Jami’an Tsaro Suka Kashe Sheikh Albani —Zakzaky(Leadership Hausa)

Danna nan domin shiga karatu Online

Mako guda bayan wasu mahara da ba a san ko su waye ba, sun harbe Malamin addinin Musuluncin nan da ke Zariya, Shaikh Awwal Albani, matarsa da dansa, sai kuma ga shi, ’yan Shi’a, sun yi zargin ana yunkurin harbe Shugabansu, Shaikh Ibraheem Yakoub Zakzaky.
A cikin wani jawabi da ya gabatar ga almajiransa a wajen karatun da ya saba gabatarwa kowace ranar Litinin a cibiyarsu da ake kira Husainiyya Bakiyyatullah da ke Sokoto Road Sabon Garin Zariya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya yi zargin an tura jami’an tsaron ne don su kai masa hari a gida da yake kwana ranar Asabar.
“Waccan Asabar din kun yi kisan kai a wajen Gaskiya, kuma wanna Asabar din an gan ku a Gyallesu. Wa kuka zo kashewa ke nan? Ai ma ba sai an ba ka bayani ba, da ganin su a Gyallesu ka san sun zo kashe wani ne”, in ji Shaikh Zakzaky a jawabinsa nasa.
A daren ranar Asabar ne aka ga wani gungun jami’an tsaro sun kakkafa shingayen suna binciken ababen hawa a daidai hanyar shiga Gyallesu, Zariya, Unguwar da Shaikh Zakzaky ke zama da iyalansa. Nan take almajiransa suka hallara a wajen.
Wasu da muka zanta da su a wajen sun yi zargin jami’an tsaron sun je wajen da wata manufa. Yayin da wasu suka yi zargin jami’an tsaron sun zo binne makamai ne, wadanda za a nunawa duniya a ce da su aka kashe Shaikh Awwal Albani, wasu kuwa cewa suka yi an zo kamawa ko kuma kashe Shaikh Zakzaky ne.
“Ba mu san abin da ya kawo su a daidai wannan lokacin ba, shi ya sa muka kasance a nan domin duk abin da za a yi ya zama a kan idonmu aka yi shi”, in ji daya daga cikin daliban Malamin a lokacin yake zantawa da Wakilinmu ta wayar GSM.
Wata majiya mai tushe da ke da alaka da jami’an tsaro ta tsegunta mana cewa an kawo su Unguwar Gyallesu a daidai wannan lokacin ne, saboda wani rahoton sirri da suke da shi na yunkurin kai wa Madugun na ’yan Shi’a hari da ake tsammanin wasu gungun mutane za su yi.
A cikin jawabin nasa, Shaikh Zakzaky ya nanata cewa suna da masaniyya game da shirin da ake da shi na kai masu hari a ranar Litinin ko Laraba; ranakun da ya saba fita don gabatar da Tafsiri da kuma karantun littafin Nahjul Balagha. “Sun dai ce za su yi Litinin, idan ba su yi ba ko wata rana idan an tashi karatu daga Husainiyyah, ko in za a zo Husainiyya za su bude wuta”, In ji shi
Wannan dai ba shi ne karon farko da almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka yi zargin ana yunkurin kashe Malamin nasu ba. Wata majiya ta shaida wa Wakilinmu cewa wannan shi ne karo na 24 a cikin shekaru uku da aka yi yunkurin kashe shi.
Sun yi zargin cewa hatta tarurrukan Maulidin Manzon Allah (SWA) da suka gabatar a garuruwan Kano da Zariya, sai da aka shirya auka masu. Kuma da suka yi Tattaki a lokacin juyayin kwanaki 40 Ashura da suka yi a watanni biyu da suka gabata sun zargin an shirya auka masu.
“Saboda haka wannan ma da suka ce za su zo su zuba makamai a Gyallesu ba don mun gan su ba, ba za mu fada ba (don ba magana ba ne). To amma sai suka yi yunkurin yi. Sun sha yin ‘attempt’, kuma mukan wuce, kuma ba ma fada. Ko a wani ‘Usulubil Wahda’ wata ranar Juma’a lallai sun ajiye masu harbi, kuma mun zo ko magana ma ba mu yi ba”, in ji shi.
Shaikh Zakzaky, wanda ya nisanta kansu daga duk wani zargi da wasu suke yi masu na hannu a kan kashe Shaikh Awwal Albani, ya tabbatar da cewa a iya saninsu babu wata rashin jituwa da ta taba shiga a tsakaninsu da Marigayin har zuwa lokacin da wasu maharan da ba a san ko su waye ba suka kashe shi; “Iyakar saninmu Albani har suka kashe shi bai taba kashe kazarmu ba, ko ya fasa kwanmu ba. Ko kuna da labarin ya taba kashe mana kaza? To ga wanda suka bude mana wuta rana tsaka mun san su, wa muka kashe a cikin su?”
Acewarsa, almajiran Albani sun san wadanda suka yi kisan, amma saboda tsoro ba za su iya fitowa fili su fada ba, don haka “ba tare da tsoron duk wani mahaluki ba, mun fadi cewa gwamnat ce ta kashe Albani”. In ji shi.
Ya jaddada cewa su ba sa rike kowa a zuciya don ya yi masu wani abu da ba daidai ba; “To inda mu masu kisan kai ne ai da mun kashe wadanda suka bude mana wuta rana tsaka, amma har muna hannu da su, wadanda suka ba da umurnin aka bude wuta a kanmu rana tsaka mun san su, sun san mun sani, amma har muna hannu da su”.
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya nesanta Shi’a daga duk wani nau’i na ayyukan ta’addanci domin a cewarsa, su Shi’a suna da ka’ida kafin su yi duk wani abu “a wajen Shi’a babu yadda za a yi ka mari mutum ba da sai izinin Mujtahidi (Ayatullahi) ba, balle kuma ka auka wa mutane da yaki. Saboda haka, horo wanda za a ji zafi ‘ittifakan’ ba a yi sai da izinin Mujtahidi, ballantana kisa. Horo wanda za a ji zafi ko da duka ne, mutum ba zai yi ba sai da izinin Mujtahidi, wannan a duk duniyar Shi’a haka yake ba a sabani, babu ra’ayi na biyu”.
A baya dai garin Zariya ya kasance mai zaman lafiya da aminci ga bako ga dan gari, inda ya kasance Cibiyar ilimi ta Nijeriya, amma yanzu bisa ga dukkanin alamu an jefa tsoro da razani a zukatan mazaunansa; inda jama’a daban-daban ke tambayar cewa “ko wane ne zai iya bugan kirji ya ce zai amfana da wannan rashin tabbas da wasu ke neman jefa garin a ciki?”.
Original Article

