By Dr. Ibrahim Jalo.
kullum Ahlus Sunnah wal Jama’ah a duk inda suke suna gina addinsu ne a kan abin da ya tabbata daga Alkur’ani Mai girma da kuma ingantattun hadithan Annabi mai tsira da amincin Allah masu daraja. Amma sabaninsu su kan gina addininsu ne kawai a kan abin da ya dace da son zuciyarsu.
Wani dan’uwa ya yi tambaya game da mas’alar da ya kamata a ce kusan yawancin al’ummar Musulmi suna sane da cewa tana rubuce cikin Alkur’ani mai girma cikin suratul Ma’idah, wannan kuwa ita ce mas’alar cin abinci ko yankan Ahlul Kitabi, watau Kafurai Yahudawa, da Kafurai Kiristoci.
Domin takaita amsar wannan tambayar za mu kawo maganar da biyu daga cikin manyan malaman duniyar Musulunci suka fada game da mas’alar.
(1) Ya zo cikin littafin fatawa na Sheik Bin Baz Shugaban majalisar malamai ta kasar Saudia a zamanin shi, littafin shi mai suna Majmu’u Fatawa Ibni Baz 5/396 kamar haka:-
((س: هل يجوز اكل ذبائح النصارى في زماننا الحاضر، علما بتعدد طرق الذبح لديهم كاستخدام الماكينات والمواد المخدرة في عملية الذبح؟
ج: يجوز اكل ذبائحهم ما لم يعلم انها ذبحت بغير الوجه الشرعي؛ لان الاصل حلها كذبيحة المسلم لقوله تعالى: وطعام الذين أوتوا الكتاب حل لكم وطعامكم حل لهم)).
Ma’ana: ((Tambaya: Ko cin yanke yanken Kiristoci a wannan zamani namu na yau yana halatta, duk kuwa da cewa hanyoyin yanka a wurinsu sun yawaita, watau kamar yin amfani da injuna, da kuma abubuwa masu daskarar da kwakwalwa a wurin yankan?
Jawabi: Cin yanke yankensu yana halatta, matukar dai ba a san da cewa an yanka tabbar ba ne ta hanyar da ba ta dace da Shari’a ba, saboda asalin lamari shi ne halaccinsa, kamar dai yankan musulmi, saboda fadin Madaukaki: Da abincin wadannan da aka ba su littafi halal yake gare ku, kuma abincinku halal yake gare su)).
(2) Sheik Uthaimeen ya ce cikin littafinsa Ash-Sharhul Mumtii 12/148:-
((فالحاصل: ان الذي عليه جمهور اهل العلم ان من تدين بدين اهل الكتاب وانتسب اليهم ولو كان يقول بالتثليث فانه تحل ذبيحته، ويحل نكاحه)).
Ma’ana: ((A takaice dai: Abin da majoratin masu ilmi suka ce shi ne duk wanda ya yi Addini da addinin Ahlul kitabi, ya kuma danganta kansa zuwa gare su koda kuwa yana cewa Allah uku ne, to lallai wannan cin yankan shi halal ne, kuma auren shi halal ne)).
Allah muke toko da Ya taimake mu. Ameen.
Leave a Reply