Hukuncin Rarraba Zakka ko bada shi ga Mutum daya

Danna nan domin shiga group na karatu Online

An Tambayi Sheikh Muhammad Bin Salih Al-Uthaymeen

Mutum ne Zakkarsa Riyal Dubu ɗaya, sai ya raba shi kan mutane ɗari, kowa yana da Riyal goma, shin hakan yafi, ko kuma ya baiwa mutum ɗaya, ko ya raba wa mutane biyu?

Amsa

Abin lura wurin bada zakka shine amfani, duk Tsarin da yafi amfani shi za’ayi amfani dashi, idan ya zamo talauci ya game mutane, to babu shakka a raba ta ga fiye da mutum ɗaya shi yafi dacewa, amma idan ya zamo talauci bata game mutane ba, to baiwa mutum ɗaya ko mutane biyu shine yafi dace wa, Domin riyal goma a wannan zamanin mun ba komi bane, ba kamar a baya ba. Saboda haka idan Mutum zai bada zakka sai ya duba wanne yafi.

Wanna Fassara ce ta Amsar Sheikh tare da sarrafa Magana,r a Duba Majmu’u fatawa wa rasa’il na Sheikh Muhammad Bin Salih Al-Uthaymeen Mujalladi na 18, Kitabu Ahlizzakat.

Ƙarin Bayani

Kamar yadda muka sani ne cewa ita zakka ana tafiyar da ita ne cikin abubuwa takwas wanda Allah ya lissafa su acikin Suratut-Taubah Aya ta 60.

{ ۞ إِنَّمَا ٱلصَّدَقَـٰتُ لِلۡفُقَرَاۤءِ وَٱلۡمَسَـٰكِینِ وَٱلۡعَـٰمِلِینَ عَلَیۡهَا وَٱلۡمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمۡ وَفِی ٱلرِّقَابِ وَٱلۡغَـٰرِمِینَ وَفِی سَبِیلِ ٱللَّهِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِیلِۖ فَرِیضَةࣰ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِیمٌ حَكِیمࣱ }

A zamanin Annabi da zamanin khalifancin Musulunci shugaba shi yake tattara zakka ya raba ga wanda ya cancanta daga cikin wa’innan Abubuwa takwas, Amma bayan faɗuwar khilafa ƙasashen Musulmi kowa ya koma cin gashin kansa, sannan musulunci ya yaɗu ya shiga wasu ƙasashe da ba na Musulmai ba sai ya zamo wasu ƙasashen Musulman suna da Tsarin tattara Zakka kamar yadda take lokacin khilafa, sai dai basu wajabta wa kowa sai ya kawo nashi, in mutum ya ga dama ya cire ya kai musu, in yaga dama kuma ya cire ya raba da kansa, wasu ƙasashen ma babu irin wannan tsarin baki ɗaya.

Saboda haka ya rage ga Mutum ya Zaɓi tsarin da zai raba Zakkar sa, ko dai ya baiwa gwamnati a ƙasashen da akwai wannan tsarin, ko kuma ya cire da kansa ya raba.

duka wannan ya halatta, sai dai in zai raba da kansa ne sai ya duba Maslaha, idan ya zamo ana talauci da yawa to sai ya raba dukiyar yadda ya dace, ba wai kuma kamar yadda wasu sukeyi ba, ya raba Naira dubu dubu wa mutane, wannan bai dace ba, domin Naira dubu babu abinda zai yi. A misali mutum zakkar sa Dubu ɗari biyu ne to babu laifi ya raba ta ga mutane Biyar ko goma.

Aƙalla kowa ya sami Naira dubu ashirin, saboda hakan zai taimaka wurin daƙile talauci a tsaƙanin mutane, domin wani zai iya amfani da wannan kuɗin wurin fara ƙaramar sana’a. Amma idan aka raba dubu dubu ga mutane masu yawa kowa zai cinye nashi cikin ƙanƙanin lokaci. Sai dai in Annoba ce ta sauƙo wa Mutane ta yadda kowa yana buƙatar gudunmawa. Allah yasa mu dace.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories