai tsaye.
Abin da ya tabbata daga Imamu Ahmad dan Hambal a ruwayar dansa Salih dan Ahmad shi ne, lokacin da aka yi masa magana a kan la’antar Yazidu. Sai ya ce: – “Yaushe ka taba jin mahaifinka ya la’anci wani mutum”?
Wani abu da ya kamata a sani shi ne: – Duk cikin malaman Sunna, babu wanda yake lissafa Yazidu dan Mu’awiyya daga cikin jerin halifofi shiryayyu ko adalan shugabanni ko salihan bayi.
Don haka koda Ahlu Al-Sunna sun ce Yazidu yana daga cikin halifofi, basa nufin yana daga cikin halifofi adalai ko salihan shugabanni. Abin da suke nufi kawai shi ne shi ma Yazidu yana daga cikin wadanda suka shugabanci al’umma. A kan haka ne Imamu Al-Suyudi ya rubuta littafinsa na tarihin halifofi.
Sannan yana da kyau a fahimci cewa manya manyan fitintinu guda uku ne suka faru lokacin halifancin Yazid, wadanda malamai suke zarginsa a kansu.
Ta daya- Fitinar kashe Sayyadina Husaini (R.A) wacce a sababinta fitintinu masu yawa suka biyo baya.
Ta biyu- Fitinar da ta faru a Madina lokacin da mutanen Madina suka yi masa bore, suka kori gwamnansa shi kuma ya tura aka yake su tare da bada dammar wawashe dukiyoyin al’umma da zubar da jinin wadanda ba su ji ba ba su ba su kuma gani ba. .
Ta uku- Fitinar yakar Abdullahi dan Zubair (R.A) a Makka, lokacin da shi ma ya yi masa tawaye, wacce a sababin ta ne, Abdullahi dan Zubair (R.A) ya buya a Harami (Ka’aba), aka dinga harba masa igwa irin ta wancan zamanai, har abin ya shafi Ka’aba, amma ba Ka`abar aka nufa da harbin ba tun asali.
Wannan kuwa dabi’a ce ta shugabanni, na gari ko ba na gari ba, wajen yakar duk wanda suke ganin ya yi musu bore.
Ko dai a cikin yin hakan, su tsaya dai-dai inda shari’ah ta tsaida su, ko kuma su wuce gona da iri kamar a nan.
Haka kuma, abu ne sa nanne a tarihin Musulunci cewa, babu wani Musulmi na gari, da aka taba samu ya nufi Ka’aba da niyyar wulakanta ta.
`Yan Shi’a, su aka taba samu a tarihi, sun je sun karkashe dubunnan masu aikin Hajji, suka jefa gawarwakinsu cikin rijiyar Zam-Zam, suka kuma dauke dutsen Hajrul Aswadu, bayan sun cire kofar Ka’aba da rigar da ake sanya mata suka tafi da su. A wannan lokaci ne suka dinga zungurin Ka’aba suna cewa: – “Ina tsuntsayen da aka ce Allah ya turowa Abrahata lokacin da ya zo ruguje Ka’aba”?
Kuma har yanzu wannan muguwar akidar ta su tana nan, domin a ko da yaushe buri suke su samu damar da zasu mamaye Ka’aba, su mayar da alkibla ta koma Karbala. kamar yadda ake jin hakan daga bakunan malamansu na wannan zamani. Barnar da ‘Yan Shi’a suka tafka a shekarar 1988 lokacin aikin Hajji, babbar sheda ne a kan abin da muka gabatar.
12) Duk wani aiki mara kyau da `Yan Shi’a zasu zargi Banu Umayya da sarakunansu da shi, to `Yan Shi’a sun aikata kwatankwacinsa ko mafi muni da shi.
Zaka gane hakan, idan ka karanta tarihin Shi’a da daulolinsu kamar daula Ubaidiyya, Safawiyya, Baha’iyya har izuwa daularsu ta yanzu dake kasar Iran.
