FATAWOYIN LAYYA(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

A yau za mu amsa wadannan
tambayoyi.
*Tambaya:
Wace dabba ya kamata a yi layya
da ita?
AMSA:
Malamai sun yi sabani akan
dabbar da aka fi so a yi layya da
ita;
Imam Mālik da daya daga cikin
riwayar Imam Ahmad suna ganin
cewa: rago shi ne yafi, sai shanu
sannan sai rakuma.
Ibn Abdul Barr ya ce: Imam Mālik
ya ce: ragon da aka fi so a yi layya
da shi, shi ne wanda ba’a fidiye shi
ba, sai wanda aka yi wa fidye, sai
tunkiya, haka kuma awaki, sai
shanu sannan rakuma. Amma idan
hadaya ce, to, rakumi shi ne ya fi,
sai shanu sannan tumaki da awaki.
Dalilinsa shi ne hadisin Anas Ibn
Mālik radhiyallahu anhu ya ce:
ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻜﻔﺄ ﺇﻟﻰ
ﻛﺒﺸﻴﻦ ﺃﻗﺮﻧﻴﻦ ﺃﻣﻠﺤﻴﻦ ﻓﺬﺑﺤﻬﻤﺎ ﺑﻴﺪﻩ .
Ma’ana:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya juya daga
wurin salla ya je ya yi layya da
raguna guda biyu masu fari da baki
kuma masu kaho…
Da kuma hadisin Aliyu Ibn Abī
Xalib radhiyallahu anhu wanda ya
ce:
ﺃﻫﺪﻯ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﺎﺋﺔ ﺑﺪﻧﺔ …
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yi hadaya da rakuma
dari…
Amma mafi yawan malamai
kamarsu Imam Shāfi’ī da Imam
Abū Hanīfah, haka kuma Imam
Ashhab da Imam Ibn Sha’abān
daga Malikiyyah da sauransu sun
tafi a kan cewa a sha’anin layya da
hadaya rakumi shi ne ya fi, sai.
shanu sannan tumaki da awaki.
Dalilin da suka dogara da shi, shi
ne hadisin da a ka karbo daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu ya ce:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﻦ ﺍﻏﺘﺴﻞ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺠﻤﻌﺔ ﻏﺴﻞ ﺍﻟﺠﻨﺎﺑﺔ ﺛﻢ ﺭﺍﺡ
ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺑﺪﻧﺔ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻧﻴﺔ
ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺑﻘﺮﺓ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ ﺍﻟﺜﺎﻟﺜﺔ
ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﻛﺒﺸﺎ ﺃﻗﺮﻥ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ
ﺍﻟﺮﺍﺑﻌﺔ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺩﺟﺎﺟﺔ ﻭﻣﻦ ﺭﺍﺡ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﺎﻋﺔ
ﺍﻟﺨﺎﻣﺴﺔ ﻓﻜﺄﻧﻤﺎ ﻗﺮﺏ ﺑﻴﻀﺔ …
Ma’ana:
Wanda ya yi wankan Juma’a ya tafi
masallaci a farkon lokaci kamar ya
nemi kusanci da Allah da yankan
rakumi ne, wanda ya tafi a lokaci
na biyu kamar ya nemi kusanci da
Allah da yankan sa, wanda ya je a
lokaci na uku kamar ya nemi
kusanci da Allah da yankan rago
mai kaho biyu, wanda ya je a
lokaci na hudu kamar ya nemi
kusanci da Allah ne da yankan
kaza, wanda ya je a lokaci na biyar
kamar ya nemi kusanci da Allah ne
da kwai…
Wannan hadisin ya nuna ana
neman kusanci da Allah ne da abin
da ya fi girma, wannan kuwa dalili
ne a bayyane da yake nuna rakumi
yafi. Wadannan malamai suka ce
hadisin da Imam Mālik ya dogara
da shi cewa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya
yanka raguna biyu masu kaho a
layyarsa, wannan abin da Allah ya
hore masa kenan, kuma Annabi
sallallahu alaihi wa sallama bai
nassanta cewa rago ne ya fi ba.
