Tambaya: Shin ya Halatta Mutum ya keɓance ranar Juma’a da yin Azumin?
Amsa: Makruhi ne(anƙi) Mutum ya keɓance Ranar Juma’a da yin azumi sai dai in ya dace da wata rana da mutum yake Azumi acikinta. Misalin mai yin azumin Annabi Dawuda Alaihissalam. Yayi azumi yau, yasha gobe, sai Juma’a ta dace da ranar Azuminsa, toh anan babu laifi yayi.
ko kuma ya dace da wasu ranaku da ake Azumtarsu toh anan ma babu laifi mutum ya azumce su koda ko sun dace da ranar Juma’a.
Misali a wannan Shekara ta 1443H. Ranar Arafah ta dace da ranar Juma’a, shin mutum zai iya Azumtar wannan Rana?
Ƙwarai babu laifi mutum zai iya Azumtar wannan Rana ta Arafah duk da cewa ta dace da Ranar Juma’a. Amma da mutum zai haɗa Azumin da ranar Alhamis da yafi, Domin Hakan zai sa ya dace da Abubuwa uku.
- Dacewa da Sunnar azumin ranar Alhamis
- Dacewa da Azumtar ranar Arafah
- Bai keɓance Ranar Juma’a da Azumi ba.
Leave a Reply