Duk wanda ya karanta tarihin wadannan dauloli da aika ce-aikacen su, babu abin da zai gani, sai bakin tarihi mai cike da zalunci, aikata miyagun laifuka, zubar da jini ga kuma uwa uba shirka, da sukan Annabawa.
Mafi munin abin da ake tuhumar daular Banu Umayya da shi, shi ne: – An samu wasu daga sarakunansu da suka shahara da zalunci, babakere a kan dukiyar al’umma, mulki na danniya da kama karya, sai nuna gaba ga Ahlu Al-Baiti.
Amma duk cikin sarakunan Banu Umayya, babu wani wanda ya taba yin da’awar Annabta, ko ya ce: a na yi masa waha yi ko ya ce: shi Allah ne.
Amma mutane nawa ne a cikin shugabannin Shi`a suka yi da’awar Annabta? Nawa ne suka ce suma alloli ne, ko suka allantar da wani ko, aka allantar da su?
Kadan daga cikinsu akwai Mukhtar dan Ubaid, wanda ya bayyanar da da`awar neman fansar jinin Sayyadina Husaini (R.A) a Irak, daga baya ya yi da`awar Annabta. Ga kuma shugabannin Daula Al-Fadimiyya wacce Banu Ubaid suka assasata.
A takaicen takaitawa, akidar Shi’a an gina ta ne kacokan, a kan allantar da wasu da shige gona da iri wajen kambama bayi da ba su matsayin daya zarce na Annabawa.
Banda wannan ma, a tarihin Daular Banu Umayya, duk da cewa an samu wasu daga sarakunansu da suka shahara da zalunci, amma a bangare guda sun taka rawa wajen yada Addini, da yakar kafirai da yada ilimi.
A zamanin daular Banu Umayya garuruwa da yawa na kafirai sun dawo karkashin Daular Musulunci.
A tarihin Shi’a kuwa, babu wani gari na kafirai da suka taba yaka.
Abin da ‘Yan Shi’a suka kware a cikinsa kawai shi ne, zubar da jinin Musulmi da taimakawa kafirai da zalunci da halatta jinin duk wani wanda ba dan Shi’a ba.
A kan haka dukkan Malaman tarihi sun hadu a kan cewa, ba’a taba samun sarakuna azzalumai masu mummunar akida da bakin tarihi ba, irin daular Fadimiyya ta `Yan Shi’a.
Dangane da ranar Ashura kuwa, abin da ya tabbata a kanta na Hadisi shi ne azumtar wannan ranar, domin a ranar ce Allah ya halakar da Fir’auna ya tseratar da Annabi Musa (A.S) da mutanensa.
Amma duk wani abu da ake hakaitowa cewa ya faru a wannan ranar, kamar ruwan Dufana, da karbar tuban Annabi Adam (A.S) ko falalar yalwatawa iyali wato cika ciki da makamantansu, tatsuniya ce: kawai mara tushe da asali.
Kamar irin a bin da ake rawaitowa na falalar watan Maulud, da abubuwan da suka faru lokacin haihuwar Manzon Allah (S.A.W) na rugujewar katangar Kisira da mutuwar wutar da suke bautawa da abin da ake dangana shi ga Nana Amina (R.A) mahaifiyar Manzon Allah (S.A.W) na mafarki da Annabawa da makamantansu.
Abin da ya inganta dangane da haihuwar Manzon Allah (S.A.W) shi ne, mahaifiyarsa ta ga wani haske ya fita daga cikin jikinta ya haske yankin Sham.
Wani misalin shi ne abin da ake ruwaitowa na falalar watan Rajab shi kadai da Azumtarsa da nafilfilin cikinsa, da wanda ake ruwaitowa na nafiloli na musamman a dararen watan Ramadan.
