Allah maɗaukakin sarki ya halicci bayinsa, kuma ya ɗaura wa kowa irin aikin da ya dace dashi wanda zai iya. Yana daga cikin nauyi da Allah ya ɗaura wa bayinsa kula da iyalai wurin basu abinci da kuma tufatar dasu da kuma kula da kiwon lafiyarsu da sauran ayyukan kulawa da Allah ya ɗaura wa Namiji. Wanda wannan aiki wajibi ne akansa yayi su, in yayi yana da lada, inkuma ya ƙiyi yana da zunubi kuma Allah zai tambayeshi ranar tashin Al-Qiyama.
Yana da kyau mai gida ya sani cewa: Allah ya ɗaura masa nauyin kula da iyalansa baki ɗayansu, kuma dole ne ya samar musu abinda suke da buƙata wanda zasu rayu dashi gwargwadon iyaka, babu almubazzaranci, babu Maƙo. Mutum yayi iya ƙoƙarin sa wurin baiwa iyalansa abinda suke buƙata gwargwadon arzikin da Allah yayi masa.
Bai dace ba Allah yayi maka buɗi Amma kuma kaƙi yalwata wa iyalanka.
Haka nan bai dace ba kayi watsi da iyalanka kaƙi kula dasu baki ɗaya.
Haka nan bai dace ba ka rinƙa yi wa iyalanka gori domin kana ciyar dasu. Wannan haƙƙinsu ne akanka wanda Allah ya ɗaura maka kuma dole ka bayar.
Haka nan Mai gida ya sani cewa Ciyar da iyalansa da biya musu buƙatunsu na yau da kullum babu abinda zai janyo masa sai ƙarin Arziƙi. Domin shi Arziƙi baya raguwa sabida Sadaqa. Haka nan ya sani wannan ibada yake yi, sai ya tsarkake Niyya yayi don Allah domin Samun lada.
Ya kamata mu lura cewa: wannan Iyalai da Allah ya bamu Kiwo ne kuma Amana, Allah zai tambayemu yaya muka gudanar da wannan kiwo. Shin munyi shi da kyau ko kuma munyi sakaci wurin yin wannan kiwo har abinda aka bamu kiwo ya salwanta?!
Allah ya sa mudace, ya kuma bamu daman kula da iyalanmu.
Leave a Reply