Ibn Taīmiyyah ya ce: ana samun
lada ne gwargwadon gimar abin da
aka yanka.
Wannan fatawar ita ce tafi rinjaye a
kan fatawar su Imam Mālik.
*Tambaya:
Shin layya farilla ce ko sunna?
AMSA:
Hakika layya sunna ce mai karfi
daga cikin sunnonin Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama.
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
umarci Annabinsa sallallahu alaihi
wa sallama da yin ta a cikin Suratul
Kauthar, inda yake cewa:
ﺇﻧﺎ ﺃﻋﻄﻴﻨﺎﻙ ﺍﻟﻜﻮﺛﺮ (1) ﻓﺼﻞ ﻟﺮﺑﻚ ﻭﺍﻧﺤﺮ (2)
ﺍﻟﻜﻮﺛﺮ١- ٢
Ma’ana:
Hakika mun ba ka Al-Kausara,
saboda haka, ka yi salla ga
Ubangijinka, kuma ka soke
(hadayarka ko layyarka)…
A wata ayar kuma Ubangiji
subhanahu wa ta’ala cewa ya yi:
ﻗﻞ ﺇﻥ ﺻﻠﺎﺗﻲ ﻭﻧﺴﻜﻲ ﻭﻣﺤﻴﺎﻱ ﻭﻣﻤﺎﺗﻲ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ
ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ (162) ﻟﺎ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺑﺬﻟﻚ ﺃﻣﺮﺕ ﻭﺃﻧﺎ
ﺃﻭﻝ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ (163) ﺍﻷﻧﻌﺎﻡ: ١٦٢ – ١٦٣
Ma’ana:
Ka ce: hakika sallata da yanke-
yankena da rayuwata da mutuwata
duk suna ga Allah Ubangijin talikai,
ba shi da abokin tarayya, kuma da
haka aka umarce ni, kuma ni ne
farkon masu mika wuya.
Kuma Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya umarci
al’ummarsa da su yi layya mutukar
suna da ikon yi. Dalili kuwa shi ne
hadisi ya tabbata Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺇﻥ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺃﻫﻞ ﺑﻴﺖ ﻓﻲ ﻛﻞ ﻋﺎﻡ
ﺃﺿﺤﻴﺔ .
Ma’ana:
Ya ku mutane! Hakika yana kan
kowanne magidanci da iyalansa
yin layya a kowacce shekara.
(Manzon Allah ya fadi haka ne
alhali yana tsayuwar Arfa).
Haka kuma, hadisi ya tabbata daga
Abū Huraīrah radhiyallahu anhu ya
ce: Manzon Allah sallallahu alaihi
wa sallama ya ce:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻌﺔ ﻭﻟﻢ ﻳﻀﺢ ﻓﻼ ﻳﻘﺮﺑﻦ ﻣﺼﻼﻧﺎ .
Ma’ana:
Duk wanda Allah ya ba shi damar
yin layya bai yi ba, to, kada ya
kusanci wurin sallar idinmu.
Wannan hadisin yana nuna narko
ne ga wanda Allah ya ba shi damar
yin layya amma yaki yi.
Kuma ya tabbata cewa Manzon
Allah sallallahu alaihi wa sallama
ya yi layya kamar yadda ya zo a
cikin hadisi daga Anas Ibn Malik
radhiyallahu anhu ya ce:
ﺃﺿﺤﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﻜﺒﺸﻴﻦ
ﺃﻣﻠﺤﻴﻦ ﺃﻗﺮﻧﻴﻦ ﺫﺑﺤﻬﻤﺎ ﺑﻴﺪﻩ ﻭﺳﻤﻰ ﻭﻛﺒﺮ ﻭﻭﺿﻊ
ﺭﺟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺻﻔﺎﺣﻬﻤﺎ .