14) A Addinin Musulunci, babu inda aka halatta sanya bakaken kaya da dukan jiki don tunawa da wata rana ta bakin ciki. Wannan kuwa Ijma’i ne na Malaman Sunna da Limaman Ahlu Al-Baiti.
A ina aka samu wani daga cikin shugabannin Ahlu Al-Baiti, tun daga kan Sayyadina Aliyu (R.A) ko Abdullahi dan Abbas (R.A) ko wani daga Bani Hashim ko Bani Al-Muddalib sun sanya bakaken kaya, suna dukan jiki wai don tunawa da ranar da aka kashe Sayyadina Husaini (R.A)? ko `Yan Shi’a, sun fi su son Sayyadina Husaini (R.A) ne?
15) A lokacin da `Yan Shi’a suke la’antar Yazidu da iyayensa, saboda sun kashe Sayyadina Husaini (R.A).
A bangare guda kuma sai ga limaman Ahlu Al-baiti, suna la’antar `Yan Shi’a, suna zarginsu da kashe Sayyadina Husaini (R.A).
Wannan maganar kuwa, malaman Shi’a sun tabbatar da ita a cikin littattafansu. Ga kadan daga ciki: –
Imamu Zainul Abidina wato Aliyu dan Husaini (R.A), wanda a gabansa aka kashe Sayyadina Husaini (R.A) mahaifinsa, ga abin da yake cewa da `Yan Shi’a: –
“Ba ku ne kuka rubuto wasika zuwa ga mahaifina ba, kuka yaudare shi, kuka yi alkawarin yi masa mubaya’a sannan daga baya kuka kashe shi, kuma kuka wulakanta shi ba?
Da wane ido zaku kalli Manzon Allah (S.A.W), idan ya ce da ku, kun kashe iyalina, kun keta min alfarma bakwa cikin al’ummata.
A wani gurin kuma cewa ya yi da ‘Yan Shi’a, bayan ya ga sun fito suna kuka suna dukan jiki a kan kashe Sayyadina Husaini (R.A), sai ya ce: –
“Kunga wadannan da suke kuka saboda mu, su ne suka kashe mana mahaifi”
Sayyadina Husaini (R.A) shi kuma cewa ya yi da `Yan Shi’a: –
“Ya Allah, idan ka kyale su zuwa wani lokaci, ka rarraba tsakaninsu, ka sanya su kungiyoyi daban-daban, kada ka sa shugabanni su yarda da su domin su ne, suka kirawo mu don su taimake mu, amma daga baya suka yi mana ta’addanci suka kashe mu” .
Kamar yadda Fadima karama da Zainab `yar Ali dan Husaini (R.A) suka zargi `Yan Shi’a, da cewa: – “Makirai ne, makaryata, masu karya alkawari”. Suka zarge su da kashe Sayyadina Husaini (R.A) da Mahaifinsa Sayyadina Ali (R.A) da jefa Ahlu Al-Baiti cikin bala’i kala-kala.
Duk wadannan maganganu malaman Shi’a sun tabbatar da su a cikin litattafansu.
Sannan ya tabbata a cikin Bukhari cewa, wani mutumin Iraki ya tambayi Abdullahi dan Umar (R.A), hukuncin kashe kuda idan mutum yana cikin harami.
Sai Abdullahi dan Umar (R.A) ya ce: – “Abin mamaki wai mutanen Iraki su ne zasu yi tambaya a kan hukuncin kashe kuda, bayan su ne suka kashe jikan Manzon Allah (S.A.W) Sayyadina Husaini (R.A).
Tambaya ga ‘Yan Shi’a a nan ita ce, wanene hakikanin wanda ya kashe Sayyadina Husaini (R.A)?
Idan suka ce Yazidu ne da mabiyansa.
Sai mu ce wannan ya ci karo da maganganun limaman Shi’a kamar yadda ya gabata.
Don haka shaidar wa za’a karba, dangane da wanda ya kashe Sayyadina Husaini (R.A)? Shaidar shi kansa Sayyadina Husainin (R.A) da `ya`yansa da `yan uwansa da Sahabbai ko shaidar ‘Yan Shi’a?
