Hukuncin wanda ya kashe mutane bisa kuskure

Danna nan domin shiga karatu Online

Tambaya: Menene Hukuncin Direban da ya bige mutane biyu ko fiye da biyu bisa kuakure?

Amsa: Da sunan Allah Mai Rahama mai jin ƙai.

Kashe rai yana daga cikin mafi girman laifuka. Saboda haka ne Allah maɗaukakin sarki yayi narkon azaba ga wanda ya kashe rai da gangan.

Allah maɗaukakin sarki yace:

Wanda ya kashe mumini da gangan sakamakonsa itace wutar jahannama, zai dawwama acikinta, Allah yayi fushi dashi, Allah ya tsine masa, kuma yayi masa tanadin azaba mai raɗaɗi.

Suratun-Nisa: 93

Amma idan anyi kisan ne bisa kuskure to hukuncin sa gashi kamar haka.

Na farko shine diyya, sannan sai kaffara.

Wanda yayi kisan da Yan uwansa su zasu biya wannan diyya gwargwadon yadda ƙimar diyya take a lokacin da akayi kisan.

Bayan Haka sai kaffara.

Kaffara kuma shine a ƴanta bawa ko baiwa mumina, ko ayi azumin wata biyu a jere.

Tunda yanzu babu bayi abinda ya rage shine mutum yayi azumin watanni biyu ajere.

Dalilin wannan Kaffara kuwa shine faɗin Allah a ƙarshen Aya ta 92 ta cikin Suratun-Nisa’i.

Wanda baisamu ba to yayi azumin watanni biyu a jere domin ya samu tuba daga Allah, lallai Allah ya kasance masani mai hikima

Suratun-Nisa’i aya ta 92.

Ma’ana wanda bai samu bayi ba.

Saboda haka abisa tambayar da kayi idan Mutum ya bige mutane biyu ko fiye da biyu bisa kuskure to ko wanne daga cikinsu za’a biya diyyarsa kuma za’ayi masa kaffara.

Saboda haka idan mutum ya kashe mutane biyu bisa kuskure zaiyi azumin wata huɗu kenan a jere, kowani mutum zaiyi masa azumin wata ɗaya.

Yazo acikin Littafin kasshaful Qina’ na Hanabila sukace:

Idan mutum ya kashe jama’a da yawa dole dole zaiyi musu kaffara duka

6/83

Wannan Shine a taƙaice, Allah shine mafi sani.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates