Ramadaniyyat: 1444 (7) – Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Ramadaniyyat: 1444 (7)

‘Yan Mazan Jiya: Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya, Malami Na Allah (7)
Ci gaba…..

  1. Ban da darasi na kowa da kowa da yake gabatarwa a babban Masallacin Juma’a, Ibn Taimiyya kuma yakan keɓance wasu daga cikin ɗalibansa masu ƙwazo ya yi musu darussa na musamman, inda yake bayyana musu wasu mas’alolin ilimi masu zurfi. Yakan kuma samu wani lokacin na daban domin rubuta littattafai ƙanan da manya da kuma amsa tambayoyin da ake rubuto masa daga wurare da daban-daban don neman ƙarin bayni a kan wasu batutuwan addini. Yakan bayar da amsoshinsu a rubuce, daga nan kuma duk abin da ya rubuta sai ya watsu ko’ina.
  2. Daga nan ne rigimarsa da abokan hamayyarsa ta fara. Masana tarihi sun bayyana cewa, wasu mtuane daga garin Hamah na ƙasar Sham sun rubuto masa tambaya game da ma’anar faɗar Allah: “Mai Rahma ya daidaita a kan Al’arshi”, bayan kuma ya ce: “Kursiyyinsa ya yalwaci sama da ƙasa” da sauran batutuwa. Sai ya rubuta musu wani littafi da ake kira daga bisani ‘Al-Hamawiyya’ wanda yake ƙunshe da amsosin tambayoyinsu. A cikinsa ne ya tabbatar da cewa, ba a tawilin ‘daidaton Allah a kan Al’arshi’, ya tabbatar da cewa Allah ya daidaita daidaiton da ba mu san yaya yake ba, daidaito ne wanda ba irin na fararrun halittunsa ba. Kursiyyinsa ma ba irin na fararrun halittunsa ne ba. Hakanan ya tabbatar musu da irin wannan magana game da duk wata aya ko hadisi da aka ambaci Allah yana da Fuska ko Hannu. Ya yi waɗannan bayanai duk a cikin littafinsa ‘Al-Hamawiyya’, bayanin da ya saɓa wa Mazhabar Ash’ariyya wadda wasu shugabanni da mutane gari suke yi wa ra’ayin riƙau.
  3. Wasu malamai da yawa suka yunƙuro domin fafatawa da shi, to amma ina! Ba inda suka kai wa, domin ba su da ƙarfin hujjoji irin nasa. To da abu ya gagare su sai suka kai ƙararsa wajen Alƙalin Mazhabar Hanafiyya, wai don ya ɗau hukunci a kansa.

Ibn Kasir Yana Ba Mu Labari:

  1. Almajirinsa Ibn Kasir a littafinsa ‘Al-Baidaya Wan-Niyahaya’, cikin labarin abubuwan da suka faru a shekara ta 698 ya ba mu labari cewa: “Wasu taron jama’a sun yunƙuro wa Ibnu Taimiyya suna son kai shi gaban alƙalin Mazhabar Hanafiyya Jalaluddini, to amma sai ya ƙi halartar majalisin. Aka yi shela a gari cewa a kamo duk waɗanda suke yaɗa aƙidar da ya rubuta wa mutanen Hamah, sai yawancinsu suka gudu suka ɓoye, aka kama wasu masu yaɗa aƙidar aka yi musu bulala, wasu kuma suka ji tsoro suka ja bakinsu suka yi shiru. Ranar juma’a Ibnu Taimiyya ya fita ya gabatar da darasinsa kamar yadda ya saba, inda ya gabatar da tafsiri a kan faɗar Allah: “Lalle kai kana kan halaye masu girma”. [Alƙalam, aya ta 4]. Washe gari Assabar kuma ya je wajen Alƙalin Shafi’iyya, Imamuddin, ya haɗu da wasu malamai a majalisarsa, suka tattauna da shi a kan littafin ‘Al-Hamawiyya’, suka yi masa tambayoyi a kan wasu wurare daga cikinta, ya kuma ba su amsar duk tambayoyinsu, har ya gamsar da su bayan doguwar tattaunawa. Sannan sai ya koma gida bayan ƙura talafa komai ya dawo daidai. Shi wannan Alƙali Bashafi’e Imamuddin ya kasance mai kyakkywar aƙida ne mai kyakkyawar manufa”. [Ibn Kasir, juz. 14, sh. 4.]

Za mu ci gaba…..

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories