Hakika Allah taala ya girmama dan Adam ya martashi, ya bashi hankali da basira, da hikma, da azanci, da sanin ya kamata,
Hankali babbar niima ne, da wadata da ya kamata a kiyaye shi, a aiwatar dashi, inda ya dace,
shan kayan maye, da kayan marisa, da buguwa, wanda yake yaduwa tsakanin matasa maza da mata, wanda hakan yake barazana, ga tabarbarewar tarbiyya, da rugujewar al’umma ta gari, abune na takaici da Allah wadai,
Acikin shan kwaya akwai matsaloli da suka shafi yawan rigima, tashin hankali, daru, rigima, tarzoma, fitintunu, kashe-kashe, akwai barazana da kayan maye sukeyi ta bangarori kamar haka :
1-Addini wanda ya haramta haka kuma yaja kunne
2-Hankali, wanda yake gushewa, sakamakon shan kayan maye
3- Yan uwa da Dangi, wanda mashayi, yake cutarwa
4- Tattalin Arziki, wanda yake fuskantar matsala sakamakon shan kayan maye
5- lafiyar jiki,
6- al’ummar da kayan maye ya mamaye matasan ta, suna cikin matsala babba
7- tsaro, da zaman lafiya da kwanciyar hankali
A ganinku manene ya jawo yaduwar kwayoyi da kayan marisa, suka mamaye rayuwar matasa kuma ina mafita ?
Leave a Reply