Hukuncin Tsintuwa da yadda akeyi da ita

Danna nan domin shiga karatu Online

Maqala

Tambaya: Idan mutum ya samu kuɗi a hanya a ƙasa shin ya Halatta ya ɗauka?

Amsa: Tsintuwa ya rabu kashi uku.

Na farko: Tsintuwan abinda bashi da ƙima mai yawa, kamar tsintuwar Sanda, ko wani abin sha kaman lemu misali, ko Biredi misali. Ko irin tsintuwar naira ashirin. Dai duk abinda a al’adance an san mai ita bazai damu da ita ba idan ta ɓace. To idan mutum ya tsinci irin wannan abu to zai yi amfani dashi babu laifi. Saboda Hadisin da Abu dawud ya rawaito

Annabi yayi rangwame game da tsintuwar sanda, ko igiya ko makamancin su. Wanda ya samu yayi amfani dasu

Abu Dawud: 1717. (Sheikh Nasirud-din Albani ya raunata Hadisin.).

Na biyu: abinda idan aka barshi bazai salwanta ba har mai shi yazo ya same shi. Kaman raƙumi, ko kujera, da makamantansu. Shi wannan baya halatta a ɗauka. Domin an tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da tsintuwar Raƙumi sai yace:

Ina ruwanka da ita? Tana tare da ruwan shanta da abinda zai tsare mata ƙafafun ta, tana zuwa wurin ruwa tasha, sannan tana cin bishiya har ta kai ga mai ita

Sahihul Bukhari: 2372

Wannan Hadisi yana nuna cewa ba’a tsintuwar raƙumi ko wata dabba da zata iya komawa zuwa ga mai ita.

Ya shiga ƙarƙashin wannan hadisi duk wani abu da idan aka barshi mai shi zai iya zuwa ya ɗauki kayansa ba tare da wani matsala ba kamar yadda mukayi bayani a baya.

Na Uku: dukiya da zata iya salwanta idan aka barta, kaman Rago ko akuya da makamantansu. Ko kuma sauran dukiyoyi kaman kuɗi na takarda, ko zinari ko azurfa.

Idan abinda aka tsinta dabba ne kaman rago ko akuya to wanda ya same ta zai yi ɗayan abubuwa uku:

  • Ko ya yanka yaci naman. Amma idan mai ita ya dawo zai biya shi kuɗin dabbar
  • Ko ya siyar da dabbar ya ajiye kuɗin duk randa aka samu mai ita sai ya bashi
  • Ko ya ajiye ya cigaba da kiwon dabbar har randa Allah zai kawo mai shi. Idan ya ɗauki lokaci mai yawa yaga bazai iya cigaba da ajiya ba to sai yayi amfani da ɗayan hanyoyi biyun farko.

Idan kuma dukiyar da ya samu kuɗi ne to zai ajiye. Yasan yawan kuɗin da yanayin kuɗin sannan yayi shela wa mutane. Zai yi ta sanar wa har na shekara guda. Idan akayi shekara guda ba’a samu mai shi ba to sai yayi amfani da shi ko ya bada sadaƙar sa. Amma idan mai dukiyar ya dawo yana nemanta to zai biya shi.

An rawaito daga Annabi an tambaye shi game da tsintuwa sai ya umarci wanda yayi tsintuwa da ya san siffar abinda ya tsinta idan kuɗine misali to yasan yawan kuɗin sannan yasan yanayin kuɗin ta yadda idan mai shi yazo yayi bayani da ya gamsu cewa nashi ne sai ya bashi. Sannan sai ya nemi mai ita har tsawon shekara guda. Idan bai samu mai ita ba to sai yayi amfani da dukiyar ko ya bada sadaƙa. Wannan Hadisi Bukhari ya rawaito shi a hadisi na 2372.

Ya kamata mu lura da abubuwa kaman haka:

  • Kafin mutum ya ɗauki tsintuwa dole sai ya aminta da kansa cewa zai nemi mai dukiyar, sannan kuma zai kiyaye dukiyar har a samu mai ita. Idan yasan bazai iya haka ba to haramun ne ya ɗauki wannan tsintuwa.
  • Dole yasan adadin kuɗin ko nau’in Dukiyar kamar yadda hadisin da muka kawo a sama yayi bayani.
  • Dole idan ya ɗauki dukiyar yayi shela ya nemi mai ita. Zaiyi shelan ne kuma da yanayi da ya dace da zamanin sa. Misali ko ta gidan rediyo ko ta waya da makamantansu.
  • Idan mai dukiyar yazo kuma ya siffanta dukiyar daidai to dole a miƙa masa dukiyar sa.
  • Idan ba’a samu mai dukiyar ba to wanda ya samu ta zama tashi. Ko yayi sadaƙa da ita ladan ya kai ga mai dukiyar ko kuma yayi amfani da ita. Amma idan mai dukiyar ya dawo zai mayar masa da dukiyar sa.

Wannan shine taƙaitaccen hukuncin Tsintuwa. Allah yasa mudace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates