Tambaya: Shin ya Halatta a rantse da wanin Allah? Misali Mutum yayi ranstuwa da Annabi ko mala’ika?
Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.
Rantsuwa da wanin Allah Haramun ne, baya Halatta musulmi ya rantse da wani sai Allah maɗaukakin sarki.
Dalili: Ibnu Umar Allah yaƙara musu yarda ya rawaito Hadisi daga Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi.
Annabi ya riski Umar acikin tawagan matafiya yana rantsuwa da Mahaifinsa, sai Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ƙira su yace: Ku saurara; Lallai Allah yana hana ku ku rinƙa rantsuwa da iyayen ku, wanda zaiyi rantsuwa to ya rantse da Allah ko yayi shiru.
Sahihul Bukhari: 6646. Muslim: 1646
A wannan Hadisi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana su yin rantsuwa da Iyayen su, sannan ya umarce su idan zasuyi rantsuwa su rantse da Allah wannan yake nuna haramcin yin rantsuwa da wanin Allah. Domin umarni yana nuna wajabci.
Sannan an rawaito daga Umar ɗan khaɗɗab Allah ya ƙara masa yarda Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
Wanda yayi rantsuwa da wani abu koma bayan Allah to yayi Shirka.
Ahmad: 329.
A taƙaice: Rantsuwa da Wanin Allah haramun ne, kuma Shirka ne ƙarami. Duk wanda zaiyi rantsuwa to ya rantse da Allah. Ba’a rantsuwa da ka’aba, ko Annabi, ko Mala’ika da makamantansu. Ana rantsuwa ne da Allah shi kaɗai.
Allah shine mafi sani.
Leave a Reply