1. YA HALATTA, KAI SUNNAH NE
MA: MATA SU KADA DUNDUFA
TARE DA WAKE-WAKE
WADANDA KE DA SAFTA A
RANAR DAURIN AURE, KO A
RANAR SADUWAR MIJI DA
MATARSA, KO A RANAR
WALIMAR AUREN.
2. YA HALATTA MATA SU YI
RAWA A LOKACIN BUKUKUWAN
AURE MATUKAR DAI SU-YA-SU
NE A WURIN BABU WANI
WANDA YAKE DAN WAJE NE A
CIKINSU, MATUKAR KUMA BA
SU BAYYANAR DA TSIRAICI BA A
LOKACIN RAWAR.
3. YA HALATTA A YI WA’AZI A
FILIN WALIMA.
20/5/1434 H 1/4/2013 M
A- Al-Haafiz Ibnu Hajar ya ce cikin
littafinsa Fathul Barii 9/110 :-
((… ﻭﺍﻥ ﺿﺮﺏ ﺍﻟﺪﻑ ﻳﺸﺮﻉ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﻜﺎﺡ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻌﻘﺪ
ﻭﻋﻨﺪ ﺍﻟﺪﺧﻮﻝ ﻣﺜﻼ ﻭﻋﻨﺪ ﺍﻟﻮﻟﻴﻤﺔ ﻛﺬﻟﻚ)).
Ma’ana: ((..Kuma bugun dundufa
yana halatta cikin aure: Lokacin
daurin aure, da lokacin saduwa
bisa ga misali, da kuma lokacin
walima shi ma kamar haka)).
Intaha.
Imamul Bukharii ya tuwaito cikin
Sahih hadithi na 5162 cewa Nana
A’isha ta shugabancin kai wata
amarya zuwa dakin mijinta cikin
Ansarawa sai Annabi mai tsira da
amincin Allah ya ce:-
((ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻌﻜﻢ ﻟﻬﻮ؟ ﻓﺎﻥ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ
ﻳﻌﺠﺒﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻮ)).
Ma’ana: ((Ya ke A’isha babu wasu
yan kade-kade tare da ku? Lalle
yan kade-kade suna kayatar da
Ansarawa)). A ma wata riwayar ta
wannan hadithin sai Annabi ya ce
da ita:-
(( ﻓﻬﻞ ﺑﻌﺜﺘﻢ ﻣﻌﻬﺎ ﺟﺎﺭﻳﺔ ﺗﻀﺮﺏ ﺑﺎﻟﺪﻑ ﻭﺗﻐﻨﻲ((؟
Ma’ana: ((Ko kun hada ta da wata
yarinya da zata rika kada dundufa
tana ta waka))? Intaha.
B- Sheik Salih Bin Fauzaanil
Fauzaan ya ce cikin littafinsa mai
suna: Fataawal Mar’atil Muslimah
2/651 :-
(( ﻻ ﺑﺎﺱ ﺑﺮﻗﺺ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺑﻤﻨﺎﺳﺒﺔ ﺍﻟﺰﻭﺍﺝ ﻭﺿﺮﺑﻬﻦ
ﺑﺎﻟﺪﻑ ﻣﻊ ﺷﻲﺀ ﻣﻦ ﺍﻟﻐﻨﺎﺀ ﺍﻟﻨﺰﻳﻪ ﻻﻥ ﻫﺬﺍ ﻣﻦ
ﺍﻋﻼﻥ ﺍﻟﺰﻭﺍﺝ ﺍﻟﻤﺎﻣﻮﺭ ﺑﻪ ﺷﺮﻋﺎ ﻟﻜﻦ ﺑﺸﺮﻁ ﺍﻥ
ﻳﻜﻮﻥ ﺫﻟﻚ ﻓﻲ ﻣﺤﻴﻂ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻘﻂ ﻭﺑﺼﻮﺕ ﻻ
ﻳﺮﺗﻔﻊ ﻭﻳﺘﺠﺎﻭﺯ ﻣﻜﺎﻧﻬﻦ ﻭﺑﺸﺮﻁ ﺍﻟﺘﺴﺘﺮ ﺍﻟﻜﺎﻣﻞ
ﺑﺤﻴﺚ ﻻ ﻳﺒﺪﻭ ﺷﻲﺀ ﻣﻦ ﻋﻮﺭﺓ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﻓﻲ ﺣﺎﻟﺔ
ﺍﻟﺮﻗﺺ ﻛﺴﻴﻘﺎﻧﻬﺎ ﻭﺫﺭﺍﻋﻴﻬﺎ ﻭﻋﻀﺪﻳﻬﺎ ﻭﺍﻧﻤﺎ ﻳﺒﺪﻭ
ﻣﻨﻬﺎ ﻣﺎ ﺟﺮﺕ ﻋﺎﺩﺓ ﺍﻟﻤﺮﺍﺓ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﺔ ﺑﻜﺸﻔﻪ ﻓﻲ
ﺣﻀﺮﺓ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ )).
