Hukuncin Ajnu(Dunƙule Hannu) yayin Tashi daga Jalasatul Istiraha

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Tambaya: Menene Hukuncin yin Ajnu a Sallah? dunƙule hannu yayin miƙewa daga zaman Jalasatul istiraha?

Amsa: Hadisin da yazo kan wannan Mas’ala akwai tsaɓanin Maluma kan ingancin sa, Wasu maluman suna ga hadisin bai inganta ba, Kaman su Ibnus-Salah da Ibnu Rajab, da Imamun-Nawawy Allah yayi musu Rahama. Amma Sheikh Nasiruddin Albany ya inganta Hadisin kamar yadda ya kawo acikin Littafin sa na Sifatu Salatin-Nabiy.

Abinda kuma yafi inganci shine Rashin ingancin Hadisin.

Mai son neman ƙarin Bayani zai iya duba Littafin marigayi Sheikh Bakr Abu Zaid Allah yayi masa Rahama da yayi bayani kan raunata wannan Hadisi.

Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates