HARAMUN NE A SIFFANTA WANIN ALLAH DA CEWA SHI MASANIN GAIBI NE(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

28/4/2013
Haramun ne wani mutum ya
siffanta wata halitta daga cikin
halittun Allah Madaukakin Sarki:
Mala’iku ne, ko Annabawa da cewa
shi wannan halitta masanin gaibi
ne, domin yin hakan tamkar
karyata Allah Madaukakin Sarki ne!
Hakan haramun ne saboda Allah
Madaukakin Sarki Ya ce cikin
Suratun Naml aya ta 65:-
{ ﻗﻞ ﻻ ﻳﻌﻠﻢ ﻣﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﺎﻭﺍﺕ ﻭﺍﻻﺭﺽ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﺍﻻ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻣﺎ ﻳﺸﻌﺮﻭﻥ ﺍﻳﺎﻥ ﻳﺒﻌﺜﻮﻥ}.
Ma’an: {Ka ce: Babu wanda ya san
gaibi a cikin Sammai da Kasa face
Allah, kuma ba sa sanin cewa a
yaushe ne ake tayar da su}.
Lalle akwai ayoyi da hadithai masu
yawan gaske da suke tabbatar da
wannan ma’ana ta haramta sifanta
wanin Allah da cewa shi masanin
gaibi ne.
KARIN HASKE
Amma idan wani ya ce: Ni ina da
hujjar halatta siffanta Annabi mai
tsira da amincin Allah da cewa shi
masanin gaibi ne, hujjar tawa
kuwa ita ce:-
Fadar Allah Madaukakin Sarki cikin
Suratut Takwiir aya ta 24:-
{ ﻭﻣﺎ ﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﺑﻀﻨﻴﻦ}.
Ma’ana: {Kuma shi (Annabi) ba mai
rowan gaibi ba ne}.
Da kuma fadarSa cikin Suratu Aali
Imran aya ta 44:-
{ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻧﺒﺎﺀ ﺍﻟﻐﻴﺐ ﻧﻮﺣﻴﻪ ﺍﻟﻴﻚ}.
Ma’ana: {Wannan daga labarun
gaibi ne muke yin wahayinsa zuwa
gare ka (ya kai Annabi) }.
Da wasu nassosi masu kama da
wannan to sai a ce da shi:-
Gaibin da ya zo cikin wadannan
nassosi yana nufin wahayin da
Allah Yake yi ne zuwa ga
manzanninSa, idan kuwa haka
lamarin yake to ba zai halatta ba a
siffanta su manzannin da cewa su
masana gaibi ba ne, saboda abu
biyu:-
Na farko dai: Ba ya halatta a ce
Alkur’ani zai karyata kansa da
kansa, ko kuwa zai yi karo da
junansa.
Na biyu: Da zai halatta a siffanta
Annabwan Allah da cewa su
masana gaibi ne saboda wahayin
da Allah Yake musu, wahayin da
yake dauke da hukunce-hukunce,
da kuma wasu abubuwa daban
kamar irinsu labaru, to da hakan
zai sa ya halatta a siffanta dukkan
mutumin da manzannin za su isar
masa da wannan aike da aka yi
musu da cewa shi ma masanin
gaibi ne! Saboda haka mu din nan
da muke karanta Alkur’ani mai
girma, da kuma Hadithai masu
daraja muke sanin hukunce-
hukunce da labarun gaskiya da
suke cikinsu, ke nan zai halatta a
siffanta mu da cewa: Mu masan
gaibi ne!! Ina jin kuwa babu wani
musulmi da zai yi jaraa’ar fadin
haka.
Misalin abin: Kamar shugaban
kasa ne ya fidda wata doka sannan
ya kira jami’in yada labarai a
fadarsa ya ce da shi: Jeka ka
karanta wa talkawana wannan
dokar. Sannan shi jami’in yada
labaran ya je karanta wa jama’ar
kasa dokar kamar yadda shugaban
kasa ya umurce shi.
Kun ga ai babu wani mai hankali
da zai kira wannan dokar da cewa
doka ce ta jami’in yada labarai, a’a
dukkan masu hankali suna sane
da cewa dokace ta shugaban kasa,
watau shugaban kasa shi ne mai
dokar, koda kuwa shi jami’in yada
labaru shi ya isar da ita zuwa ga
sauran talakawa.
Tun da aka fara duniyan nan har
zuwa yanzu mu halittu: —
Mala’ikunmu da Annabawanmu- ko
wannenmu yana iya sanin wasu
abubuwa sannan kuma yana iya
jahiltan wasu abubuwan, wannan
sifa ce tabbatacciya gare mu, duk
kuwa mai irin wannan sifa
haramun ne wani ya siffanta shi da
cewa shi din nan masanin gaibi
mutlaqii ne.
Allah Ya taimake mu Ya tabbatar
da dugaduginmu a kan sunnar
Annabi mai tsira da amincin Allah.
Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

3 responses to “HARAMUN NE A SIFFANTA WANIN ALLAH DA CEWA SHI MASANIN GAIBI NE(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. SHU,AIBU SANCO Avatar

    T A O

  2. Shamsuddeen Auwal Avatar
    Shamsuddeen Auwal

    AMMA AI KUN YADDA IBN TAIMIYA YASAN GAIBU KO

  3. Idris Muhammad Bakori Avatar
    Idris Muhammad Bakori

    lallai Iro Jalo! Na tabbata ka cika baqin Dan iska, Kuma Qasurgumin jahili, Shinema kake Misalta Ubangiji Da Shugaban Kasa, Kuma kake Siffanta Annabi S.A.W Da danjarida, kuma garkake Qara danganta ANNABI S.A.W Dasiffar Jahilci, Uwarka Tayi Asarar Haihuwarka, Tokasani Ba ANNABI ba Sahabima Allah Yasanar Dashi Gaibu.
    Allah Yaqara Dulmiyar dakai dajama’arka cikin Qiyayyar Sayyadis Saqalaini S.A.W

Leave a Reply to Idris Muhammad BakoriCancel reply

Latest updates
Categories