Idan wani ya ce: – Ya ya za’a ce, `Yan Shi’a ne, suka kashe Sayyadina Husaini (R.A) bayan sanannen abu ne cewa Gwamnan Iraki ne ya turo sojojin da suka kashe shi, karkashin Jagorancin Umar dan Sa’ad, shi kuwa ba dan Shi’a ba ne?
Sai mu ce, amsa a nan ita ce kamar haka: –
Na daya – duk limaman Ahlu Al-Baiti sun tabbatar da cewa `Yan Shi’a ne suka kashe musu dan uwa. kuma shi kansa Sayyadina Husaini (R.A) ya tabbatar da cewa ‘Yan Shi’a suka kashe shi, kamar yadda ya gabata.
Na biyu– Litattafan Shi’a da Malamansu duk sun yarda da cewa `Yan Shi’a ne suka kashe Sayyadina Husaini.
Na uku – `Yan Shi’a ne, suka rubutawa Sayyadina Husaini (R.A) wasiku, suka ce ya zo su taimake shi, amma da ya je gurinsu, duk suka gudu suka je suka yiwa Ubaidullahi dan Ziyad mubaya’a, suka kyale Sayyadina Husaini (R.A) da `yan uwansa da almajiransa babu mataimaki har aka kashe shi.
Na hudu– Duk wanda ya yaudare ka, ya tura ka cikin halaka, sannan ya gudu ya barka, shi yake da alhakin kashe ka.
`Yan Shi’a kuwa, su ne suka yaudari Sayyadina Husaini (R.A) daga baya suka kwaye masa baya.
Na biyar– Ba Sayyadina Husaini (R.A) kawai `Yan Shi’a suka yaudara ba. Sun yaudari Ahlu Al-Baiti da dama, tun daga kan Sayyadina Ali (R.A) zuwa wadanda suka biyo bayansa.
Kamar yadda suka yaudari Sayyadina Husaini (R.A) da Zaid dan Ali dan Husaini dan Aliyu dan Abi Dalib jikan Sayyadina Husaini (R.A).
Na Shida: – Mun gabatar da sunayen wadanda suka kashe Sayyadina Husaini (R.A), kuma ya tabbata cewa dukkanninsu ‘Yan Shi’a ne.
Wakar da ‘Yan Shi’a suke dangantawa ga Yazidu ta murnar kashe Husaini, da kwatanta ta da abin da ya faru a matsayin daukar fansar abin da ya faru ga iyayensa ranar yakin Badar. Waka ce ta karya wacce Muhammad dan Humaid ya jingina masa. Shi kuwa Muhammad dan Humaid cikakken dan Shi’a ne.
Banda wannan ma kafiran Makkah tuni suka yi alfaharin daukar fansar abin da aka yi musu a Badar, a ranar yakin Uhud. Domin a wannan ranar ne, Abu-Sufyan ya dinga cewa “Mun rama abin da ya faru a garemu a ranar yakin Badar” sai musulmi suka ba shi amsa da cewa “Ba ku rama ba, domin wadanda aka kashe mana suna Aljannah. Naku kuwa suna wuta”
Sannan malamai sun tabbatar da cewa ita asalin wannan wakar ta Ibn Zaba’ara ce, wacce ya yi ta bayan yakin Uhud.
Don haka, tuni maganar daukar fansar abin da ya faru a Badar ya zama tarihi.
Zamu cigaba Inshaa Allahu..

4 responses to “DARASI NA GOMA SHA BIYU (12)SHUBUHOHIN SHI’A A MAHANGAR SHARI’A(Malam Aminu Ibrahim Daurawa)”
 1. rufai Avatar
  rufai

  jaxakallahu khyran wafata’allahu alaika warahamna iliman nafiya

 2. Manu Bulama Avatar
  Manu Bulama

  Jazakallahu bikhair

 3. Haruna yusuf Avatar

  A gaskiya yan shi,a ba kananan makaryata bane.

 4. asheer abubakar Avatar
  asheer abubakar

  Allah kashiryamu bakidaya akan sunnar annabi muhammad saw

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: