Tambya: Shin ya halatta mutum ya ambaci Allah, ko yayi wa Annabi Salati ko ya karanta Al’qur’ani alhali ya a da janaba?
Amsa: Baya Halatta a karanta Al’qur’ani matuƙar mutum yana da Janaba sabida an rawaito daga Aliyu Bin Abi dalib Allah a kara masa yarda yace:
Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yana karantar damu Alquráni a kowani yanayi, matukar bashi da janaba.
Sunan Abi Dawud: 212, Sunan ibn Majah: 598
Haka nan an rawaito Umar Radiyallahu anhu yana ƙin karanta Al’qur’ani alhali yana da janaba
Musannaf Abdurrazzak: 1307
Amma game da zikiri da salatinn Annabi yanayi da yafi shine Mutum yayi su yana da tsarƙi, amma kuma babu laifi idan mutum yayi bashi dashi. Sabida an Rawaito daga Aisha Allah ya ƙara mata yarda tace:
Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance yana ambaton Allah a dukkan yanayinsa
Sahihu Musulim: 373
Wannan hadisi yana nuna cewa A kowani yanayi Annabi yana Ambaton Allah ba’a keɓance wani yanayi ba. Sabida haka ne maluma suka tafi kan cewa ya halatta ga mai janaba ya ambaci Allah.
Hakanan game da ambaton Allah da ya ƙunshi ayoyin Alkur’ani don neman kariya, kaman karanta ayatul kursiyyu ga wanda zai yi bacci shima babu laifi.
Allah yasa mudace.
Domin tura taka tambayar danna nan
Leave a Reply