Ma’ana:
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya yanka raguna biyu
masu kahonni guda biyu farare tas,
da hannunsa mai albarka, a
matsayin layyarsa, sannan ya
ambaci sunan Allah, ya girmama
shi (watau a lokacin yin yanka ya
kasance yana cewa Bismillahi,
Allahu Akbar!) Kuma ya dora
kafarsa akan wuyansu.
Wannan ke nuna cewa lallai layya
sunna ce mai karfi, ga wanda Allah
ya ba shi iko. Kuma malamai sun
hadu a kan cewa: ita layya tana
daga cikin ibada, amma ga wanda
Allah ya ba shi iko kawai.
*Tambaya:
Wace irin falala da alherai Ubangiji
subhanahu wa ta’ala ya tanadar
wa mai yin layya?
AMSA:
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
tanadarwa mai yin layya alkhaīrai
da dama, amma ga kadan daga
ciki:
1-Ubangiji subhanahu wa ta’ala zai
sa shi daga cikin masu tsoronsa
idan har ya kyautata niyya, saboda
Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya
ce:
ﻟﻦ ﻳﻨﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺤﻮﻣﻬﺎ ﻭﻟﺎ ﺩﻣﺎﺅﻫﺎ ﻭﻟﻜﻦ ﻳﻨﺎﻟﻪ ﺍﻟﺘﻘﻮﻯ
ﻣﻨﻜﻢ … ﺍﻟﺤﺞ: ٣٧
Ma’ana:
Ba namanta ko jininta su ne suke
isa wajen Allah ba, sai dai tsoron
Allah, shi ne yake isa wajensa.
2-Haka kuma Ubangiji subhanahu
wa ta’ala zai sanya shi ya kasance
daga cikin managarta. Domin a
karshen ayar, Ubangiji subhanahu
wa ta’ala ya ce:
… ﻭﺑﺸﺮ ﺍﻟﻤﺤﺴﻨﻴﻦ (37) ﺍﻟﺤﺞ: ٣٧
Ma’ana:
… Ka yi wa managarta bushara.
3-Haka kuma Ubangiji subhanahu
wa ta’ala zai sa a rubuta masa
ladan masu raya sunnar Annabi
Ibrahim alaihissalam da Annabi
sallallahu alaihi wa sallama
matukar ba da kudin haram ya yi
layyar ba, kuma ya yine don Allah,
saboda Allah ba ya karbar aiki sai
tsarkakakke.
3-Haka kuma Ubangiji subhanahu
wa ta’ala zai sa shi daga cikin
masu tausayawa fajirai da
makwabta, in dai har ya raba
layyar yadda sunna ta koyar.
Duk da irin falalar da layya take da
ita, akwai hadisai da`ifai (raunana)
da wadanda aka kago a kan falalar
layya, misalin hadisin da aka ce
wai Zaīdu Ibn Arkam radhiyallahu
anhu ya ce:
ﻗﺎﻝ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻳﺎ
ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ. ﻣﺎﻫﺬﻩ ﺍﻷﺍﺣﻲ ؟ ﻗﺎﻝ ) ﺳﻨﺔ ﺃﺑﻴﻜﻢ
ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ( ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻓﻤﺎ ﻟﻨﺎ ﻓﻴﻬﺎ ؟ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ : ﻗﺎﻝ
) ﺑﻜﻞ ﺷﻌﺮﺓ ﺣﺴﻨﺔ ( ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻓﺎﻟﺼﻮﻑ ؟ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ
ﺍﻟﻠﻪ : ﻗﺎﻝ ) ﻳﻜﻞ ﺷﻌﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻮﻑ ﺣﺴﻨﺔ )
Ma’ana:
Sahabban Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama sun ce: Ya
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama; mece ce wannan layyar ?
Sai ya ce: “ Sunnar babanku
Ibrahim alaihis salam ce. Sai suka
ce: me za mu samu idan mun yi
ta? Sai ya ce: za ku samu lada ne
da kowane gashi daya na dabbar .