Ma’ana: ((Babu wani laifi game da
rawan mata saboda dalilin aure,
haka nan bugun dundufarsu tare
da yin wani abu na waka mai
sabta, saboda wadannan abubuwa
duka suna daga cikin yayata
maganar aure da Sahri’ah ta zo da
shi, amma fa da sharadin hakan ya
zamanto cikin wurin da mata ne
kawai ke ciki, kuma ba tare da an
daga murya ta yadda sautin zai
ketare inda suke ba, sannan da
sharadin a samu matan su
kasance cikin cikakkiyar sutura ta
yadda wani abu na al’aurarsu ba
zai bayyana ba a lokacin rawar,
watau kamar kwabrinsu, da
damatsansu, da zira’ansu, babu
abin da za su bari a jikinsu ya
bayyana sai abin da yake da ma a
al’adance mace tana bayyanar da
shi ga yan’uwanta mata)). Intaha.
C- Sheik Bin Baz ya ce cikin
littafinsa: Majmuu’u Fataawaa Wa
Maqaalaatin Mutanawwi’ah
21/101 :-
(( ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻨﺎﺳﺐ ﺟﺪﺍ ﺗﺬﻛﻴﺮ ﺍﻟﻤﺠﺘﻤﻌﻴﻦ ﻓﻲ ﺣﻔﻼﺕ
ﺍﻟﺰﻭﺍﺝ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺑﻤﺎ ﻳﺠﺐ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻣﻦ
ﺣﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻃﺎﻋﺘﻪ ﻭﺍﻟﺘﻌﺎﻭﻥ ﻋﻞ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺘﻘﻮﻯ
ﻭﺍﻟﺘﻮﺍﺻﻲ ﺑﺎﻟﺤﻖ ﻭﺍﻟﺤﺬﺭ ﻣﻦ ﻛﻞ ﻣﺎ ﻧﻬﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
ﻣﻦ ﺍﻟﺘﺸﺠﻴﻊ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺰﻭﺍﺝ ﻭﺍﻟﺤﺚ ﻋﻠﻰ ﺗﻘﻠﻴﻞ
ﺍﻟﺘﻜﺎﻟﻴﻒ ﺣﺘﻰ ﻳﻜﺜﺮ ﺍﻟﺰﻭﺍﺝ ﻭﺍﻻﻋﻔﺎﻑ ﻟﻠﺮﺟﺎﻝ
ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ )).
Ma’ana: ((Abu ne da ya dace
kwarai da gaske a yi wa’azi wa
jama’ar da suka taru saboda
bukukuwan aure daga maza da
mata, a yi musu wa’azi a kan abin
da yake wajibi ne a kansu na
hakkin Allah da yi masa da’ah, da
taimakon juna a kan takwaa, da
kuma yi wa juna wasiyya a kan yin
gaskiya, da kuma barin sukkan
abin da Allah Ya hana yin sa,
watau: Jan hankulansu a kan yin
aure, da jan hankulansu a kan
saussauta dawainiyoyin aure
domin aure da kamun kai ya
yawaita ga maza da mata)). Intaha.
Muna rokon Allah Ya taimake mu
ya kuma tabbatar da
dugaduganmu a kan sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah.
Ameen.
Leave a Reply