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “Jami’an Tsaro Suka Kashe Sheikh Albani —Zakzaky(Leadership Hausa)”
  1. Abdullahi sadiq Avatar

    Haryanzu bamu san wanda.yakashemuna.malamba?kusuwane susani fa.sufito suyi jahadi fisabilillah.saboda sheik muhammad auwal adam baygazaba.sannan yashammace duniya.saboda yazan tauraruwa.chikin duniya.

  2. Haruna Mukhtar Avatar
    Haruna Mukhtar

    Hhhhhmmm haka komai ke faruwa kuma yake wucewa haka watarana muma zamu wuce da wanda yaso mutuwar Albani dawanda yaji dadin mutuwar dawanda yadauki nauyin mutuwar dawanda sukasan da shirin mutuwar dawanda suka ribaci mutuwar don wani buri nasu damu damuke jimamin mutuwar dikkanmu muma zamu mutu Amma kowadaga cikinmu mu masoya muduba mugani muna aiki da abinda malan yakarantarda duniya na ilimi? Kumasu farinciki damutuwarsa kuduba shinkunkai matsayinda Allah yakaishi na ilimi dana rayuwa ? Ku wainda kuka kashe malan kodon wane daliline shin burinku yacika? Ku wainda kuka dauki nauyin kisan malan shin kunshirya shara.a dashi gaban Allah kuwa? Kuma masu fada da da.awar shin mutuwarsa ta dakatarda da.awar kokuwa ?

    Allah yajikan malan yakai haske kabarinshi yakarbi kyawawan Ayyukanshi yayafemasa kurakuranshi yasakamishi zaluncinshi da akayi yakarbi shahadarshi yakeutata makwancinshi yahadashi da megidanshi ya Albarkaci zuri.arshi mukuma yabamu wani malamin koda makamancishne munsani bawani abu da zegagari Allah

Leave a Reply

Categories
Latest updates