To, wannan hadisin maudū’i ne,
domin a cikin sanadinsa akwai
Nufaīl Ibn Hārith, wanda malamai
suke tuhumar sa da kaga hadisai
na karya, kuma ire-iren wadannan
hadisai suna da yawa.
Haka kuma akwai wani hadisi da’ifi
(mai rauni) shi ma da ake cewa wai
Nana A’ishah ﺭﺿﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta
ruwaito cewa Manzon Allah
sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﺎ ﻋﻤﻞ ﺁﺩﻣﻲ ﻣﻦ ﻋﻤﻞ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻨﺤﺮ ﺃﺣﺐ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻣﻦ ﺇﻫﺮﺍﻕ ﺍﻟﺪﻡ ﺇﻧﻬﺎ ﻟﺘﺄﺗﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺑﻘﺮﻭﻧﻬﺎ
ﻭﺃﺷﻌﺎﺭﻫﺎ ﻭﺃﻇﻠﺎﻓﻬﺎ ﻭﺃﻥ ﺍﻟﺪﻡ ﻟﻴﻘﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻤﻜﺎﻥ
ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﻘﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﺄﺭﺽ ﻓﻄﻴﺒﻮﺍ ﺑﻬﺎ ﻧﻔﺴﺎ .
Ma’ana:
Babu wani aiki mafi soyuwa a
wurin Allah da Dan Adam zai yi a
ranar idin babbar salla, kamar
zubar da jinin dabbar layya. Ya ce
wai, hakika dabbar za ta zo da
kahonta da gashinta da kofatonta.
Hakika jininta zai isa wurin Allah
kafin ya zuba kasa, saboda haka
ku yi ta da dadin rai.
Wannan da ire-irensa, suna da
yawa wadanda lokaci ba zai ba mu
damar kawo su ba a cikin wannan
littafi, sai dai a yi hattara, kuma a
rika tambayar malamai masana
sunnar Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama.
*Tambaya:
Mene ne matsayin wanda Allah ya
ba shi ikon yin layya, amma ya ki
yi?
AMSA:
Hakika wanda Ubangiji subhanahu
wa ta’ala ya ba shi ikon yin layya
amma ya ki yi, ya sabawa sunnar
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama da aikin magabata na
kwarai, kuma (sakamakon abin da
ya yi) shi ne kada ya je sallar idi,
ya yi zamansa a gida. Saboda
hadisin da ya tabbata daga Abū
Huraīrah radhiyallahu anhu ya ce:
Hakika Manzon Allah sallallahu
alaihi wa sallama ya ce:
ﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻟﻪ ﺳﻌﺔ ﻭﻟﻢ ﻳﻀﺢ ﻓﻼ ﻳﻘﺮﺑﻦ ﻣﺼﻼﻧﺎ .
Ma’ana:
Wanda Allah ya ba shi yalwar yin
layya, amma bai yi ba, kada ya
kusanci wajen sallar idinmu.
Lallai ba karamar ukuba ba ce;
Manzon Allah sallallahu alaihi wa
sallama ya hana mutum kusantar
wannan alheri mai dimbin yawa a
wurin da ake neman kusanci ga
Allah da haduwa da al’umma
domin nuna farin ciki, wanda ba a
yinsa daga shekara sai shekara.
*Tambaya:
Wanda Allah ya ba shi abin yin
layya, amma iyayensa ba su samu
ba, shin ya kamata ya yi, ko kuwa
zai ba wa iyayensa ne su yi?
AMSA:
Ya kamata a fahimci cewa, a
wajen sha’anin ibada, yi wa Allah
da Manzonsa biyayya shi ne gaba
da komai. Saboda haka tunda
yake, ita layya ibada ce, wanda
duk Allah ya bai wa dama, sai ya
gabatar da tasa, sannan ya
sayawa iyayensa abin da za su yi
tasu.
Allah ya horewa duk musulmi
masu niyya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates