Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Allah maɗaukakin sarki yace:
Menene Allah zai amfana da yi muku azaba idan kun gode, kuma kunyi imani? Lallai Allah ya kasance mai godiya kuma Masani.
Suratun-Nisa: 147
Wannan ayah tana nuna mana falalar godiya wa Allah alan duk Ni’ima da yayi mana. Domin godiya wa Allah yana ƙara Ni’imah wa bawa, kamar yadda rashin godiya wa Allah yakan jawo gushewar Ni’imah.
Ana yin godiya ne da abubuwa uku. Baki, gaɓɓai, zuciya.
Ga bayaninsu kaman Haka:
1. Godiya da Zuciya: Shine mutum ya ji Falalar wannan Ni’imah da Allah yayi masa acikin zuciyar sa, sannan ya ƙudurce a zuciyarsa cewa wannan ni’ima daga Allah ne shi kaɗai.
Domin baya halatta mutum ya danganta ni’imar da Allah yayi masa zuwa ga wani. Domin hakan kafirce wa ni’imar Allah ne.
2. Godiya da Harce: Shine mutum ya tabbar da ni’imar Allah da bakinsa bayan ya ƙudurce acikin zuciyar sa, da kuma Shagaltar da Harshen sa wurin gode wa Allah. Misali a duk lokacin da zaiyi magana kan ni’imah da yake dashi ya rinƙa dangana shi ga Allah, sannan ya yawaita faɗin Alhamdulillah a kowani lokaci.
An rawaito daga Anas Allah ya ƙara masa yarda yace:
Lallai Allah yana yarje wa bawansa idan yaci abinci ya masa godiya akai, ko yasha abin sha ya gode masa akai.
Sahihu Muslim: 2734
Shiyasa yana da kyau Mutum ya bayyana Ni’imar da Allah yayi masa sannan yayi masa godiya akai. Kada Allah yayi wa mutum ni’imah ya ɓoye.
Allah maɗaukakin sarki yace:
Amma game da ni’imar ubangijin ka, ka bada labarin sa.
Suratu Duha: Aya ta 11
Shi yasa wasu magabata sukace:
Wanda ya ɓoye ni’ima, to haƙiƙa ya kafurce mata, wanda ya bayyana ta, ya yaɗa ta haƙiƙa ya gode wannan ni’ima ɗin.
Madarijus-salikin: 2/246
Sai dai kuma idan akwai tsoron idan ya bayyana ɗin za’a iya cutar dashi to anan sai ya ɓoye saboda lalura.
3. Godiya da gangan jiki: Shine mutum yayi amfani da gabbansa baki ɗaya wurin yin biyayya wa Allah, kada yayi amfani da ni’imar da Allah ya bashi wurin tsaɓa wa Allah.
Misali idan Allah ya azurta mutum da lafiya da ƙarfi to kada yayi amfani da wannan lafiyar wurin zuwa tsaɓon Allah, haka nan idan Allah ya azurta mutum da dukiya, to kada yayi amfani da wannan dukiyar wurin tsaɓa wa Allah, haka idan Allah ya azurta mutum da yin aure, kada ya tsaɓawa Allah wurin yin bukukuwa da suka tsaɓa wa Shari’ah. Duka wannan Yana daga cikin godiya wa Allah.
Saboda Haka mu guji tsaɓa wa Allah cikin Ni’imar da yayi mana, domin hakan na janyo gushewar Ni’imar Allah da yayi wa Bawa.
Allah yasa mudace.
Leave a Reply