Tambaya: Shin ya Halatta na miji yayi limanci wa mata su kaɗai?
Amsa: da farko babu tsaɓani kan limancin na miji ga maza da mata, sai dai matan zasu tsaya a baya, nesa da maza. Domin mafi alherin sahu ga mata shine baya kamar yadda aka rawaito daga Annabi Muhammad Tsira da Amimcim Allah su tabbata a gare shi Sahih Muslim: 440
Na biyu: Baya halatta ga na miji ya jagoranci mace Sallah ita kaɗai wacce ba muharramansa ba domin hakan yana shiga ƙarƙashin keɓance wa da Ajnabiyya(wanda ba muharrama ba) wanda Haramun ne a Musulunci.
Na uku: Ya halatta ga na miji ya jagoranci mata Sallah idan suna da yawa. Wasu maluman kuma suna ga yin hakan Makruhi ne idan babu wani na miji a tare dashi. Amma wasu maluman sun tafi kan cewa ya halatta matuƙar An amince duk wata fitina.
An tambayi Sheikh Bin Baz Allah yayi masa Rahama game da Irin wannan Tambaya sai yace:
Ƙwarai ya Halatta na miji ya jagoranci mace a Sallah ko Tarawihi. Annabi ya kai ziyara gidan su Anas Bin Malik yayi Sallah tare da Anas da Wani Maraya. Suka tsaya a bayan shi sannan Ummu Sulaim ta tsaya a bayan Su Anas.
Haka nan mata sun Kasance suna Sallah a Masallacin Annabi a zamanin sa. Haka nan a bayan sa.
Babu laifi ga mata suyi sallah a bayan Limami koda kuwa su kaɗai ne a bayan shi babu Maza. domin keɓance wa wanda yake Haram yana kasancewa ne idan mutum ya keɓance da mace ita kaɗai, amma idan suka kai su biyu yayi sama to babu laifi.
Domin Karanta Nassin amsar da Sheikh Bin Baz ya bayar kan wannan tambaya danna nan
Sabida haka: ya halatta ga namiji ya jagoranci mata Sallah matuƙar ba’a tsoron wata fitina. Domin asali shine halaccin namiji ya jagoranci mata da maza a Sallah. Haramci yana buƙatar dalili.
Allah shine mafi sani.
Leave a Reply