As-salamu alaikum.
Haram ne a yi kowace mu’amala mai zama ƙarfafawa ga aikin zunubi da mai yinta kai tsaye.
AL-MUGNY; 4/154, MA’DA’LIBU ULIN NUHA; 3/607
Aya ta biyu a Su’ratul Ma’ida ita ce gimshiƙin kowace mu’amala:
وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ.
Allah Mađaukaki Ya ce:
Ku Taimaka A Kan Ayyukan Kirki Da Kiyaye Dokar Allah, Kuma Kada Ku Taimaka A Kan Ayyukan Zunubi Da ƙetare Iyakokin Allah
Kowace Mu’amala Mai ƙarfafa ma ayyukan zunubi haram ce. [AL-MUHALLA; 7/522]
Leave a Reply